Babban abin da yakamata mu fara la'akari da shi shi ne, yawan jari ko kalar sana'a ba shi zai tara maka kuɗi ba. Da yawan mutane suna gabatar da wani aiki ko sana'a, amma kuma ba sa samun irin kuɗaɗen da suke buƙata na rayuwa.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
To yaya kuma ga wanda zai fara sana'ar yanzu, har yake tsammanin da zarar ya fara sai kuɗi su yi ta shigowa?
Duk wanda ya gina sana'a ko kasuwanci, ya san irin ƙalubalen da ya fuskanta, kuma idan kasuwancin nasa ya tsaya yana kawo riba, ya san hanyoyin da ya bi, da kuma wasu dabaru da ya riƙe, a matsayin sirrin neman sa.
Sai dai bisa ɗabi'ar mutanen mu, da wuya mutum ya gaya ma irin dabarun nasa, musamman idan ya zama sana'ar ku iri ɗaya ce, ko kuma kasuwa ɗaya kuke ci.
Masu kuɗi da waɗanda suka samu nasara a kasuwanci da sana'a, sun fahimci cewa, babu wani wanda yake son rabuwa da kuɗinsa haka kawai.
Sai dai akwai wasu buƙatu da domin su ma yake tara kuɗaɗen sa, kuma a shirye yake ya biya kuɗi domin biya masa waɗannan buƙatu.
Masu kuɗi sun gane cewa, zuba kuɗin su a irin waɗannan buƙatu na al'umma, ko kuma samar da sana'a wacce za ta magance matsalolin waɗanda suke da kuɗin biya, hanya ce miƙaƙƙiya ta gina arziki.
Sun gane cewa akwai buƙatun da dole a zo neman su, kuma da zarar ka shirya yadda za ka magance waɗannan buƙatu, mutane za su yi ta layi suna biyan ka kuɗade, domin warware musu damuwarsu, ko kuma buƙatar su.
Abin da yakamata mai sana'a ko kasuwanci ya fahimta shi ne, wacce irin matsala ko buƙata yake iya warwarewa a cikin aikinsa, saɓanin abokanan kasuwancin sa.
Akwai abubuwa da yawa da za'a iya duba zuwa gare su, amma bari mu kawo kaɗan daga ciki;
1. ƘARANCI
Wannan yana nufin wani abu na buƙatar rayuwa ya yi ƙaranci ko wahala, kai kuma sai ka nemo shi duk inda yake, ko kuma ka samar da shi.
Hakan zai zama dole mutane su biya ka ladar ka, domin ka samar da abin da suke buƙata, yayin ƙaranci.
2. LOKACI
Mutane suna da buƙatu, amma a mafi yawa, buƙatun nasu suna da lokaci.
Matsawar ba za ka iya biya musu buƙatunsu akan lokacin da suke buƙata ba, tabbas za su rabu da kai da kayan ka, ka yi ta hamma ba ciniki.
Wannan ce tasa yanzu da yawa, za ka ga ana yawan tallata kaya, tare da cewa za mu iya kawo maka kayan inda kake, kuma sai ka gani sannan ka biya.
Akwai kuma abubuwan da suke da kaka, wato ƙayyyadadden lokaci, duk wanda ya kawo kayan sanyi cikin tsananin zafi, ya san sai dai ya kai su ma'ajiya.
3. FARASHI
Kusan duk abin da mutum zai saya, kafin ya zo kasuwa ya ƙulla a zuciyar sa farashin da zai iya biya.
Saɓanin wannan zai iya fasa buƙatar, ba don ba shi da kuɗin ba, sai dai buƙatar ba ta kai wannan farashin ba a gurin sa.
Wajibi ne ka warware matsala a farashin da masu buƙata za su iya biya.
Idan farashin ka ya zarta waɗanda kake tare da su, ya zama wajibi ka nemi sabbin abokan hulɗa.
Wannan shi zai kai mu ga mataki na gaba a ƙasa.
4. MUHALLI
Wannan kamar yadda na zayyana a sama yana da alaka da irin matsalar da za ka warware, su wa za ka warwarewa, kuma a wane farashi.
5. GAMSARWA
Kamar yadda kowa ya sani, duk wanda zai rabu da kuɗinsa, so yake kuma ya rabu da matsalar da ta sa shi kashe kuɗin.
Don haka dole ne ka samar masa da abin da yake buƙata, har ya gamsu cewa biyan ka da ya yi bai yi kuskure ba.
RUFEWA
Wato gaba-ɗaya shi nema, ɗaukar ƙafa ne da kuma ɗaukar dama, abinda ake kira LEVERAGE.
Dole ne kake la'akari da buƙatun al'umma na ƙashin kansu, sai kuma yanayi da wani salo wanda ba kowa ya fahimce shi ba.
Wannan ce tasa za ka ga mutane masu sana'a iri ɗaya, wani lokacin a waje ɗaya, amma wani yana ta bunƙasa, wani kuma sai a hankali kawai.
Masu magana suna cewa, kowa ya ci Zomo, ya ci gudu tukunna.
Allah yasa mu dace Amin.
