Wannan da kuke gani shine hoton makamin
kare-dangi (Atomic bomb or Nuclear
weopon) kamar yadda ake kiranshi da
kalmar Hausa shine karshen makami mafi
girma da hatsari wanda binciken ilmin
kimiyya ya samar dashi a tarihin duniya
Kamar yadda Bahaushe ya kira makamin da
suna makamin kare-dangi tabbas haka ne,
domin hakika idan aka harba makamin zai
iya karar da dangi, zuriya, gari koma wata
kasa gaba daya
Babu wani tabbataccen tarihi da zai nuna
maka ga lokacin da aka fara gina makamin
kare-dangi, amma ana hasashen cewa kasar
Germany itace kasar da ta fara samar da
ilmin fasahar gina makamin tundaga
shekarar 1894 shekaru 112 da suka gabata
kenan
Makamin kare dangi makami ne ake kerashi
da sinadarin Uranium, Nitrogen, Toluen da
sauransu, ana sanya masa injin roket, akwai
na'ura mai sarrafashi zuwa inda akeso a
aikashi, idan wata Kasa ta mallakin makamin
takan iya anfani dashi wajen samar da
wutar lantarki, iskar gas da sauransu,
makamine wanda wata karamar kasa wacce
bata da karfin tattalin arziki bata isa ta
ginashi ba saboda makudan biliyoyin daloli
da yake lakumewa kafin a iya ginashi
Asalin Makamin Kare-Dangi ana batun cewa
bai wuce kasashe 8 zuwa 15 cikin kasashen
duniya da suka mallaka ba, cikin wadannan
kasashe akwai, Jamus, Amurka, Burtaniya,
Isra'ila, Korea ta arewa, Turkiyya, Italiya,
Netherland, Pakistan da India wadannan
sune kasashen da ake tunanin sun mallaki
makamin
Makamin kare-dangi yana da ka'idoji kafin
ayi anfani dashi wajen kaiwa hari, sai an
samu amincewar shugaban kasa,
shugabannin tsaro da kuma amincewar
majalisar dinkin duniya, shiyasa aka samar
da wata hukuma wacce zata sa'ido akan
makamin saboda hatsarinsa
Idan aka harba makamin ya fashe, yana
sakin wata irin iskar gas mai matukar
tsananin zafi, shiyasa a lokacin da aka
harbashi yake gudu duk abinda ya wuce ta
kasansa indai mutum ne ko bishiya ko
dabba zai kone kurmus nan take ya zama
toka saboda tsananin iskar zafi da yake
sakewa, bayan ya tarwatse garin
sinadarinsa kuma zai cigaba da watsuwa,
tare da haddasa mummunan fashewa da
rugujewa da girgizan kasa da bala'in
tsunami, yana ruguza tsaunukan duwatsu
duk girmansu
Makamin idan ya fashe yana kashe duk wani
abu mai rai hatta wanda yake a cikin ruwa
yana kashewa saboda gubar da yake
fesawa, yana haddasa kafewar kugunan
ruwa, ya lalata wutar lantarki da kafofin
sadarwa, hatta tauraron 'dan adam bai tsira
daga illar makamin kare dangi ba, yana
dusashe hasken rana, ya haddasa
mummunan dumamar yanayi
Saboda hatsarin wannan makami wani
lokacin baya kwamitin tsaro na majalisar
dinkin duniya sun taba gabatar da kudirin
cewa a kawar da wannan makami daga
doron duniya, duk kasar da ta mallaka ta
lalatashi
Shekaru kamar 6 da suka gabata akwai
wani masanin tsaro tsohon sojin Amurka ne
ya taba shirya wani wasan kwaikwayo yake
nuni ga Amurka ya nuna hatsarin samar da
makamai masu hatsari irin wannan, domin
idan wata hatsari ta auku zai iya rusa kasar
Ga misali da abinda ya faru a masana'antar
girka sanadarin makamashin nukiliya na
kasar Japan dake yankin Fukushima Daiichi
a shekarar 2011 inda aka samu tsautsayi
wata tukunyar girka sinadarin tayi bindiga,
daga karshe ya haddasa asarar dubban
rayuka, rugujewar gine-gine, girgizan kasa
da bala'in tsunami, wannan fa wata
tukunyace tayi bindiga, ina kuwa ace
makamin ne gaba dayansa yayi bindiga?
Makamin daga cikin illar da yake haddasawa
ga al'umma shine za'a koma ana haifan yara
nakasassu, akwai kananunshi irinsu (Missile)
makami mai linzami, irin wanda gwamnatin
North Korea take yawan gwajinsa, hankalin
duniya yana tashi ne idan akayi gwajinsa
saboda illar da yake haddasawa ga lafiyar
bil'adama, a wani lokacin ma har da girgizan
kasa
Tarihi ya nuna cewa dakarun Nazi na kasar
Jamus Sarki Hitler ya basu umarni sunyi
anfani dashi a lokacin yakin duniya na biyu a
yankin Hiroshima na kasar Japan wanda har
zuwa yanzu illar makamin bai daina aiki ba
har sai ya cika shekaru 100, shiyasa a
wannan yanki yanzu babu wani abu mai rai
da yake rayuwa. a lokacin ba'a ingantashi da
fasaha irin na yanzu ba fa
To yanzu abinda yake faruwa tsakanin
Amurka da Korea ta arewa har wani tsohon
sojin Amurka yace idan aka fara yaki
tsakanin kasashen a tsakanin mako guda
mutum sama da miliyon biyu zasu iya
hallaka, wato saboda kasashen ta iya yiyuwa
suyi anfani da makaman kare danginsu ne,
domin dama dashi suke gadara
A karshen wannan rubutu ina tausayawa
al'ummar kasashen musulmi da basu mallaki
wannan makami ba
Ko kunsan cewa Isra'ila da Amurka sun saita
makaman kare danginsun akan cewa idan
wata tsautsayi ma ta faru makamin ya fashe;
to ya tashi yaje ya fadi a kasashen gabas ta
tsakiya, wato kasashen musulmi?
Ko kunsan cewa hankalin kasashen da suka
mallaki wannan makami a tashe yake domin
tsoron kada wasu kasashen musulmi su
samu sirrin fasahar suyiwa makamin kutse
(hacking)
ta hanyar na'ura su tayar dashi ya fashe
musu a gari ko kasa?
Allah ya bamu lafiya ya kuma kare kasashen mu
na musulmi
Amin
.
.
Source By © Farouk Abdullahi Tukuntawa
0 comments:
Post a Comment