Muhimman ababe 7 da shugaba Buhari ya fadi a sakonsa na sabuwar shekara
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa za ta hana shigo da shinkafa daga kasar waje a sabuwar shekarar 2018.
Muhammadu Buhari ya sanar da wannan matakin ne a jawabin sabuwar shekara da ya gabatar wa ‘yan Nigeria ranar Litinin da karfe 7 na safiya.
Shugaban ya ce hakan ya biyo bayan bunkasar noma da aka samu a fadin kasar. Don haka ya umarci ‘yan Nigeria da su koma amfani da shinkafa ta gida wacce “tafi gardi kuma tafi lafiya.”
Baya ga wannan, Alfijir ta yi bitar wasu sakonnin guda bakwai da shugaba Buhari ya aikewa yan Nigeria:
Yace yan zagon kasa ne suka haddasa karancin man fetur. Don haka gwamnati za ta bankado su tare da hukunta su.
Gwamnati za ta bunkasa sufuri ta hanyar samar da layukan dogo da kuma inganta hanyoyin mota.
Za’a sake inganta wutar lantarki ta hanyar kara tashoshin samar da wuta da bunkasa hanyoyin rarrabata.
Gwamnati ta murkushe Boko Haram kuma za ta magance masu garkuwa da mutane nan bada jimawa ba.
Yakamata matasa su samawa kansu aikin yi maimakon neman aiki a gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu.
Babu bukatar sake fasalin tsarin mulkin Nigeria sai dai a mayar da hankali wurin aiwatar da shi bisa ka’ida.
Babu ruwan siyasa da addini ko kabilanci. Don haka yakamata ‘yan Nigeria su yi koyi da Yarabawa, wadanda su ba sa bari bambancin addini da siyasa su yi tasiri a siyasarsu.
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Hausa Times
0 comments:
Post a Comment