Wasu sojojin jamhuriyar Nijer da na Amurka sun
hallaka yayinda wasun su suka yi batan dabo
bayan da suka fada tarkon ‘yan bindiga a jiya a
wani wurin dake arewacin jihar Tilaberi kan
iyakar Nijer da Mali lokacin da suke aikin sintiri.
A yayin da suke kokarin cafko wasu ‘yan bindiga
da suka kai hari sojojn na jamhuriyar Nijer da
wasu Amurkawa dake basu horo suka yi arba da
wasu ‘yan takife dake dauke da manyan
bindigogin yaki inda suka yi masu kwanton bauna
wato kan iyakar Mali da jamhuriyar Nijer.
Rahotanni sun bayyana cewa an kwashe okaci
mai tsawo ana musayar wuta tsakanin bangarorin
biyu, kafin daga karshe ‘yan ta’addar suka yi
nasarar hallaka sojojin Amurka da na jamhuriyar
Nijer.
Honorable Karimu Burema, na daga cikin wakilan
al’ummomin jihar Tilaberi, a majalisar dokokin
kasa ya bayyana cewa sojojin Amurka uku suka
hallaka guda kuma ya ji mummunan rauni, sai
kuma guda biyu na jamhuriyar Nijer, ya kuma
kara da cewa an hallaka dabbobi da dama, amma
‘yan ta’addar sun arce da mutanen su da suka
mutu da kuma wadandasuka jikkata.
Ministan tsaro na jamhuriyar Nijer, Kallla Musa,
wanda ya tabbatar da afkuwar wannan hari ya
kara da cewa kawo yanzu basu kammala
harhada bayanai ba, amma gwamnati zatafitar da
sanarwa a karshen taron majalisar koli mai kula
da harkokin tsaro da za a gudanar a karkashin
jagorancin shugaba Mahamadou Issoufou , a
yammacin yau Alhamis.
Wannan kazamin hari ya faru ne a lokacin da
kasashen kungiyar hadin gwiwa mai kokarin yaki
da ta’addanci ta fara aiki a fagen daga, saboda
haka shugaban ‘yan kwamitin ‘yan majalisar
dokoki masu kula da sha’anin tsaro Muhamman
Asa, ya kara jaddadawa askarawan kasar Nijer,
da gwamnatin kasar goyon baya.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni
Barma nada Karin bayani.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa
0 comments:
Post a Comment