Cin amana yana daga cikin Halayen munafurci.
Manzon Allah (saww) ya lissafta wasu halaye guda uku, yace duk wanda yake dasu acikin halayensa, to hakika shi munafiki ne. Koda yayi sallah yayi Azumi, koda yayi Hajji yayi Umrah, koda yace Shi Musulmi ne (Subhanallah!!!).
CIN AMANA yana daga cikin abubuwan da suke Tauye Imanin Mutum. Mutukar mutum zai rika cin amanar Mutane, to kullum Imaninsa raguwa yake yi.
CIN AMANA yana daga cikin halayen da suke Qaskantar da darajar mutum awajen Allah. Mutukar mutum bai rike amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa aranar Alqiyamah (Subhanallah!!!).
CIN AMANA yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'ummah, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al'ummah su rika gudunsa.
CIN AMANA yana zama sanadiyyar Dulmiyar mutum acikin wutar Jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi, Allah zai sanya amanar acikin chan Qasan Wutar Jahannama, sannan a umurci Maciyin amana cewa ya shiga ya dauko-ta. Sai ya dauko ya hauro wani babban Tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta subuce ta koma chan Qasan ramin Jahannama.
Sai Mala'iku su daka masa Tsawa suce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har Illa ma sha'Allahu.
CIN AMANA yana zubar da albarkar dukiya. Domin kuwa komai yawan kudi, in dai aka chudanyashi da kudin Cin amana sai ya lalace.
Yaku Jama'a!!! Ya Zama Wajibi mu rika kiyaye amanar junanmu don samun mutunci awajen Allah da bayin Allah.
Aslm. Yan 'uwa! Ko kun lura da yadda rayuwarmu ke karewa? Dare na saurin yi idan gari ya waye?
Shekara ta zama kamar wata, wata kamar sati, sati kamar yini, yini kamar awa, awa kamar minti kamar secon.
Ya dan'uwa mu yawaita bautar Allah, biyayya ga iyaye, tuba daga sabo, Sallah akan lokaci, hakuri da juna, adalci, yawaita Istigfari, Hailala da Salatin Annabi muhammadu (s.a.w) Allaah mai kowa da komai Ya jikan Mu ya gafarta mana yasa mutuwa Hutuce a garemu Amin S. Amin
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Muhammad Kabiru Muhammad (M. Kabiru Muhammad)
0 comments:
Post a Comment