Sunday, 17 September 2017

TARIHI: 2 ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.

Tura Wannan Zuwa Ga

Kashi na Biyu

Bayan anyi haka, sai sarki Kano Ali ya bar kano
ranar 4 ga ga watan shawwal tare da tawagarsa,
wadda ta kunshi dogaransa, dakarunsa da sauran
barorinsa.
Kwana 26 bayan sun bar Kano sai labari ya riski
kano cewar turawan yamma sun isa zariya harma
sun kwaceta da yaki.

Da fari da suka shigo kano, sun riski wani kauye
mai suna Bebeji ne. Sai kuwa suka kori mutanen
garin suka kashe shugabansu da ake kira sarkin
fulanin Bebeji.

Da labari ya riski sarkin shanu, sai nan take ya
sanar wa da Ma'aji Usmanu cewar Turawa fa sun
shigo kasar kano, harma sun cinye Bebeji da yaki.
Dajin haka, sai Ma'aji Usmanu ya tashi ɗan aike
zuwa ga Larabawan nan mazauna kano, yace
yana bukatar ganinsu.

Zuwansu keda wuya, sai ya shiga labarta musu
halin da ake ciki na zuwan Turawan Yamma,
sannan ya rufe da cewar wacce shawara zaku
bamu bisa wannan lamari?
Larabawan nan sai suka ce ka sani ya kai Ma'aji,
mu baki ne anan kasar, bamu da abin cewa
anan. Kurum dai idan har suka rufar mana da
yaki da niyyar kashemu tare da kwace dukiyoyin
mu, to hakika muma zamu far musu da yaki
daboda faɗin Annabi Muhammad S.A.W cewar
duk wanda ya mutu yana kokarin kare dukiyarsa,
to yayi mutuwar shahada. Haka kuma duk wanda
ya mutu yana kokarin kare kansa daga halaka,
shima yayi mutuwar shahada. Iya abinda zamu
iya cea kenan.
Ma'aji Usmanu yace ku fahimce ni. Sarkin mu ya
bar garin nan kuma ya umarcemu da cewa duk
binda ya taso, muyi shawara daku, kuma kada
mu tsallake ra'ayinku. Don haka kuji zancena, a
yanzu muna zaune daku gari ɗaya, muna neman
taimakon kune domin kare garinmu daga makiya.
Sai larabawan nan sukace wa Ma'aji Ka barmu
muje gidajenmu tukunna.
Sai kuwa Maaji ya barsu suka tafi.
Da yammaci, sai dukkansu suka hallara kamar
haɗuwa ta fari. Ma'aji ya kara nanata musu
abinda ya faɗa da farko, sukuwa sai suka amsa
masa da cewa "mun amince da duk abinda
ubangiji yayi hukunci damu."
Sai Ma'aji yace "to idan Allah ya kaimu gobe
muna raye lafiya, inason dukkanku da bayinku ku
ɗauki makamai ku taru a bakin ganuwa. Nikuwa
zaku sameni a bakin ganuwar Bebeji, don haka
sai muga abinda Allah zaiyi."
Sai larabawa suka ce "munji abinda ka faɗa,
Allah ya bamu nasara akansu amin."
Daga nan sai Ma'aji Usmanu ya tura da wasika
izuwa sokoto, yana mai sanar da Sarkin Kano Alu
Babba lamurorin da suka auku bayan barinsa
birni.

Kashe gari, ranar talata (koda yake lissafin ranar
ya nuna 4 ga shawwal + kwana 26, zai baka 1
gawatan zulka'ada na 1320, kuma ranar jumua ta
kama) tun da sassafe wasu larabawan sukayi
hawa da bayinsu suka tsaya a gefen ganuwa
suna masu ɗauke da makamai.
Babu jimawa sai muka ga wasu mutane da suka
fita izuwa Bebeji tare da Ma'aji sun shigo birni a
sukwane kuma a gigice. Suna gudu kamar ransu
zai fita, kowanne ya nufi gidansa suka shige
abinsu.
Koda mutane suka ga haka, sai suka bisu a baya.
Bayan ɗan lokaci wasu suka fito kofar gida, shine
kuma sai mutane ke tambayarsu abinda ya faru.
Shine sai suka ce hakika yau munga abinda zai
fitar da zomo daga raminsa.
Mutane sukace bamu gane ba, me kuka gani
kenan?
Mutanen nan "sukace munga kiristoci turawan
yamma waɗanda zasu fitar damu daga garinmu.
Suna ɗauke da madafu da ɗakaru masu yawan
gaske. Lallai mun shaida waɗannan 'yan ta'adda
suna nufowa ganuwar mu."
Kafin kace haka, sai muka fara jiyo kararrakin
bindigogi, ana harba wata babbar bindiga da ake
kira mai ruwa.
Harbinsu na farko suka karya kofar birni. Da suka
harba na biyu kuwa sai da gidan sarkin kofa ya
rushe. Harsashin yayi fata-fata dashi kansa
sarkin kofar, ya faɗi matacce.
Koda larabawa suka ga haka, sai suka shiga
cewa Ya Ubangiji Allah ka tsaremu daga sharrin
wannan rana. Madalla da ubangijinmu mai
tsarewa.

Daga nan fa sai suka rarrabu, kowannensu ya
nufi gidansa ya shige, suka kulle kofofinsu,
sannan suka haye bisa saman sorayen gidajen
nasu.
Jim kaɗan da faruwar haka, sai turawa suka
shigo birnin kano.
Suka shigo dasu da sojojinsu. Sannan kai tsaye
suka nufi kofar fada. Suka shiga gidan ta kofar
kudu. Jagoransu wani bature ne da ake kira Mai
kwagiri.
Da shigarsu sai suka hangi wani mutum a tsaye
da takobi zare a hannunsa. Su basu san
kowanene ba, amma nan take baturen nan mai
kwagiri ya harbeshi da bindigarsa, mutumin ya
faɗi matacce. Kai kace tun jiya ya mutu. Ashe
kuwa sarkin shanu ne wanda sarki Ali ya baiwa
ajiyar gari.
Turawa fa suka rinka kutsawa cikin fadar nan
tare da sojojinsu, da alamar akwai abinda suke
nema amma basu same shiba. Domin babu
abinda suka taras sai yara kananu da mata. A
Gidan kuwa babu abinda kakeji sai koke-koke..
.
A wannan fada, turawa suka kafa dandalinsu.
.
Zamu cigaba Insha ALLAH
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By SADIQ TUKUR GWARZO

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: