Tuesday, 10 October 2017

Hausa Film RA'AYI RIGA: Ba Ni Da Dan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Wuce Atiku A Zaben 2019-Rashida Mai Sa'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa'a ta bayyana cewa a zaben 2019 ba ta da dan takarar shugaban kasa da za ta zaba wanda ya wuce tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.

Rashida wadda take rike da mukamin mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin mata, ta kuma kara da cewa a yayin zaven gwamna, za ta zavi Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne, amma zaben shugaban kasa ba ta ra'ayin sake zaben shugaba Buhari.

Jarumar wadda ita ce shugabar mata na matasan jam'iyyar APC ta qasa kuma Ambasadan matasa ta jihar Kano, ta kara da cewa "mu muka yi Buhari a 2015 inda muka shiga lungu da sako don yakin zabe har Allah ya sa aka samu nasara Buhari da Ganduje suka ci zabe.

A dalilin jajircewa ta a harkar siyasa ce ta sa aka ba ni mukamin darakta a gidauniyar Atiku reshen Arewa maso yamma".

Rashida ta kara da cewa a siyasar duniya ba ta da ubangidan da ya wuce gwamna Ganduje saboda ya yi mata halaccin da ba za ta tava mancewa da shi ba. Saboda shi ya dauki mukami ya ba ta, don haka tana fatan Allah ya maimaita masa muqaminsa na gwamnan Kano.

Kuma tana kyautata zaton nan gaba za ta samu mukamin da ya wuce wanda take da shi yanzu, saboda kyakkyawar alaqar dake tsakanin ta da gwamnan.

Kuma yana xaya daga cikin burin gwamna Ganduje yin tafiya da jajurtattun matasa irinta. Kuma tana xaukar Ganduje tamkar uban da ya haifeta, saboda ya yi mata rana a duniyar siyasa. Kuma shine wanda ya kara fito da ita duniya ta san ta.

A bangaren mukamin da aka ba ta a gidauniyar Atiku kuma, Rashifa ta ce" ita siyasa rigar 'yanci ce duk wanda ya nemi ya tafi da kai za ka iya binsa. Kuma ni tun kafin na yi Buhari dama Atiku nake yi tun kafin a yi maja. Kuma ko da aka zo aka haxe ma muna tare.

Kuma wanann matsayi da aka ba ni a gidauniyar Atiku na yi farin ciki matuka. Don ina tare da tafiyar Ganduje, sannan kuma ina tare da tafiyar Atiku dari bisa dari".

Rashida ta ce babu shakka a zaben gwamna tana ra'ayin Ganduje ya zarce, amma a zaben shugaban kasa Atiku za ta zava saboda ya san da zaman ta, amma Buhari bai saman da zaman ta ba.

Saboda siyasa rigar 'yanci ce, rigar da kake so ita za ka saka sa a jikin ka, babu wanda zai tilasta maka ka saka rigar da ba ka yi ra'ayi ba.

"Na sha alwashin zan sake shiga lungu da sako tare da saka qarfi na da dukiyata don ganin Ganduje ya zarce a zaben 2015. Ni babu wanda ya san da zama a tafiyar Buhariyya, amma a bangaren Atiku a san da ni.

Ka ga kenan duk mutumin da zai gina daki ya ce taho ka shiga, ai ya gama yi maka komai".

Game da tambayar da aka yi wa Rashida kan cewa ganin tana yin Ganduje amma kuma a sama ba ta yin Buhari, ko hakan ba zai kawo mata cikas ba a gwamnatance, sai jarumar ta kara da cewa "ai abin da zai iya kawo min nakasu a siyasa ta shine na ce ba na yin Ganduje, saboda shi ne ya ba ni mukami, kuma kowa ya san ina yin sa dari bisa dari.

"Wannan magana da nake faxa ba kai kaxai nake faxawa ba duniya baki daya nake fadawa, cewa ni gaskiya ina ra'ayin Atiku, kuma ko yau Gwamna Ganduje ya ce Rashida na sauke ki daga matsayin da kike, Wallahi duk inda zan shiga na fita sai na ga Ganduje ya koma kan mukaminsa, saboda ina ra'ayin sa a cikin zuciyata. Haka zan bi loko da sako don ganin na samowa Atiku kuri'a tun da ya riga ya furta yana son takarar shugaban kasa.

Kuma a ko ina na tsinci kaina zan kare mutuncin Atiku da Ganduje, domin sune iyayen gidana a siyasa".

Game da rikicin siyasar da ya ki ci ya ki cinyewa a tsakanin vangaren Gandujiyya da Kwankwasiyya kuma, Rashida ta bayyana cewa ita jaririya ce a wannan fannin kuma babu yadda za a yi ta sa kanta cikin irin wannan rikici a matsayin ta na karama. Don haka ta yi fatan Allah ya kawo mafita, sannan kuma ita ba ta yin siyasar rigima.

"Hausawa sun ce da ka ba ni kifi, gara ka koya min yadda ake kama shi. To ni Ganduje ya nuna min yadda zan kama kifin har ma wani ya mori kifin a hannuna. To ka ga ni batun rigimar Gandujiyya da Kwankwasiyya ni jaririya ce a ciki.

Saboda ni na tashi ne na ga waxannan mutane guda biyu (Kwankwaso da Ganduje), kuma ni ban ma san me ya haddasa rikicin na su ba. Ka ga ba zan na ce ina rigima da wani daga cikin su ba. Ni dai na riga na san ni 'yar Gandujiyya ce ta halak".

A yayin da aka tambayi Rashida ko har yanzu tana cikin harkar fim kasancewar ta tsinci kanta a harkokin siyasa, sai Rashida ta ce tabbas har yanzu tana cikin harkar fim tsindum. Domin har yanzu tana shirya finafinai kuma kamfaninta ba ya wata biyu ba tare da ya shirya fim ba. Domin ko a yanzu a kwai Series din da suke yi. Inda ta fi fitowa a finafinan da kamfanin ta ke shiryawa ba na wasu kamfanonin ba.

Kasancewar ci gaban da ta samu, wasu masu shirya finafinan ma tsoro suke su kira ta, duk da cewa kofar ta a bude take ga duk kamfanin dake son ta yi masa aikin fim. Ta ce har yanzu tana martaba masana'antar fim domin ita ce silar daukakar da ta samu a siyasance da kuma duk wani mataki da za ta taka a duniya.

"Saidai a samu bambanci tsakanin jaruman yanzu da na baya, saboda wasu jarumai matan da suka shigo harkar fim a yanzu da ma ko a gidan su ma ba kunya ce da su ba, don haka idan ta shiga masana'antar fim sai ta ga kamar kowa bai isa ba. To mu lokacin da muka shigo masana'antar fim idan aka sa kara babu hali ka tsallake saboda mun san darajar abin, kuma biyayyar da muka yi ta kai mu matakin da ba mu yi tsammani ba. Amma na yanzu ba haka bane. Mu har yanzu farin jininmu yana nan, saboda ko a yanzu idan zan wuce wuri sai an ambaci sunana.

"Ka tafi da nisa ma, akwai Saima Mohammed shekarar ta nawa rabon ta da fim, amma yanzu idan aka taso sai an yi maganarta. Haka kuma irin su Hadizan Saima, Maryam Jan Kunne, Ummi Nuhu duk idan an gan su sai an kira sunansu. Amma na yanzu jarumar da za ta yi fim sau goma a cikin wata guda, sai ka ga na fi ta sanuwa a cikin al'umma".

Game da irin ci gaban da aka samu a masana'antar fim kuma, Rashida ta ce "tabbas an samu ci gaba a masana'antar fim fiye da baya saboda an samu kayan aiki. Amma matsalar da harkar fuskanta a yanzu shine jarumai don mu tsoffin jarumai muke son su dawo don ganin sun wanke kazantar dake cikin harkar a yanzu.

"Abu ne mai wuya ka je wurin sharholiya ka ce ka ga fuskata.

Sabanin jaruman yanzu da za ka duk wani wurin wasanni za ka dinga ganin su. Ni tun da nake a rayuwata ta duniya ban tava zuwa yawon gala ba, inda za ka ga an tara mutane kana rawa ana kallonka. Domin na dauki fim da muhimmanci kuma na ga ribar hakan. Kuma ko yanzu idan furodusa ya nemi na yi masa aiki, zan ba shi lokacin da na san ba zan samu matsala a wajen aiki na ba.

Rashida ta kuma kara da cewa ranar da fim din ta na Sa'a ya fito kasuwa, ita rana mafi farin ciki da ba za ta tava mancewa ba a harkar fim.

"A lokacin da aka kai fim din Sa'a kasuwa, kwafe dubu dari sun kare a take. Wadanda suka ga na fito a fim din suke so kalla da na tura kasuwa a sayo min, babu ko kwaya daya ya kare. A dalilin haka sai da na yi sallar nafila raka'a biyu na godewa Allah tare da fatan Allah ya sa na shigo harkar a sa'a.

"Sannan kuma ranar da na shiga bacin rai a masana'antar fim ita ce ranar da muke aikin wani fim din kamfanin HRB a Abuja. Sai aka zo aka samu rashin fahimta tsakanin Kubura Dako da Maimuna Wata Yarinya da kuma marigayi Nasiru Kabuwaya. Yadda na ga an ci mutuncin Kabuwaya sai aka yi rigima da ni, a qarshe ma kin yin fim din na yi sai sako ni aka yi a mota na dawo gida Kano. Tun daga Abuja har na shigo Kano kuka nake yi saboda ba a kyale ni na amayar da abinda dake cikin zuciyata ba.

Shi kuma Kabuwaya abin da aka yi masa a Abuja na bacin rai shine silar da ya yanke jiki ya fadi mutu bayan sun dawo Kano da kwana daya. To wannan ita rana mafi muni da ba zan mance ba a masana'antar fim".

Rashida ta kuma kara da cewa a yanzu jaruman da suke burge ta sune Sadiya Adam da kuma Garzali Miko da Nuhu Abdullahi saboda sun san darajar mutane.

Tace idan Sadiya Adam ta gan su a waje, saidai ta zauna a kasa a gefen su. Kuma Allah ya daukaka ta saboda zuciyarta.

Baya ga harkar fim da kuma muqaman siyasa da na kungiyoyi da Rashida take ciki, ta kuma kara da cewa tana da gidauniyar da ta kirkira mai suna Mai Sa'a Foundation, saboda a rayuwarta tana da sha'awar ta ga ta taimakawa marayu da marasa galihu. Da kuma matsalar shaye-shaye da mata suke yi da kuma yawaitar fyade. Inda suke hada kai da hukumar kare hakkin dan Adam don ganin sun dauki mataki.

"Za mu je gidajen marayu da sansanin 'yan gudun hijira da kuma gidajen fursuna da asibitoci domin kai gudummawa. Idan na samu kudi kamar milyan daya na kan kasa ta gida biyu, inda zan yi sadakatul jariya da rabi, rabi kuma na yi bukatun kaina da su".

Ta ce gidauniyar ta su ta taimakawa marasa lafiya da dama, sannan kuma sau da yawa mutane suna kawo mata bukatun kansu kamar biyan kudin haya ta biya musu.

Sannan kuma suna daukar nauyin sanya almajirai a makarantun boko da kuma kai gudummawa gidajen fursuna da sauransu.

Ta kuma kara da cewa a yanzu haka gidauniyar ta su na shirin ganawa da gwamnonin Akwai Ibom da Gombe, Mejo Hamza Al-Mustapha da kuma Sarkin Gombe, don ganin sun hada karfi da karfe wajen taimakawa talakawa. Haka kuma za su zauna da Sarkin Kano da gwamnan Kano. Domin a cewar ta irin wadannan gidauniyoyin sukan taimakawa gwamnati ne wajen isar da sakon su ga talakawa. Domin su suke amfani da motocin su shiga lungu da sako su jiyo kukan talakawa.

Ta ce a yanzu ayyukan da gidauniyar take yi a aljihunta ake yi, domin babu wanda ta suka nemi gudummawa a wajensa.

Ta ce suna kokarin soma farautar masu hali wadanda suke da kudirin taimakawa al'umma, domin ko a kwanan nan wani attajiri ya kira ta daga Yola game da yadda za a yi ya bada gudummawarsa ga gidauniyar, inda aka tura masa asusun ajiyar gidauniya ya turo da kuxi amma ya bukaci kada a bayyana sunansa.

Haka ma wani daga jihar Lagos ya kira a waya kan yadda za su yi su turo da na su gudummawar. Kuma shi ma ya tura nasa tallafin, wanda na bada jimawa za su tsara yadda za su yi su sai kayayyakin da za a rabawa mabukata.

A karshe Rashida ta yi kira ga matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen bangar siyasa, kuma su sani suna da matuqar muhimmanci a cikin al'umma don haka su tashi tsaye wajen ganin sun kare martabar kansu, kada a dinga amfani da su ana ba su xan abin da bai taka kara ya karya ba. Su kuma zama masu ra'ayin kan su, kada wani ya sauya musu ra'ayi.

"Matasa su sani cewa su ma za su iya kaiwa matakin da 'yan siyasan da suke sa su yin bangar siyasa, domin ni Rashida ba na fitar da ran cewa zan iya zama shugabar kasa a nan gaba, kama daga kan matakin kansila har zuwa sama.

Ba na shakkar fadin gaskiya ko da a gaban majalisar dinkin duniya ne, Allah kawai nake tsoro ba dai wani dan Adam ba".

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com
.
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Aliyu Ahmad

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: