Saturday, 3 February 2018

Karanta Kaji: Abubuwan da Baku sani ba Dangane da Rayuwar Ummi Zee-Zee

Tura Wannan Zuwa Ga
Ummi Ibrahim ZeeZee dai ba bakuwa ba ce, shahararriyar ‘yar fim ce wacce ta ci zamanin ta tsakanin 2004 zuwa 2006.

A wannan hirar da tayi da gidan jaridar PREMIUM TIMES HAUSA, Ummi ZeeZee ta tabbatar da soyayyar da ke tsakanin ta da tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Babangida.
PT: Ummi mu na yi miki ta’aziyyar rashin mahaifin ki. Allah ya gafarta masa.
Zeezee: To na gode kwarai. Allah ya bada lada.
PT: Wane hali ki ke ciki na jimamin rabuwa da mahaifin ki, domin duk wanda ya san ki, ya san kin damu kuma kin kula da mahaifin ki sosai?
Zeezee: A gaskiya da mahaifi na ya rasu na shiga damuwar da ban taba shiga irin ta ba, kasancewar na shaku da baba na fiye da mama ta.
Domin ni ce ‘yar fari a wurin baba na. Ya shagwaba ni sosai, ya na so na fiye da sauran kanne na, ni ma kuma ina son baba na fiye da komai a duniya. Shi ya sa ma da ya rasu saboda kuka har ciwon wuya na yi, ba na iya hadiyar yawu sai da naga likita.
Yanzu haka baba na saura sati daya ya cika kwanaki arba’in da rasuwa, amma babu ranar da idan na tuna shi ba na kuka. Don haka ina mai addu’ar Allah ya sa aljanna fiddausi ce makomar sa, amin.
PT: An sha buga labarin soyayyar ki da Tsohon shugaban Kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Shin ko Babangida din ya samu yi miki ta’aziyyar rasuwar mahaifin ki?
Zeezee: Bai samu damar zuwa yi min ta’aziya ba, don ba shi da lafiya, kafar sa ta na ciwo, kowa ya san ya jima ba ya iya yin tafiye-tafiye, saboda ciwon kafa. Amma ya yi min ta’aziya ta waya. Kuma ya ce idan ya ji sauki zai zo insha Allah. Amma yaran sa da yawa sun zo sun yi min ta’aziya. Ka san shi ubangidan mutane ne da dama.
PT: Shekaru da yawa an daina ganin ki a fim. Me ya sa ki ka ja baya da harkar fina-finai?
Zeezee: Na ja baya ne saboda ka san kafin rasuwar baba na, daga watannin baya can, na fi zama a Dubai da kuma Cairo. Duk da nan ma Nijeriya ina zama din.
PT: Wadanne manyan finafinai ki ka yi can a baya farkon shaharar ki?
Zeezee: Na yi Gambiza, Jinsee, Aaliya, Masakin Kauna, Sanafahana da sauran su da yawa.
PT: Yaushe rabon da ki fito a fim?
Zeezee: A gaskiya na fi shekara goma. Tun Sanafahana ba a sake haska ni a fim ba.
PT: To yanzu me ki ke yi ne?
Zeezee: Harkokin kasuwanci na ke yi. Ina yin kwangiloli, harkar filaye da sauran saide-saiden harkokin kasuwanci.
PT: Har yanzu ki na mu’amala da ‘yan fim kuwa?
Zeezee: E ina yi. Idan mun hadu ana gaisawa, kuma a social media ma muna gaisawa sosai. Kuma nan gaba zan fara shirya finafinai ni ma.
PT: Da yanzu da can da yaushe aka fi samun riba a fim?
Zeezee: A yanzu an fi samun riba, sannan kuma na yanzu sun fi inganci, saboda kyamarorin yanzu ba irin na da ba ne.
PT: Su kuma masu fitowa a fim fa. Yaushe su ka fi samun kudi?
Zeezee: Su ma sun fi samu a yanzu. Domin ni ka san ko a lokacin da na ke yin fim, ni ba don neman kudi na ke yi ba. Kawai sha’awa ce. Kusan kashi 95% bisa 100% idan na yi fim ba na ma karbar ladar da za a biya ni..
Su kan su furodusoshin ma sun sani, ko sun ba ni wani lokaci a wurin zan rabar da kudin, ko kuma idan na je gida na ba mabukata.
PT: Kin taba cewa kin fi ‘yan matan fim aji. Shin har yanzu kin fi su ajin?
PT: Hahahaha. Wannan ma ai ba sai ka tambaya ba. Ka tuna fa ni da farko a Saudiyya ma na ke zaune.
Amma da na yi wani zuwa Nijeriya, sai na yi sha’awar harkar fim. To tun cikin 2004 ban sake zama Saudiyya ba, sai dai na je aikin Hajji ko Umra na dawo. Ni fa har yau ban taba fashin zuwa Umra ba. Kuma aikin Hajji na sha yi ba sau daya ko sau biyu ba.
PT: Mene ne sirrin sana’ar ki?
Zeezee: Na farko hakuri da juriyar fadi-tashi. Sannan kuma tashi neman na kai. Sai kuma babban ginshiki mutum ya sa Allah a dukkan al’amurran sa.
PT: Zeezee mene ne asalin soyayyar ki da IBB ne?
Zeezee: Hahaha! To ni dai tun ina sakandare IBB shi ne gwarzo kuma gwani na a duk cikin shugabannin kasar nan da aka yi. To daga baya muka hadu, kuma da aure na ke son sa.
PT: An sha buga wannan labarin soyayyar ki da IBB a jaridu, amma akwai masu tababa fa.
Zeezee: Ai sai su tsaya su na tababar su. Idan babu soyayya a tsakanin mu zan fito na ce akwai ne? Ya taba cewa karya na ke yi? Ko ya taba cewa na daina fada?
Babban mutum kamar IBB na isa na fito na yi masa karya ne? Idan bai san da maganar ba, ai sai ya fito ya ce karya na ke yi.
Shi ya sa wai idan ka ji an ce wai na ce a kasuwa na ke ko kaza da kaza, to ni ba a kasuwa na ke ba. Na fi karfin na yi tallar kai na. Aji na ya wuce na tallata kai na. Roko na a yi mana addu’ar fatan alheri kawai.
Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba
Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
ALLAH yabar Zumunci Amin
Source By ©Premium Times Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user