Sakataren Ƙungiyar Izala Ta Ƙasa kuma
shahararren mai wa'azin nan, Malam
Muhammad Kabiru Gombe ya ce, saɓawa
Allah da faɗi Annabi Muhammad
ﷺ ne jama'a su taru su kashe
wani don sun ji ya zagi Annabi
ﷺ
Malamin yayi wannan tsokaci ne a yayin da ya
ke amsa tambayoyi daga Zuma Times Hausa
a ofishinsa a Abuja inda ya jaddada cewa
rashin sanin addini ne ya ke kawo irin
waɗannan ɗabi'u a al'umma.
"Babban abinda ke jawo irin wannan shine
jahilci, duk lokacin da al'umma ta zauna cikin
jahilci kuma ga ta tana son addini, babu abin
tashin hankali kamar mutum yana son
Musulinci amma kuma bai san Musulunci ba,
ko wani irin shirme zai iya yi da sunan
Musulunci wanda hakan ya haifo mana da
matsaloli da dama a Musulunci kuma har
yanzun muna fuskantar wannan matsalar."
Malam Kabiru Gombe ya ƙara da cewa ilimi ne
kaɗai zai iya sa Musulmi su gane cewa, ba su
ke da ikon yanke hukunci tare da zartar da
hukunci ga mai laifi ba face hukuma.
"Addinin Musulunci bai yarda mutane su ɗauki
doka a hannunsu ba ko da dokar ta Allah ce.
Duk wanda ya yi haka ya saɓa wa Allah da
Annabi Muhammadu ﷺ .
"Hukama ita kaɗai aka yarda ta yi hukunci
sannan ko hukumar ma akwai sharuɗa da aka
gindaya kafin ta ɗauki hukunci ko ta zartar,
milali, ta yi bincike sosai sannan a samu
shaidu da sauransu kafin alƙali ya yanke
hukunci sannan a zartar da wannan hukunci.
"Ba wai kawai da an ce wannan ya zagi
Annabi sai a kashe shi, to ko da mutum ya ji
ba shi ke da hurumin ya yanke hunkunci
sannan ya zartar da hukuncin a Musulunci ba.
Kai dai naka shaida ne ko ka yi ƙararsa ga
hukuma.
Misali in mutum ya yi sata an ce a
yanke hannunsa ko in yayi zina a jefe shi
amma ai ba Allah Ya ce ni da ku za mu zartar
da wannan hukunci ba sai alƙali kuma dole sai
an yin bincike da sheidu kafin a yanke
hukunci.
"Ko a gabanka aka zagi Annabi
ﷺ baka da hurumin zartar da
hukunci sai hukuma in hukumar ba ta ɗauki
mataki ba, babu ruwanka, ita Allah zai
tambaya ranar Alƙiyama ba kai ba."
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
Source By ©Zuma times Hausa
0 comments:
Post a Comment