Cikakken sunansa shine Abu Abdullahi
Muhammad Ibn Umar al Husayn al Taymi al Bakri
al Tabari'at fakhraddin al Razi. Amma anfi masa
lakabi da 'shaikul Islam' ko kuma ace 'Al fakhrur
Razi', ko 'Sultan Al Mutakallimina', ko kuma ace
masa 'Shaykul Mushakkiqina'.
Shi Gangaran ne a fannin Ilimi. Gwanin tafsirin
Al-kur'ani, Jagaba a ilimin falsafa, Shugaba neshi
a ilimin Balaga, zakaqaquri ne kuma a ilimin
lissafi.
An haife shi a a shekara ta 1149 miladiyya, a
wani gari mai suna Rey wanda yake a cikin kasar
Iraqi. A hannun mahaifinsa ya soma ɗaukar
darasu sannan daga bisani ya soma zagayawa
wajen malumma domin ɗaukar ilimi daga garesu,
harma an bayyana shi a matsayin ɗaya daga
cikin mutanen nan da ake yiwa lakabi da 'Al Majd
al Jilil' masu bin falsafa da koyarwa ta Imamuna
Ghazali.
Kusan ana iya cewa a neman ilimi da karantarwa
Imam Ar Razi ya k'arar da kwanukan rayuwarsa,
domin kuwa ance ya rinka bin garu-ruwa na nesa
dana makwabta akan haka, har daga bisani Allah
ya karɓi ransa a wani gari mai suna Herar dake
kasar Afghanistan.
Ance Imam Ar Razi yayi muhawara da masana
daban daban na zamaninsa, sannan ya rubuta
littattafai na ilimi kimanin guda ɗari, ya kuma
tara ɗumbin dukiya da ɗalibai masu yawa a
rayuwarsa, har saida takai akwai lokacin da idan
zaiyi tafiya izuwa wani gari ɗalibai 300 keyi masa
rakiya, sannan mutane dubu ɗaya keyi masa
dakon dukiyarsa wadda ta kunshi zinare da
azurfa da kayayyakin alatu.
Imam Razi, ya rayu a wani lokaci mawuyaci,
lokacin da ake ganiyar rikici tsakanin mabiya
shi'a da Sunni a Iran, a lokacin da rikicin mulki ya
mamaye daular farisa, a lokacin da kuma sa-in-sa
ta dabaibaye malumma akan falsafar wanda ya
kamata ayi biyayya dashi tsakanin Imam Ibn Sina
da kuma Imam Al Ghazali.
Saboda haka a wancan lokaci Imam Ar Razi sai
ya zama mabiyin Sunni, kuma ya nesanta kansa
da neman mulki, tare da ɗosanuwa bisa tafarkin
falsafar Imam Ghazali.
Kasancewar sa gwani a fannin tsara zance da
iya muhawara, yasa duk wani malami na zamanin
ke shakkar ya kalubalanceshi akan inda yasa
gaba, domin matsawar za'a zubeta, to shine zaiyi
nasara. Amma kuma hakan, sai ya jaza masa
hasada da bakin jini a wurin malamai 'yan
uwansa. Har ana tsammanin silar mutuwarsa
yazo ne a bisa guba da mabiya ɗarikar
Karramiyawa suka sanya masa a abinci.
A fannin Ilimin Alkurani mai girma, Imam Razi ne
marubucin littafin tafsirin nan mai mujalladi
takwas mai suna 'Mafatihul Ghaib', da kuma wani
littafin daya rubuta mai suna 'Aja ibul Quran'
wanda ya tattaro abubuwan mamaki da al'ajabi
da suka zo a cikin alkurani mai girma. Don haka
ka tsaye ana iya cewa yayiwa Al-kur'ani hidima.
Dangane da falsafar sa a ilimin sararun samaniya
kuwa, Ar Razi ya taɓa faɗa cewa "Khalala la
nihayata laha" (watau ita sama an halicce ta ba
tare da tana da iyaka ba).
Sannan kuma yayi tsokaci a game da falsafar
cewa duniyar mu kaɗaice ke ɗauke da bil'adama
a duk faɗin maɗaukakiyar duniya, inda ya tafi
akan cewa hakika Sarkin daya halicce ta, yana da
ikon ya halicci dubunnai misalinta tare da wanzar
da halittu acikinta.
A karshe ya rasu a hekarar 1209 a garin Herat
na kasar Afghanistan bayan gajeriyar rashin
lafiya.
Ga kaɗan daga littattafan da ya rubuta kuma:-
-Al Mutakallim fi ilmul Kalam
-Ilm Alkhalq
- Kitab al firasa
- Kitab al nafs wal ruh
- Kitab al manɗiq
- Sharh quwa-huma
-Risala al Huduth
- Sharh almaa lahil Husna
- Nihayat al iqul fi Dirayal al usul
-Mabahith al Mashriqiyy fi ilm al Ilahiyya wal
tabiiyyat
Da wasunsu.
Da fatan Allah yajiqansa ya kuma kyauta namu
zuwan amin.
Source By ©SADIQ TUKUR GWARZO
0 comments:
Post a Comment