Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane
wani itacen baure a bakin wani rafi. Kullum suka
tashi sai su nufi can su hau, su yi ta ci.
Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani
kunkuru. Kullum idan gaurakin na cin baure,
wadansu ‘ya’yan su kan kucce musu su fado
kasa. Da kunkuru ya ga suna fado masa yana ci,
sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi
kyauta, don suna sonsa. Saboda haka, da ya ga
alherin ya yi yawa, ran nan sai ya daga kansa ya
dubi gauraki, ya ce, “Kai ‘yan’uwana, na gode!
Kullum dai na kan ga ‘ya’yan bauren da ku ke
sako mini. Abin maku ya yi yawa, wallahi har
kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya saka da
alheri!”
Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi,
sai suka gane abin da ke aukuwa.
Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu
bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana
ta. Ta dubi kunkuru ta ce, “Don mun ga kai ba ka
iya hawowa, shi ya sa mu da Allah ya ba fiffike
mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka
sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar
zumunci.”
Kunkuru ya ce, “Amin! Na ko yi godiya.”
Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har
ya zama aminci na gaskiya.
Gaurakin nan da sun
zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun
tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba
su son abin da ya taba shi, shi kuma ba ya son
abin da ya taba su.
Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare,
gauraki suka koma neman kwadi da tana. Bayan
kamar wata biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya
kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai duniya ruwa
bai taba zama nan ba.
Da gauraki suka ga haka, sai suka yi shawarar su
tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda
ke da danshi-danshi.
Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, “Ya
kamata mu je mu sallami kunkuru, kada ya ga
shiru hankalinsa ya tashi, ya yi zaon wani abu ne
ya same mu.” Suka tashi, suka tafi wajen
kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura.
Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, “Af, to, ai ba ku
barina, sai mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi
ya yi Kaura. Ni ina na ke iya zama inda babu
laima?”
Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, “Yaya za ka
yi ka bi mu, alhali kuwa kai ba ka da fiffike?”
Kunkuru ya ce, “Sai ku dauke ni, in kun ga kwa
iya kokarin hakanan.”
Babbar gaurakar ta ce, “Wa ka ke zato cikimmu
zai yia daukar kato kamarka? To, ce ma muna
iyawa, ina za a kama, ga ka jiki duk kwarya?”
Karamar ta ce, “Bar shi, mu ji tasa, watakila
yana da dabara, Kin san an ce mai rai ba ya rasa
kokari.”
Kunkuru ya ce, “I, ina kuwa da wata ‘yar
gurguwar dabara, in kwa iya. Sai mu sami kara
mai karfi kamar zira'i biyu, ni in cije tsakiyar, ku
kuma kowace ta kama gefe guda da baki. Kun ga
da haka sai ku tashi da ni har inda za ku.”
Babbar ta ce, “Wannan dabarar ban ga za ta
yiwu ba ga kamarka, mai surutu.”
Karamar ta ce, “A’a, in ya ce dai ya iya kyalewa,
sai sai mu dauke shi.”
Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta
dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi,
ta ce, “To, don Allah in ka kama, ban da yawan
magana.”
Kunkuru ya ce, “Haba, wannan ma sai an
dankwafe ni kansa, sai ke ce yaro? In yi surutu
mana, in ina so!”
Gauraki suka ce, “To, madalla!” Suka kama kara
suka tashi da kunkuru yana cije.
Suna cikin tafiya, sai hanya ta dauke su ta bisan
kasuwa. Suna kaiwa tsakiyar, sai mutane suka
daga kai suka hange su, suka ce “Eho, eho, ku
zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai
jama’a. abin mamaki ba ya karewa nan duniya!”
Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, “Kai,
Allah ya tsine idandunan nan naku mutane, da ba
su iya ganin abu su kyale.”
Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya
kawo kasa kum.
Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna
cewa “Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba,
lalle yana tare da halaka.”
Tushe/Asali: Waziri Aku