Fadar shugaban Najeriya ta karyata labarin da ke cewa dan shugaban kasar Yusuf Buhari ya rasu.
“Yusuf Buhari yana samun sauki a asibitin da yake jinya a kasar Jamus kuma likitoci suna sake duba kansa da ya bugu da kuma kafarsa,” in ji mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan shafukan zumunta, Malam Bashir Ahmad, a hirarsa da BBC.
Wasu shafukan intanet ne suka wallafa labarin da ke cewa dan gidan shugaban kasar ya rasu a ranar Talata da yamma.
Sai dai Malam Bashir ya ce labarin ba shi da kanshin gaskiya, yana mai cewa “ko jiya [Talata] na yi magana da ‘yar uwarsa da ke jinyarsa a asibitin Jamus kuma ta shaida min cewa yana samun sauki sosai.”
Sai dai tun bayan da aka tafi da shi Jamus ba a sake jin wani abu na labarin halin da yake ciki ba daga bakunan wadanda ke da kusanci da fadar shugaban, ko da kuwa a kafafen sada zumunta ne.
Kakakin na shugaban kasa bai fadi ranar da Yusuf Buhari zai koma Najeriya ba.
A farkon watan Janairu ne aka sallami dan Shugaban kasar daga wani asibitin Abuja bayan hadarin da ya yi a watan Disamba.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin da daren ranar Kirstimeti.
A cewar Garba Shehu, “Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki”.
‘Ya’yan masu hannu da shuni kan yi wasan tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da hatsari.
A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta haramta yin irin wannan tsere bayan wasu rahotanni da aka samu na tukin ganganci da masu tseren ke yi.
Source by ©Arewaplaza
0 comments:
Post a Comment