Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na
cikin shugabannin kasashen da suka yi
jawabi a taron kolin Majalisar Dinkin
Duniya yau a birnin New York dake
Amurka inda shugaban ya tabo abubuwa
da dama.
Bayan da
shugaban ya gabatar da jawabinsa wa
Majalisar Dinkin Duniya, MDD, akan
mahimman abubuwan da suka shafi
kasa da kasa da kuma Najeriya 'yan
kasar na cigaba da tofa albarkacin
bakinsu.
Yayinda wasu suka jinjina masa wasu
kuwa gani suke da ya maida hankali
akan neman kudaden da aka sace daga
kasar kuma aka ajiyesu a kasashen
ketare.
Dr. Usman Muhammad mai sharhi akan
al'amuran da suka shafi kasa da kasa
yana tsokaci akan jawabin shugaban.
Yana mai cewa jawabi ne mai nauyi
amma dan kadan. Yana da
mahimmanci saboda shugaban ya tabo
nahiyar Afirka da ECOWAS da siyasar
duniya da rubuce rubuce da batun 'yan
gudun hijira da kuma kasashen dake
tamaimaka wa 'yan gudun hijiran,
musamman na kasar Siriya.
Shugaba Buhari ya bada shawarar
yadda za'a fitowa muguwar manufar
shugaban kasar Koriya ta Arewa.
Akan cewa bai mayar da hankali akan
dawowa Najeriya kudadenta da aka
sace ba, Dr Usman yace irin wannan
maganar ba 'a yinta a waje dalili ke
nan da zai gana da Shugaban Amurka
Donald Trump domin tattauna
al'amarin.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By ©Voa Hausa
0 comments:
Post a Comment