Tuesday, 12 September 2017

Shin ko Kasan Hukunci Yin Magana yayin da Liman yake Hudubar Juma'a???

Tura Wannan Zuwa Ga

Jama'a mu kula kuma mu gyara


Hakika mafiya rinjayen Malamai sun tafi akan
wajibcin yin shuru a bisa dukkan mutumin da ya
halarci sallar Juma'a, a lokacin da
Liman yake gabatar da Khutbah.

JUMA'A


Duk wanda ya yi wa 'Dan uwansa magana, koda
kuwa ce masa ya yi "KA YI SHURU", to ya aikata
lagawu. Duk wanda ya aikata
lagawu kuwa, ba shi da ladan Sallar Juma'ar.


Sayyidina Abu Hurairah (ra) ya ruwaito daga
Manzon Allah (SAW) cewa: "DUK WANDA YA CE
WA DAN UWANSA "YI SHURU KA SAURARA"
YAYIN DA LIMAN YAKE KHUTBAH, TO HAKIKA
YA AIKATA LAGHWU". (Sahihul Bukhary Hadisi
na 892, da kuma Sahihu Muslim Hadisi na
851).


Malamai sun ce wannan haramcin ya hada har
da amsa tambaya, koda akan Musuluncine
balantana kuma wadansu zantuka daban, ko
kuma zancen duniya.


Zamu samu misalai da hujjoji da dama daga
rayuwar Sahabbai da kuma sauran magabata na
kwarai akan haka. Sayyiduna Abud Darda'i (ra)
ya ce: "Watarana Manzon Allah (SAW) ya hau kan
mambari yana yi mana Khutbah, sai na ji ya
ambaci wata ayar Alkur'ani (Wacce ban santa
ba). Ubayyun bn Ka'ab yana zaune
kusa dani, don haka sai na tambaye shi "YA
UBAYYU YAUSHE NE AKA SAUKAR DA WANNAN
AYAR? ". Sai ya yi shuru bai kulani ba. Nasake
tambayar sa amma duk da haka bai ce min
komai ba.

Har sai da Manzon Allah (SAW)
ya sauko daga kan mambari sai (Shi Ubayyun)
yace min "BA KA SAMU KOMAI DAGA WANNAN
SALLAR JUMA'AR TAKA BA, SAI
DAI ZANTUKA MARASSA AMFANI".


Bayan an idar da Sallar sai na je na gaya wa
Manzon Allah (SAW) dukkan abinda ya faru. Sai ya ce min: "HAKIKA UBAYYU YA YI GASKIYA. YAYIN DA KUKA JI LIMAMINKU YA FARA YIN
MAGANA, TO KU YI
SHURU KU SAURARA HAR SAI YA IDAR".


A duba MUSNADU AHMAD, hadisi na 20,780, da
kuma SUNANU IBN MAAJAH hadisi na 1,111.

Wannan hadisin ma yana karfafa hujjar cewa
wajibi ne yin shuru yayin da
Liman yake Khutba, kuma koda dan uwanka yayi
maka magana ba za ka amsa ba.

Ibnu Abdil-Barri ma ya fada acikin AL-ISTIZKAAR
juzu'i na 5, shafi na 43 cewa "BABU SABANIN
RA'AYI TSAKANIN MALAMAI AKAN WAJIBCIN
YIN SHURU YAYIN DA LIMAN YAKE KHUTBAH".

A cikin BIDAYATUL MUJTAHIDI juzu'i na 1, shafi
na 389, IBNU RUSHDIN (Allah ya rahamshe shi)
ya kawo maganganu wasu Malamai da suke
ganin rashin wannan wajibcin. Amma ba su da
wata hujja mai karfi, don haka ba za'a dauki
wannan maganarsu a matsayin hujja ba.

Amma Malamai sun ce Liman yana da damar
tsayawa yayi magana da masu sauraron Khutbar,
suma sunada irin wannan damar. Amma idan
akan wani muhimmin al'amari ne.


Hujjah a nan ita ce Bukhary da Muslim sun
ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (RA)
cewa: "Wata rana Manzon Allah (SAW) yana
tsakiyar Khutbah sai wani Balaraben kauye ya
tashi yace: "Ya Rasulallahi dukiyoyinmu
sun lalace, 'Ya'yanmu suna cikin wahala. Don
haka muna so ka yi mana addu'a".


Manzon Allah (SAW) ya cira hannunsa sama ya
yi musu addu'a. Nan take aka fara ruwa,
washegari ma haka, har sai da wata Juma'ar ta
kewayo ana ruwa. A duba Sahihul Bukhary Hadisi
na 891. Sahihu Muslim hadisi na 897. Sannan
akwai hadisin Jabir bn Abdillahil Ansary (RA)
wanda ya nuna cewa
Manzon Allah (SAW) yana gabatar da Khutubah
amma ya tsaya ya umarci wani mutum cewa ya
tashi yayi nafila. (Bukhary Hadisi na 888).


Imamu Ahmad da Is'haq suna ganin halaccin
gaisar da mai atishawa a lokacin da Liman yake
Khutbah. Amma Shafi'iy ya karhanta hakan. Don
karin bayani a duba ALMUGHNEE na Ibn
Kudaamah juzu'i na 2 shafi na 85.


WALLAHU A'ALAM.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user