Fitaccen dan wasan barkwanci na fina-finan
Hausa Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da
Bosho ya ce tsundumar da ya yi cikin harkar fim
ce ta hana shi zama farfesa.
"Na samo sunan Bosho ne saboda lokacin da
nake makarantar sakandare ina yawaita karatu.
Na kan kwashe kwana 15 ban yi cikakken bacci
ba saboda yawan karatu.
"Shiga ta harkar fina-finai ce ta hana ni zama
farfesa," in ji Bosho, a hira ta musamman da ya
yi da BBC Hausa.
Dan wasan ya ce sha'awarsa wajen karatu ce ta
sanya yake amfani da wasu kalmomi na boko a
fina-finansa.
"Za ka ji ina yawaita cewa 'A shekarar 1778 da
na je Ingila sarauniya ta bukaci a dafa min shayi
amma na ce tuwo nake so' ko kuma na cewa
'wane ne ubanka a Northern Nigeria', in ji
Sulaiman Yahaya.
Bosho, wanda ya kwashe fiye da shekara 30
yana fitowa a fina-finan Hausa, ya kara da cewa
ya rungumi bangaren barkwanci ne saboda shi
dama mutum ne mai yawan son raha.
A cewar Bosho, "Na soma fim tun lokacin da ake
wasan kwaikwayo na dandali; ni mutum ne mai
son bunkasa al'adun Hausa da addinin Musulinci,
shi ya sa na zabi zama dan wasan kwaiwayo.
"Na dauki al'adarmu da matukar muhimmanci
kuma na soma fim ne tun lokacin da ake yin
wasannin kwaikwayo a Gidan Dan Hausa da ke
birnin Kano. 'Yan wasa irin su Danhaki da
Mallam Mamman su ne gwanayena".
Dan wasan na Hausa ya nuna bakin cikinsa kan
yadda masu shirya fina-finan Kannywood ba sa
mayar da hankali wurin bunkasa al'adar Hausa,
yana mai cewa, "hakan ne ya zubar da
mutuncinmu a idanun masu kallo".
Ya kara da cewa saboda irin mummunan kallon
da ake yi wa 'yan fim ya bude kamfanin hada fim
wanda zai mayar da hankali wurin tallata al'adun
Hausa.
Bosho ya ce akwai dangantaka mai kyau
tsakaninsa da marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.
"Ibro ya kan taso daga garinsu Danlassan ya zo
nan [cikin birnin Kano] mu sha hira; shi mutum
ne mai kokarin zumunci.
"Ni ma na kan je garinsu na sada zumunci kuma
har yanzu ina ci gaba da zuwa mu gaisa da iyaye
da iyalansa. Kafin ya rasu mu kan bai wa juna
shawara kan al'amuran rayuwa. Allah ya jikansa",
a cewar Sulaiman Yahaya.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
Source By Bbc Hausa
Thursday, 14 September 2017
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
0 comments:
Post a Comment