Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi
al'ummar kasar sabbin alkawari yayin da yake
musu jawabi a ranar bikin cikar kasar shekara
57 da samun 'yancin kai.
Shugaban ya yi wa dubban matasan kasar
marasa aikin yi alkawarin ba su aiki, inda ya ce
zai samar wa matasa dubu 10,000 aikin yi.
Sai dai wannan ba sabon abu ba ne, don ko a
lokacin da yake yakin neman zabe ya taba yin
irin wannan alkawari - abin da wasu suke ganin
har zuwa yanzu bai cika ba.
Har ila yau shugaban ya yi alkawari game da
wata matsala da ta dade tana ciwa 'yan kasar
tuwo a karya wato matsalar karancin hasken
wutar lantarki.
Ya yi alkawarin kara adadin wutar lantarkin da
kasar take samarwa daga Mega Watt dubu 7,001
zuwa 10,000.
Sai dai sabanin alkawarin samar da ayyukan yi,
shugaban ya ce yana fatan wadatuwar wutar
lantarkin ne nan da shekarar 2020.
Hakazalika ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da
tattaunawa da masu ruwa da tsaki a yankin Neja-
Delta (mai arzikin man fetur) don samun
dawwamanman zaman lafiya a yankin.
Sai batun yaki da cin hanci da rashawa, wanda
shi ma an saba ji shugaban yana shan alwashin
magance shi a baya.
Ga kadan daga cikin ra'ayoyin ma'abota
shafinmu na Facebook game da batun:
" Me jiya ta yi bare yau? Mun gaji da gafara sa
ba muga kaho ba. Tsoho (Buhari) ka kauce
kawai ka ba wa matasa filin su kawo canji," in ji
Hudu Muhammad Huduwala.
Sai dai Bashir Sahal Nguru addu'ar fatan cika
alkawuran ya yi:
"Hakika sabon alkawarin da Shugaba Buhari ya
yi wa matasa na samar musu da ayyuka kimanin
dubu goma a kowacce jiha, hakan shi ya nuna
cewa shugaban na sane da dimbin matsalolin
rashin aikin yi da matasa suke a ciki, da fatan
Allah Ya ba shi cika alkawuran da ya dauka," in
ji shi.
" Ko shakka babu na yi imanin cewa Shugaba
Buhari zai iya ciki wannan alkawari da ya
daukarwa matasan kasarmu tun da mun gani a
shirin N-Power," a cewar Mustapha Marabar
Musawa.
Amma ra'ayin Abubakar Sarina ya bambanta
inda ya ce:
"Wannan alkawarin 'yan siyasa ne kawai wanda
ake dauka ba a cikawa. A baya dai idan kafadi
magana ina gasgatawa, amma yanzu na fara
dawowa daga rakiyarka Buhari," in ji shi.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa
0 comments:
Post a Comment