Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi
fatauci, sai ya bi ta kasar Yarbawa, Wawa ba ya
jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a wannan gari
su kuma ba su jin Hausa.
Amma duk da wannan
Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo
kofar gari, sai ya ga wani katon garken shanu
fari fat suna kiwo. Wawa ya yi mamakin wanda
ke da wadannan shanu masu yawa haka, sai ya
tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko
shanun wane ne wadannan.
Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, “Ni ban ji
ba.”
Wawa da ya ji haka tsammani ya ke “Ni ban ji
ba” shi ne mutumin da ke da shanun. Don haka
ya ce, “Ni-ban-ji=ba lalle yana da sukuni.” Ya
wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani babban
gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa
sunansa, samari, wa ke da wannan babban gida
haka?”
Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin
harshensa “Ni ban ji ba.”
Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, “Kai, ba shakka
Ni-ban-ji-ba ba wanda ya fi shi sule garin nan.
Wannan irin gida sai ka ce na Sarki.
Da ganin
wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin
nan sule ya zauna da gindinsa.” Ya haura
takalmansa ya wuce faram, faram, faram, faram,
har bakin kogin garin. Yana zuwa sai ya tarad da
wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa.
Wawa ya dubi kaya, ya ce, “Oi! Wannanjirgi ya
yiwo kaya!” Ya dubi wani nan kusa gare shi, ya
ce, “Dan’uwa, duk ko kayan nan na mutum guda
ne?”
Shi bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube
shi, ya ce, “Ni ban ji ba.”
Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce,
“masu gari! Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce
haushinsa. Ina ma Allah zai sa in gamu da
wannan mutum, ko wajen adonsa ma in more ma
idona!” Sai ya zauna ya huta, ya debi ruwa ya
sha, ya kama hanya zai wuce.
Ya kai kofar gari
ke nan, sai ya ga wani mattacce an dauko shi,
za a kai shi a rufe, wadansu na ta kuka. Wawa
ya tsaya yana dubansu. Tausai ya kama shi, ya
matsa wajen wata tsohuwa, ya ce mata, “Wane
ne wannan ya riga mu gidan gaskiya?”
Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta
ce, “Ni ban ji ba.”
Wawa da ya ji haka sai ya daffe kai, ya ce,
“Allah mai girma! Ka san kowa samun nan na
duniya ya ruda, ya shiga uku. Don Allah dubi abin
da Ni-ban-ji-ba ya tara.
Ga shi yanzu ya zama
sai labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi
ba! Cikin duk abin nan da ya tara, dubi dan
kyallen da za a kai shi da shi. Tun da ya ke
al’amarin nan haka ya ke, to, ni yanzu me ya
ruda ni har da na rabo da gida don rashin wadar
zuci? Ga shi Allah bai hana mini abin da zan ci
ba.
Watau ba dai abin da ya fid da ni gida sai in
sami abin alfahari in kara sabo.
Mhm, Allah ya
kiyashe mu da aikin Shaidan! Na gode Allah da
ya kawo ni nan na sami gargadi daga al’amarin
Ni-ban-ji-ba. Ba sauran abin da ya fi, sai in koma
garimmu, in dangana da abin da Allah ke ba ni
wajen ‘yar gonata.
Da ma an ce, “Gani ga wani ya isa tsoron Allah.