Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin
Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin shi ne
sabon hafsan hafsoshin tsaron Najeriya.
Shi dan asalin jihar Ekiti ne da ke kudu maso
yammacin kasar.
Kafin a nada shi a kan wannan mukami, shi ne
shugaban cibiyar bayar da umarni ta sojin
Najeriya da ke birnin Minna na jihar Naija.
Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai
Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne
hafsan dakarun sojin kasa na Najeriya.
Buratai dan asalin jihar Borno ne da ke arewa
maso gabashin Najeriya.
Kafin nadin sa, Buratai shi ke jagorantar
rundunar tsaro ta hadin-gwiwa wacce ke da
hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi.
Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi
da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki
da 'yan ta'addan da ke yankinsu.
A baya dai, Manjo Janar Buratai ya yi aiki a
matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin
Najeriya da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers,
sannan ya taba zama Kwamandan makarantar
horas da sojin kasa da ke Jaji, jihar Kaduna.
Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas
Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas shi aka nada a
matsayin hafsan dakarun sojin ruwa.
Ibok-Ete Ekwe Ibas dan asalin jihar Cross River
da ke kudu maso kudancin Najeriya ne.
Ya shiga makarantar horas da sojoji, wato
Nigerian Defence Academy a shekarar 1979, kuma
ya zama Sub-Lieutenant a shekarar 1983.
Cikin mukaman da ya rike kafin wannan mukamin
har da: shugaban makarantar sojin ruwa da
shugaban ma'aikatan da ke samun horon sojin
ruwa da shugaban gudanarwa na sojin ruwa, da
kuma shugaban tsare-tsare na sojin ruwa.
Haka kuma ya rike mukamin babban jami'in
kamfanin sojin ruwa na Navy holding limited.
Air Vice Marshal Sadique Abubakar
Air Vice
Marshal Sadique Abubakar shi ne sabon babban
hafsan sojin sama.
Shi dan asalin jihar Bauchi ne.
Kafin nadin sa ya taba zama shugaban sashen
da ke tabbatar da ingancin aiki na rundunar sojin
sama da kuma jami'in kula da sadarwa da
Kwamandan horas da sojin sama na Najeriya.
Air Vice Marshal Monday Riku Morgan
Air Vice Marshal Monday Riku Morgan shi aka
nada a matsayin babban jami'in kula da bayanan
sirri na tsaro a kasar.
Air Vice Marshal Morgan dan asalin jihar Benue
da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ne.
A shekarar 1982 ne ya zama sojin sama.
Cikin mukaman da ya rike har da: Kwamandan
Sojin Sama da ke kula da tsare-tsare.
Manjo Janar Babagana Monguno
Manjo Janar
Babagana Monguno shi ne sabon mai bai wa
shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.
An haifi Monguno a garin Monguno da ke jihar
Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Ya shiga makarantar horas da sojoji, wato
Nigerian Defence Academy.
Kafin ya yi ritaya daga soji, ya rike mukamai da
dama, cikin su har da: Kwamandan rundunar
tsaron shugaban kasa, mataimakin kwamanda a
kwalejin koyon aikin soji, babban mai kula da
sha'anin sirrin soji.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com hanya me sauki ko kuma daga kasan Website din akwai inda akasa
Name...
Email...
Message...
Sai Ku turo mana mun gode
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Bbc Hausa
0 comments:
Post a Comment