Jama’a barkanmu da warhaka. Deendabai ne ke muku fatan alkhairi.
A yau zan kawo maku bayanai kan yadda zaka sanya subtitle a hoton video (movie) ta hanyar amfani da wasu yan hikimomi akan wayarka ta android.
Menene video subtitle ?
Video subtitle ba komi bane face rubutun dake fitowa a kasan hoton video wanda ke fassara maganar da ake fada zuwa wani harshen ko kuma kara jaddada kalaman da ake fadi a cikin shi wannan video din.
So da yawa dai an fi samun subtitles na turanci a fina-finan wasu yarukan misali fina-finan Hausa , Chinese , Hindi , Larabci , Turkish , French dadai sauransu. A wasu lokutan zaka samu wadannan fina-finai ba tare da subtitle ba wanda hakan ka iya rage maka jin dadin kallon.
Bisa la’akari ga yadda mutanen mu ke kallon fina-finan kasashen kewaye sosai, na yanke shawarar rubuta topic akan yadda zaka sanya ma video subtitle in ya kadance bai zo dashi ba.
Abubuwan da ake bukata
• Wayar android
• MX Player
• Video da akeson sawa subtitle.
Matakai
Matakai
Da farko dai ya kasance kana da Mx player a wayarka , idan baka da ita sai kaje playstore kayi download nata.
Sai ka lalubo fin din da kake son dorawa subtitle din sannan sai ka bude shi da Mx player din, wato “open with mx player” .
Daga nan zai fara playing.
Sai ka danna option zaka ga an rubuto maka jerin abubuwa ciki harda subtitle da sauran wasu rubuce-rubucen kamar yadda yake
get-subtitle...
Idan ka shiga nan zai kaika zuwa wani shafin mai dauki da rubututtuka ciki harda get subtitle online to dai ka shiga nan kamar haka
get-subtitle
Daga nan sai ka shiga wajen search inda zai danyi searching kadan sannan sai ya kaika zuwa wani page dake dauke da rubutu mai dan tsawo, rubutun dai shine “Search for English subtitles from opensubtitles.org ” idan subtitle na turanci kake so sai kawai ka danna ok, amma idan na wani yare ne daban to sai kayi tick din wajen da aka rubuta ” Enter your search text ”
inda daga nan zai baka gurin rubutu sai kasa na yaren da kake so. Sai ka danna ok ka jira zuwa wasu yan dakiku.
Da zarar ya gama download din zaka subtitle din ya hau kan video ko film din . Idan kuma babu shi to zai rubuta maka cewar no subtitle found.
Karin haske: wannan ba ita kadai ce hanyar da za’a iya sanya subtitle ta waya ba, akwai wasu hanyoyi daban kamar ta amfani da vlc player ko kuma ta hanyar download na subtitle daga net da sauransu, to amma wannan da nayi bayani itace nike ganin zata kasance mafi sauki.
Tura ma yan uwa da abokai wannan post zuwa dandalinsu na Facebook , Twitter , Whatsapp dadai sauransu , sannan kada a manta da cewar duk wanda ya kwafi wannan bayani to yana dakyau ya saka backlink na Arewa Mobile
Source By ©Arewa Mobile