Wednesday, 24 January 2018

Karanta Wannan Labarin: Ina Gargadin Buhari kada Ya sake Fitowa Takarar Zabe Kawai Yaje Ya Huta-Obasanjo

Tura Wannan Zuwa Ga
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da
cewa ya kamata ya hakura da neman ta-zarce a
shekarar 2019, saboda yawan shekaru da
yanayin lafiyarsa.

A wata budaddiyar wasika da Obasanjo ya fitar
wacce BBC ta samu kwafi, tsohon shugaban
kasar ya ce mulkin Najeriya al'amari ne da yake
bukatar mutum mai cikakkiyar lafiya wanda kuma
shekarunsa ba su ja ba, saboda aiki ne ba dare
ba rana.



Obasanjo ya kara da cewa Shugaba Buhari yana
bukatar lokacin da zai zauna ya yi tunani, ya
murmure ya kuma huta da kyau, ta yadda daga
baya zai iya shiga sahun tsofaffin shugabannin
Najeriya da suke da gogewa da hikima da basirar
da za su dinga bayar da shawarwari don ciyar da
kasar gaba.

A wasikar ya kuma tabo yadda rikicin makiyaya
da manoma yake daukar wani salo daban, yake
kuma kara muni ba tare da gwamnatin tarayya ta
dauki wani mataki na magance matsalar ba..

"Kuma abun takaicin shi ne yadda bayan kwana
guda da kashe kimanin mutum 73 a jihar Benue
sai ga shi wasu gwamnoni da ko sakon jaje ba
su aika ba sun goyi bayan Shugaba Buhari ya
sake neman tsaywa takara a 2019.

"Bai kamata su yi hakan a wannan lokaci ba, bai
kamata a mayar da batun rikicin manoma da
makiyaya na zarge-zargen juna ba. Dole ne
gwamnati ta jagoranci kawo mafita kan hakan,"
in ji Obasanjo.

A ganinsa, raunin gwamnati da suka dabaibaiye
kasa sun hada da karuwar talauci da
tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da azurta
dangi da abokan arziki da saba doka da wanke
ma su laifi, da kuma rashin sanin makamar hadin
kan kasa.

Tsohon shugaban ya ce, wadannan dalilan ne
suka sa ya yi watsi da jam'iyyarsa ta PDP domin
marawa 'yan adawa a zaben da ya gabata, domin
a cewarsa yana ganin matakin shi ne ya fi
dacewa da Najeriya da ma Afirka baki daya a
lokacin.

"Halin da Najeriya ta shiga ne ya sa jama'a suka
fito jefa kuri'a domin kawar da dan uwana
Jonathan".

Obasanjo ya ce duk da cewa shekaru hudu da
suka gabata ya yaga katin jam'iyyarsa ta PDP,
tare da fito wa baro-baro ya bayyana yin
bankwana da siyasa, amma hakan ba zai sa ya
kawar da kai da rashin nuna damuwa ga ci gaban
Najeriya da Afirka ba.

Sannan Cif Obasanjo ya ce, tun da farko ya san
inda shugaba Buhari ke da rauni, kuma ya taba
magana tare da rubutu akai tun kafin 'yan
Najeriya su zabe shi.

Kuma ya jefa ma shi kuri'a ne saboda a lokacin
ana neman wani zabi sabanin Jonathan.

A cewarsa wannan ne dalilin da ya sa ya
rubutawa Shugaba Jonathan wasika mai taken
"kafin lokacin ya kure", don ya dauki mataki cikin
gaggawa amma kuma ya yi watsi da
shawarwarin.

Obasanjo ya ce ya san Buhari tun kafin ya zama
shugaban kasa kuma ya taba fada cewa yana da
rauni a ilimin fahimtar tattalin arziki, amma ya
zata zai iya amfani da kwararru da za su iya
taimaka ma sa.

"Na san cewa ba za ka iya bayar da abin da ba
ka da wadatar shi ba, kuma tattalin arziki fanni
ne da ba ruwan shi da bin umurnin soja", a cewar
Obasanjo.

Tsohon shugaban ya ce akwai 'yan Najeriya da
dama da za su iya taimakawa a fannin ci gaban
tattalin arziki da kuma harakokin kasashen waje.

Sannan ya ce akwai manyan zarge-zargen da ake
game da wadansu da sai abin suke so ake yi a
fadar shugaban kasa da ya kamata ace tuntuni
an dauki mataki akai.

"Wannan ai yana iya zama rashawa" in ji
Obasanjo.

Tsohon shugaban na Najeriya ya kuma ce kin yin
watsi da irin wannan al'ada tare da kawar da kai,
tamkar rufa-rufa ne, maimakon gyara. Kuma
tabbatar da adalci ya shafi aiki da hannu masu
tsabta.

"Na san cewa shugaba Buhari zai yaki rashawa
da tayar da kayar baya, kuma dole a yaba ma sa
a ci gaban da ya samu a wadannan fannonin
guda biyu, amma fa har yanzu da sauran aiki".

Cif Obasanjo ya ce yadda aka bari rikicin
makiyaya da manoma ke kara girma ba tare da
neman mafita ba, baraka ce ga gwamnatin
Tarayya.

Ya ce wani abin bakin-ciki shi ne, yadda wasu
gwamnoni suka fito suna yi wa Buhari kamfen, a
yayin da a Benue ake zaman makokin binne
gawarwakin mutane 73 da aka kashe amma ba
tare da gwamnonin sun aika da sakon ta'aziya
ba.

Tsohon shugaban ya ce gwamnatin tarayya ce ya
kamata ta zauna ta samar da mafita ga rikicin
makiyaya da manoma domin kare rayuka da
dukiyoyinsu.

Obasanjo ya zana abubuwa uku game da
gwamnatin Buhari.

1.Gwamnatin 'yan uwa da abokan arziki, da
rashin daukar mataki a kan gurbatattu a fadar
shugaban kasa.

2.Rashin fahimtar siyasar cikin gida.

3.Daura laifin gazarar gwamnati a kan
gwamnatocin da suka gabata.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user