Monday, 6 November 2017

Tarihi: TAKAITACCEN TARIHIN MARIGAYI RABILU MUSA DAN (IBRO)

Tura Wannan Zuwa Ga

An haifi marigayi Rabilu Musa Ibro a shekarar
1971. Ya yi karatun Firamare dinsa a Danlasan
da ke cikin karamar hukumar Warawa. Sannan
kuma ya yi Sakandare a Kwalejin horon malamai
ta Wudil (Teachers College).

Daga nan ne ya
shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a
shekarar 1991. Ya yi shekara takwas Ya na aikin
Gandiroba inda ya kai matakin insfekto, daga
nan ne ya bari ya cigaba da sana’ar wasan
kwaikwayo. Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar
Fim a tun ya na aji uku na makarantar
sakandare. Ya na da
Mata da Yara hudu ko uku akwai : Jamila,
Kubra, Auta. Daga cikin yaransa akwai: Akwai
Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni,
Sannan akwai Asma’u, Annabe, Sa’adiyya, Akwai
wani yaro kuma da ya Haifa ya sa sunan mai
gidansa
wato Baba Yaro.

Kafin Rasuwarsa Ya bayyana
Ciroki a matsayin dan wasan
hausa abokin sana’ar sa da ya fi burgeshi. Da
aka tambayi Rabilu Musa ibro dan wasan
santimental da ya fi burgeshi sai yace “ Adamu

Usher, ka ga wannan, yana bani sha’awa.
Saboda ba shi da girman kai, ba zan manta ba
lokacin rasuwar kulu da Yautai, tun daga farkon
rasuwar mu na tare da su.” In ji Ibro Daga cikin
dubunnan fina finansa ibro ya bayyana cewa ya
fi son wadannan fina finai “Akwai Kauran Mata,
Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa. Ibro
ya bayyana ya fi son tuwon dawa a bangaren
abincinsa, fannin sutura kuma sai yace “Na fi
son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa,
ba in sa Shadda ba kwana biyu in ga tana
kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a lokacin ya na
raye me ya fi bakanta masa rai a kan harkar
sana’arsa sai yace“ Ni abinda yake bata mani rai
kawai a wannan sana’a bai wuce rashin hadin
kan ‘yan wasa ba.

Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran mahallicinsa ya
na da shekaru 43, a duniya. Allah ya kyautata
makwanci.
Amin

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Fadila M. Idris

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: