Saturday, 14 October 2017

Tarihi A Karanta Za'a Karu: ASALIN INDA KALMAR 'HAUSA' TA FITO. (Tsakure daga Muk'alar Nazarin Tarihin Hausa)

Tura Wannan Zuwa Ga

Hakika, sanin inda kalmar hausa ta samo asali
abin bukata ne a garemu, duba da yadda muke
da kauna gami da soyuwar son jin tarihi mafi
gaskiya na wannan harshe namu.

Idan wasu sunce asalin kalmar 'Bahaushe' wadda
ake lakabawa wanda duk ya fito daga masu yara
harshen Hausa, ta zone daga kalmar 'Baushe',
ma'anarta kuma mafarauci, to sai muce ita
kalmar hausa kuma daga ina ta samo tushiya?

Kalmar Hausa ance bakuwa ce, wai daga baya
tazo.

Ance ma masanin tarihi Leo Africanus ya
tabbatar da cewa a zuwansa Katsina da Kano a
karni na sha biyar, baiji ana faɗin sunan hausa
ba, kuma da yaren gobiranci yaji ana magana.

Haka kuma manazartan littafin nan mai ɗauke da
tarihin kano mai suna 'Kano chronicle' sun
tabbatar da cewa tun daga zamanin Bagauda har
zuwa kan Abdullahi Burja, ba'a amfani da kalmar
hausa. Sai a wuraren karni na sha biyar, lokacin
ɗansa Yakubu aka soma jinta
Tabbas, hakan na iya zama gaskiya, sai dai
akwai-ja a maganar yaren gobiranci da akace Leo
Africanus ya tarar ana yarawa a kadar hausa.

Domin masu bada tarihin Gobirawa sunce asali
daga misira suke, yaki ya korosu, suka rinka
sauka da tashi a wurare mabanbanta, sai a karni
na sha biyar suka riski birnin Lalle da
Gwararramu.

Kunga kenan a wancan lokacin
(karni na shabiyar) basu iso inda kasar hausa
take ba a yanzu.

Sannan kuma a wancan lokacin, wasu littattafai
sun bada tabbacin wanzuwar wasu kabilu a
wannan yanki namu. Misali, kabilun Maguzawa,
Katukawa, Gazargawa, Tokarawa, Damarguzawa
da sauransu.

Hakan na iya nufin Kabilar hausa mai yara yaren
hausa itama ta wanzu amma dai bada Hausa ake
kiranta ba, kuma sai daga bisani ta bunkasa tare
da haɗiye ɗaukacin kabilun dake makwabtaka da
ita.

Amma dai ga binda wasu masana suka faɗa
dangane da asalin kalmar hausa:-

- Mr C.R Niven (1971) cewa yayi: Hausa daga
buzaye ta fito, domin sunan da ake kiran
mutanen dake zaune a arewacin kogin kwara
kenan.

- Farfesa Skinner (1968) cewa yayi :Hausa daga
kalmar Aussa ne na mutanen songhai wadda ke
nufin Arewa.

Kuma yace akwai daɗaɗɗiyar alaka
tsakaninsu ta yadda har hausawa sun aro
kalmomi a wurinsu. A cewarsa ma kalmomin
Bene da Soro duk nasu ne.

Marigayi Mal Aminu kano cewa yayi hausa daga
Kalmar Habsha ne.

Domin shi yana ɗaya daga
masu cewa asalin hausawa mutanen habasha ne
tun lokacin daya riski habashan yagano akwai
kamance-ceniyar al'adu a tsakaninsu da
hausawa.

A cewarsa 'Habsha' ne asalin sunan,
sai aka koma Habsa, sannan daga baya ya dawo
Hausa.

Sarkin Ningi Marigayi Alhaji Haruna cewa yayi an
samo kalmar Hausa ne daga labarin Bayajidda
sa'ar daya kashe macijiya shine sai tsohuwa
Ayyana ta rinka ceea 'ai wani mutum ne ya
kasheta wanda ya HAU-SA' maimakon tace
yahau doki...

Shin menene Ra'ayinku game da Asalin Kalmar
ta Hausa???

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: