Monday, 19 February 2018

KARANTA KAJI: WAYYO ALLAH! BA MUTUWAR BA!! BALA'IN DAKE BAYAN MUTUWAR!!!

Tura Wannan Zuwa Ga

Annabi SAW ya kasan ce yana zagayawa a cikin
kashi daya na farkon dare (11-30pm) yana cewa:

"Ga mutuwa nan tazo da bala'in dake bayan ta"
Turmuzi ya rowaito.

Kadan daga cikin bala'in
bayan mutuwa sun hada da
Kwanciya a cikin wani ziririn rami(KABARI)
wanda mutum ko juyawa ba ya iya yi
Zaman BARZAHU, Mutum bai san rana/lokaci da
zai fita daga wannan yanayi ba
Bayan wannan zaman,Za'a tashi a firgice, kowa
zai dauki kayan laifin sa a kan shi kuma wallahi
komin nauyin su sai ya dauka
Masu korar mutane za suyi kora...
za'a fara
Gudun fanfalaki

Wani zufa ta rufe shi kamar wanda ya shiga
swimming pool, a haka zai ta gudu baya gani
Wani cikin shi yayi kato kamar yana dauke da
'yan adam duka, a haka zai ta gudu
Wani zai tashi da jikin shi, half na jikin ya shanye
a haka zai ta gudu
A haka dai mutane zasu yi ta gudu cikin nau'uka
daban-daban na wahala da azaba sakamakon
zunubai

Ana cikin wannan gudu sai haske ya dauke gaba
daya. Ga firgici ga wahala, Masu kora kuma suna
ci gaba da kora har dai a iso wani katon rami
wanda karka shin sa wutan JAHANNAMA ce

TSALLAKE SIRADI...

Ana nan cikin wannan tashin hankali, an tsaya
cak sai ace a fara tsallakawa ga tsananin duhu
Wasu da sun taka siradin zasu fada
Wasu suna tsallakawa ana yago naman su
Wasu su wuce da sauran jikin su da ya rage
Wasu kuma jikin ya kare. Ya Allah kayi mana
tsari da shiga wannan hali
Allahu Akhbar! Wasu gabobin su da suke Alwala
zasu haska masu hanya su wuce kamar keftawar
Ido cikin jin dadi da nishadi.

Wasu kuma duk hakan bazata faru gare su ba
domin zababbun Allah ne, suna can karkashin
inuwar Allah SWT,wato Al-Arshe
Ya Allah kasa mu cikin su.

Bayan an gama wannan sai a kora mutane zuwa
wani fili, a nan za'a tsaya cak kowa ba kaya a
jikin sa, ba Uhm ba...

Yinin wannan rana ya kai shekara 70 idan aka
kwatanta shi da na duniya

ALLAH yasa Mu da CE

Source by ©Halima Suleiman

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: