Sunday, 24 September 2017

Samar Da Aikin Yi a Yankunan Igbo Zai Iya Kawo Zaman Lafiya - Kwararru

Tura Wannan Zuwa Ga

Bayan da babbar kotun tarayyar Najeriya ta bai
wa gwamnatin kasar ikon ayyana kungiyar IPOB
a matsayin kungiyar 'yan ta’addanci.

Mazauna
yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun yi kira
ga gwamnati ta samar wa da matasan kungiyar
aikin yi don samar da zaman lafiya.

An yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta
tsara ingantacciyar hanyar samarwa ‘yan
kungiyar IPOB aikin yi, don magance illolin dake
tattare da zaman banza.

Yayin da Muryar Amurka ta zanta da wasu
mazauna yankin Kudu maso Gabashin Najeriya,
da akwai alamar cewa batun rashin aikin yi shine
ya mamaye yankin ya kuma haddasa damuwa ga
al’ummar.

A cewar Dakta Stanly Okereke, wanda ke zama
babban malami mai kula da harkokin dalibai a
jami’ar jihar Abia, na ganin idan har gwamnatin
ta samarwa da al’umma isasshiyar wutar lantarki
za ta cimma buri, saboda matasa kan iya amfani
da wutar lantarki wajen yin wasu sana’o’i don
dogaro da kai.

Shi kuma wani malami mai koyar da kimiyyar
harsuna da lamuran yada labarai, Dakta Cimma,
na ganin rashin kulawa ne ya janyo irin wannan
zanga-zangar da kuma kafa kungiyoyi irin su
IPOB.

Amma babbar tambaya ita ce ta wacce hanya ce
ya kamata a bullowa lamarin, kasancewar a baya
an taba yin irin wannan zanga-zanga a yankin
Kudu maso Kudu da kuma yadda aka magance
ta.
Ya ce dole sai gwamnatin tarayya ta samar da
ingantacciyar hanyar tsara wani shiri da zai
taimakawa matasan yankin domin samar da
zaman lafiya.

Domin karin bayani saurari rahotan Alphonsus
Okoroigwe.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: