Abun dai ruwan dare ne, ba ga mazan ko matan ba. Kowane ɓangare na maza da mata suna taɓa waccar halayya ta yaudara a soyayya kuma suna fuskantar hakan daga abokan zamansu.
YADDA YAUDARA TAKE A SOYAYYA
Hoto: Goodmenproject
Marubuci: Abba Muhammad Dan Hausa
To amma shin wai mene ne yake kawo yaudara a soyayya? Mece ce ma ma'anar kalmar yaudara?
Yaudara ita ce, hali na ɓoye gaskiya da niyyar cuta ko zambatar wani.
A lokuta da yawa maza su ke sakin jiki har mata su yaudare su, ko kuma su mata suke sakankancewa har maza su yaudare su a soyayya.
Ina ganin za ku yarda da ni idan na ce "A dukkan lokacin da ka ji yaudara to da akwai rashin so da tausayi.".
MAZA
A sau da yawan lokuta namiji kan makance a kan soyayya har idanuwansa su rufe a kan haka, ya gaza gane macen da ta ke son shi dan abun hannunsa, ko ta ke kula shi kawai saboda rage dare, ko dan wani abu da ta ke nema a wajensa, ko macen da ta ke kula shi ba dan tana son shi ba, sai dan kawai ya matsanta mata akan ta so shi, da macen da ta ke son shi kawai dan tana jin daɗin kalamansa ko jin daɗin hira da shi amma ba dan tana son shi ba, har ta kai daga baya da zarar ta samu wani da take so ko ta gama cimma burinta a gare shi sai ta guje shi. Sai ka ji daga bisani ana mayar da yawu kan cewa ai wance ta yaudare ni, bayan kuma da ma can babu son gaskiya a tsakani.
Domin gujewa faɗawa irin wannan halin, tun da fari akwai buƙatar ka san wasu alamomi da ganinsu zai tabbatar maka da cewa tabbas wance tana sonka da gaskiya. Amma duk da haka sai ka yi taka-tsantsan.
MATA
Ke ma akwai buƙatar dukkan wanda ya zo miki da batun soyayya, ki tsaya ki nutsu ki tantance masoyinki na gaskiya, domin gujewa faɗawa tarkon samarin shaho ('yan-yaudara).
Akwai wani zai zo ne yana son ki kawai dan ya yi alfahari da cewa ke budurwarsa ce. Wani kuma zai yi ƙoƙarin neman hanyar da zai bi ya yaudare ki ne dan ya lalata miki rayuwa. Wani zai zo wajenki dan ya rage dare ne kawai da sauran su.
Da yawan 'yan yaudara, za su iya kashe miki ko nawa ne, har ma su yi wa waninki hidima, domin buƙatarsu ta biya a kanki.
Sun iya kalamai masu daɗi amma na yaudara.
Maza 'yan yaudara suna da wahalar ganewa a wajen mata, wani zai iya zubar miki da hawaye, wai dan duk ki yarda ya na son ki da gaskiya, zai iya siyo miki duk abun da kike so, zai iya ba ki duk abun da kika buƙata daga wajensa matuƙar buƙatarsa za ta biya a kanki.
Domin gujewa hakan ya kamata kike lura da irin kalaman da yawanci ke futa daga bakinsu, kike tace na gaskiya da kuma na ƙarya. Karda SO ya rufe miki ido ki gaza tabbatarwa da zuciyarki wane yaudararki kawai yake son yi, bayan kin gano hakan ko alamun hakan sun bayyana ƙarara a zahiri, saboda gudun yin da-na-sani daga baya.
Wanka da gari dai ba ya maganin yunwa.
Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.