Wednesday, 27 September 2017

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci kwashe dalibai 'yan Najeriya masu karatu a yankin tsibirin Dominica

Tura Wannan Zuwa Ga

'Yan Najeriya suna karatu likita a tsibirin
Dominica wanda zai shirya su zuwa Amurka da
Turai

- Shugaban kasa ya damu sosai lokacin da ya
samu labarin wannan mumunar hadarin

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba
Muhammadu Buhari ya umarci kwashe dalibai
'yan Najeriya masu karatu a yankin tsibirin
Dominica nan da nan bayan wani mumunar
taguwa wanda ake kira Hurricane Maria ta rushe
tsibirin.

'Yan Najeriya sun halarci makarantun likitanci a
tsibirin Dominica wanda zai shirya su zuwa
Amurka da Turai don kammala karatun digiri na
likitanci.

Babban mataimakin shugaban kasa a kan kafofin
yada labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da
umarnin shugaban kasa, yana cewa shugaba
Muhammadu Buhari ya damu da halin da daliban
suke fuskanta.

Ya ce an ba da umarnin ga ma'aikatar harkokin
kasar waje wanda tuni suka fara aiki dagan
dagan.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Shehu ya ce
ma'aikatar ta sanya wani babban jami'in ta
wanda ya tafiya don ba dalibai takaddar tafiya na
wucin gadi.

Shehu ya ce: "Shugaban kasa ya damu sosai
lokacin da ya samu labari cewa wasu daga cikin su
ba su tsere da komai ba sai dai kayan da ke
jikinsu”...

A cewarsa, za a tura daliban zuwa Brazil, inda ba
su buƙatar takaddar tafiya don dawo da su
Najeriya.

Mumunar taguwar tare da iskar har zuwa mil 155
a kowace awa (kilomita 250 a kowace awa),
wannan ne mafi babbar hadarin da ya mamaye
yankin Amurka a kusan shekaru 90.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Hausa. Naij.com

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: