Fassara ©Zaidu Ibrahim Barmo
MrZaid
Gabanin Najeriya ta samu ƴan
cin kanta a ranar 1 ga watan
Oktoban shekarar 1960, ƙasar na
amfani ne da tutar Birtaniya a
ƙarƙashin gwamnatin turawan
mulkin mallaka na Ingila.
Har sai a shekarar 1958 lokacin da
ake shirye-shiryen mika mulki ga
ƴan Najeriya aka fidda sanarwar
gasar zana tutar kasar.
Jama'a da dama sun shiga gasar, inda kowa ya
tura irin nasa zanen.
A wannan lokacin wani ɗalibi ɗan
Najeriya dake karatu a Kwalejin
fasaha ta Norwich dake Ingila mai
suna Micheal Taiwo Akinkunmi ya
shiga gasar, inda ya tura zanen sa
zuwa Legas kuma bayan tantance
zanuka kimanin 2,800 na wadanda
suka shiga gasar, a ƙarshe aka zaɓi ta
sa mai launin Kore da fari da kore.
Sai dai kuma asalin zanen da ya aike
na ɗauke da hotan rana a kan farin,
wanda alkalai suka cire a lokacin.
Kuma a ranar 1 ga watan Oktoban
shekarar 1960, ranar da turawa suka
ba Najeriya ƴancin kanta aka ɗaga
tutar da Micheal Taiwo Akinkunmi ya
zana wato mai launin Kore da Fari da
Kore, yayin da aka sauke tutar Ingila.
Ma'anar launin koren dake jikin tutar
Najeriya shine Noma, wato hakan
nan nufin Allah ya albarkaci Najeriya
da kasar Noma, yayin da launin farin
ke nuni da zaman lafiya a kasar.
Turawan da suka miƙa mulkin ga
gwamnatin Nigeria a wannan
lokacin sun ba Micheal Taiwo
Akinkunmi kyautar pan 100 na Ingila.
#Micheal_Taiwo_Akinkunmi : An
haifi PA Micheal Taiwo Akinkunmi a
garin Owu a jahar Ogun ne, shekaru
74 din da suka wuce.
Ya yi karatun primary a
makarantar Baptist Day Secondary,
Ibadan, ya yi kuma karatun
sakandirinsa a Ibadan Grammar
School, ita ma a garin na Ibadan.
Daga nan ne kuma ya samu aiki a
sakatariyar gwamnati ta Ibadan,
inda yai aiki na tsawon wasu
shekaru, daga nan ne kuma ya ta fi
Ingila karo karatu a a kwalejin
fasaha ta Norwich, inda ya karanta
fasahar noma.
Mr. Akinkunmi ya koma Najeriya
bayan da ya kammala karatunsa,
inda ya kama aiki a ma'aikatar
ayyukan gona.
Zaidu Ibrahim
(Member a ƙungiyar marubutan katsina)
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By © Zaidu Ibrahim Barmo
MrZaid
0 comments:
Post a Comment