Rahoton Raba Press
Kungiyar jamiyyar PDP Amana reshen jahar
Katsina ta yi shelar cewar, zai yi wuya a zaben
shekarar 2019 ‘yan Nijeriya su sake bawa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari damar sake
darewa shugabancin kasar nan.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a taro da ta yi a
Sakatariyar PDP dake jahar a karqashin
Jagorancin dan Takarar Kujerar Shugaban
Matasan Jamaiyyar na yankin Arewa maso
Yamma Mallam Ibarahim Munafata Funtua.
Acewar kungiyar, gwamnatin APC karqashin
shugaba Buhari ta karbi mulki ne kawai ba tare
da wani kwakwaran tanadi da take dashi ba
musamman ga talakawan kasar nan da kuma
kasar.
Kungiyar tace, shelar da shugaba Buhari yake ta
faman yi musamman akan kudurorin gwamnatin
sa musamman, tattalin arzikin kasa da gyaran
hanya da yaki da cin hanci da rashawa, har
yanzu a shekaru biyun gwamnatin sa bata canza
zani ba, inda har ta kasance ga mafi yawancin
talakawan kasar nan gwamma jiya iyau.
Acewar ta, tattalin arzikin kasa, akwai cibaya
sosai, domin mafi yawancin talakawan da
gwamnatin shugaba Buhari take shelar dan su
take yi, ambar su cikin ukubar talauci da yunwa
da rashin aikin yi da kuma rashin sanin wata
kwakwarar madafa.
Data juya akan maganar hanyoyi Kungiyar ta yi
nuni da cewa, hanyoyin da gwamnatin tsohon
shugaban kasa Jonathan ta samar sun ninka na
gwamnatin Buhari, inda tayi tuni da cewa, mafi
yawancin hanyoyin kasar nan musamman a
Arewa sun zama tarkon mutuwa ga matafiya.
Akan cin hanci da rashawa kuwa, kungiyar ta ce,
abin kunya ne ace an samu wasu mukarraban
gwamntin da hannun su dumu dumu a cin hanci
da rashawa.
Tace, ficewar da jigogin da aka kafa gwamnatin
APC dasu suka fara, misali tsohon Mataimakin
Shugaban kasa Atiku Abubakar, alamace APC
zata kwashi kashin ta hannu a 2019.
0 comments:
Post a Comment