Friday, 2 March 2018

Takaitaccen Tarihin Abubakar Imam: Me yasa Aka Manta da Babban Marubucin Hausa Abubakar Imam? Shin Waye Wannan Abubakar Imam din??

Tura Wannan Zuwa Ga
Shine Mawallafin Littafin Magana Jari CE tinda ga NA daya har zuwa Na Uku Karanta Kaji Tarihin Rayuwar sa da Nasarorin sa.

Biography of Abubakar Imam

Sunan Abubakar Imam kusan daya yake da adabin Hausa, don duk inda aka yi maganar adabin Hausa sunan da ya kan fara fadowa shi ne Abubakar Imam.

An haifi Abubakar Imam a Kagara a 1911. Bayan ya sami karatun allo a gaban iyayensa, ya ci gaba da neman ilimi a Katsina a 1927, ianda daga bisani ya zama malamin makaranta.

A 1933 an yi gasar rubuce-rubucen adabin Hausa, inda aka gabatar da dokar a yi rubutu da Hausar boko, sabanin yadda ake rubutu da Ajami a baya, yayin da gwarzon ya zama zakara ya yi cara, musamman don Turawa sun karfafa wa matasan wancan lokaci da rubuce-rubuce, inda aka ga ribar hakan.

Ya ci gasar da littafinsa Ruwan Bagaja (1933), inda littafin ya shiga gaban littattafan Gandoki na dan uwansa Muhammadu Bello da Shehu Umar na Abubakar Tafawa balewa. Yayin da ya bar koyarwa ya shiga harkar fassara, inda ya rubuta Magana Jari Ce (1936) daga tushen tatsuniyoyin da labaran Larabawa, Turawa da kuma na Gabas, watau Indiya da Caina, inda kaifin basirarsa ta fito, yayin da yake hausantar da labarin sai ka ce sun faru a kasar Hausa.

A 1939 aka ba Malam Abubakar mukamin Edita na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, wadda ita ce jaridar da aka fara kaddamarwa a kasar Hausa, kuma ta sami karbuwa. Zuwa 1943 Malam Abubakar ya kai ziyara Ingila, inda ya nemi Gwamnatin Biritaniya ta kawo kayan aiki, ta yadda za a yi yaki da jahilci a Arewacin Najeriya. 

Wannan ya zama matakin da aka bi wajen kafa kamfanin Gaskiya Corporation a 1945. Nan aka ba Malam Abubakar jagorancin bangaren wallafa littattafai a 1951, watau ya zama mutum dan kasa na farko da aka ba mukamin da ya zama sai Turawa suke rikewa a da.

Malam Abubakar dan baiwa ne, yana magana da harshen Hausa, Larabci da Turanci, ganin karbuwarsa shi ya sa mutane suka yi masa kamfen don ya tsaya takara a Majalisar Tarayya a zaben 1951. Ganin daukakarsa ne Malam Sa’adu Zungur (1915-45), ya ce shi ne direban Arewa, yayin da ya sha gwagwarmaya a siyasance sai ya bar siyasa ga matasa, inda ya koma ga aikinsa na ci gaba da rubuce-rubuce.

A fagen rubuce-rubuce, Malam Abubakar ya ba da gagarumar gudumuwa, inda ya zama shi ne wanda ya fara fito da wasan kwaiwayon da aka taka rawarsa a dandali da harshen Hausa. Ya rubuta littafin Tarihin Annabi Muhammadu, sannan ya rubuta Tafiya Mabudin Ilimi a 1943, inda ya ba da labarin zuwansu Biritaniya da kuma zuwansa Makkah a 1953.

Daga 1959 zuwa 1966, Malam Abubakar ya dukufa wajen aikin gwamnati, inda ya zama memba a Hukumar Kula Da Ma’aikata Ta Lardin Arewa kuma ya ci gaba da aiki a lokacin mulkin soja. Daga bisani ya kamu da rashin lafiya kuma ya rasu a Zariya a ranar Juma’a 19 ga Yuni 1981. Ya bar mata daya da ’ya’ya 14. Yayin da mutanen Zariya suka mallake shi a matsayin dansu kuma mutanen Katsina na cewa nasu ne, musamman don an nada shi Walin Katsina; Kwantagora na cewa nata ne kuma Barno na cewa ai daga can ya fito.
Baiwarsa ta burge Baturen nan Mista East, ta yadda ya bukaci ya rubuta Magana Jari Ce, inda ya dukufa a cikin watanni shidda ya yi bakandamiyarsa, kuma littafin da aka fi sani a harshen Hausa, aka buga na farko a 1937, sannan na biyu da na ukun suka fito a 1938.

A lokacin da ya fara aiki a kamfanin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, ya nuna kwarewa inda aka rika sayen jaridar a kowane sashen Najeriya ba Arewa kadai ba, har da Ikko; yayin da ya zama jaridar na dauke da manufofin gwamnati tare da ra’ayoyin jama’a a kan duk abin da aka rubuta ko aka aiwatar, koda zai zama suka ga hukuma ko mahukunta. A matsayinsa na Editan jaridar, ya yi hobbasa wajen yaki da jahilci, zalunci da lalaci, inda ya nuna babban makamin da za a yaki wadannan dabi’u shi ne ilimi, musamman ilmin da zai zo tare da tarbiyya; yayin da ya shaida wa Lord Lugard a wata wasika cewa: “Ba abin da yake sauya mutum da duniya baki daya kamar ilimi,” da zarar an ilimantar da mutane, an sauya su.

A fahimtar Malam Abubakar, ilimi ya wuce karatu da rubutu, aiki da karatu shi zai warware duk matsalolinmu, ya zama mafita gare mu, sabanin yau inda ake ta gasar gina jami’o’i da bautar kwalayen shahadu da satifiket. Bayan an bar ilimin firamare da na sakandare a baya, to ta yaya za a sami ginin kwarai bayan babu fandisho? Don a yau kusan bambancin daliban firamare da jahilai kadan ne, kai wani sai ya kare sakandare bai iya rubuta wasika da Hausa ba! Allah Ya sauwake.
Abubakar Imam Ya jaddada cewa ilimi ke haifar da shuwagabanni nagari kuma ba lallai sai shugaban ya fi kowa ilimi ba amma ya kasance wanda zai iya aiki da iliminsa, sannan ya zama yana da karbuwa a wajen jama’a, kuma wanda zai ba mutane muhimmanci, inda yake cewa: “Amfanin ilimi aiki da shi.”
Duk da haka ya goyi bayan a kara neman ilimi, inda ya karfafa hujjarsa da cewa mai karamin ilimi kamar takardar firamare kuma yana aiki da shi, ya fi mai digiri ko difloma kuma ba ya aiki da shi, amma idan aka sami mai digiri kuma yana aiki da shi, zai kawo gagarumin ci gaba.

Wani abin takaci shi ne, idan muka dubi nazariyar Malam Abubakar, sai mu ga mutane nawa suke da digiri a yau amma masu firamare a da sun fi su kwazo da amfani da kwakwalwarsu?

A ranar farko da ya fara aiki a gidan jarida aka gane baiwarsa da basirarsa, inda aka yi wata hayaniya, inda ya nuna ba zai iya kiran Almasihu (Jesus) dan Allah ba, inda wasu suka tsaya kan cewa a bar shi a matsayin Annabi Isa kawai, sai Malam Abu ya ce, ai Jesus ya fi dacewa da Isa dan Maryam, kuma kowa ya amince.

Shekaru goma sha shida da ya yi a matsayin edita, wani lokaci yakan sha wuya wajen daidata bukatun ’yan mulkin mallaka da na ’yan kasa, wani lokacin yakan sami sabani da ma’aikatan gidan jaridar ko kamfanin, don wani na son wata bukata ko son ransa. Hakan ta sa shi a tsakiya, wasu na masa kallon kamar dan koren Turawa, su kuma Turawa wani lokaci suka dauke shi a matsayin dan adawarsu.

Ya sami daukakar da ba za ka hada shi da kowa ba a Hausa ko Fulanin kasar Hausa sai Shehu Usman danfodiyo da kanensa Sheikh Abdullahi danfodiyo da dansa Sultan Muhammadu Bello. Su ma don irin gagarumar gudummuwar da suka kawo, wadda har yau ake cin ribar iliminsu.

Zuriyarsa sun yi wani yunkuri da yin wani gidan tarihi, inda aka aje kayansa da hotunansa, watau Cibiyar Abubakar Imam a Zariya, sannan abokinsa marigayi Abubakar Mora ya yi wa tarihin rayuwar Abubakar Imam aikin edita a 1989, kuma aka buga shi a Zariya, sannan a kwanan nan kungiyar Marubuta (ANA) tare da wasu malaman Jami’ar Bayero a Kano sun karrama shi. Duk da haka Malam Abubakar ya sami gata ga masu son gaskiya da ci gaba, kamar yadda ake yunkurin bude masa wani shafin yanar sadarwa watau: www.abubakarimam.com

Idan muka lura har yau, yana da wuya ka sami malaman jami’a wadanda ake kira da farfesoshi, Shehunnai ko malamai da irin wayewar Abubakar Imam, ko don ya lakanci harsunan uku watau Hausa, Larabci da Turanci, yayin da a yau malaman jami’a ba ruwansu da Larabci sai Turanci, haka malaman addinin ba ruwasnu da Turanci, kuma kadan suka iya Larabcin! Balle wadanda suke kiran kansu marubutan Hausa a yau, wadanda Hausar ma ba ta ishe su ba.

A dunkule, ya kamata marubuta watau su yi kanshin turare ba kaurin makeri ba. Ta yaya za a kama Abubakar Imam a kan abin da ya rubuta ko a haramta karanta littattafansa? Lallai wannan abin tunani da taunawa ne ga marubutan wannan zamanin da ake sa masu dokoki.

Wai me aka yi bayan Abubakar Imam? 

Maganar gaskiya ba abin da malaman jami’a suka yi wajen ganin sun kama kafarsa, duk da ya yi shekaru nawa da rasuwa, kuma idan muka lura da shekarunsa, nawa ya ci gasa, kuma yadda ya sami wayewar kai a duhun zamaninsa, sai mu auna da duk da haske da ci gaban sadarwa irin su intanet me aka yi? Imam ya shiga sahun gaba wajen yin shimfida, sannan ya yi rubutu a kan kowane nau’in rubutu, adabi, addini, fasaha. kokarinsa ya wuce na samun yabo a wajen marubuta ko malamai da ’yan jarida, ya kai ga cewa ’yan siyasa, ’yan kasuwa da talakawa sai sun dauki darasi game da rayuwarsa, don ya yi rubutun da zai amfani kowa daga cikinsu. 

Ganin baiwa da basirarsa ya sa ya zama daga cikin manyan na hannun dama da mashawartan Malam Aminu Kano (1920-83) a zamanin da aka sha gwagwarmayar siyasa.

Amma Alhamdu lillahi da a yau an kafa jaridu masu zaman kansu, wadanda suka tashi tsaye irinsu Aminiya da Leadership Hausa, sai kuma kafafen yada labarai na waje wadanda suke fassara wasu abubuwa a kan lokaci, ta yadda za mu fahimci ina duniya ta dosa.

A ra’ayina, ya kamata akwai dakin karatu ko sakatariya ta marubuta a Kano da za a sa wa sunan Abubakar Imam kuma ko babu ya kamata shugabannin kungiyar marubuta su mayar da hakan babban burinsu, ta yadda za a sami dakin taro, ba wai kowane wata sai an ara ba. Wa zai hada Abubakar Imam da Janar Murtala Muhammad, kai ko da ya kai za a rika tara kwandala a kowane taro kuma wasu attajirai a cikin marubuta su ma sai su ba da tasu gudummuwar, ta yadda za a mallaki fili kuma a nemi taimakon gwamnati da fada don a gine. Wani abu da ke kara daure min kai shi ne, har yau wasu ba su san hoton Abubakar Imam ba. Hoton da ya kamata akwai shi a laburari, gidajen jaridu, madaba’u da dakunan marubuta, abin da in a Turai ne har gunkinsa sai sun yi don kiyaye tarihi, mu a nan sai ka nemi hoton ka rasa, ko a ce ashe da wannan shi ne Abubakar Imam!

Sannan ina ganin ya kamata akwai (stamp) kan sarki mai hoton Abubakar Imam koda a nan Arewa amma shin wai me ake yi da kan sarki? Wa yake rubuta waskikar? Ko ina zancen zumuncin da ke tsakanin marubuta? Kai, ya kamata marubuta su yi damara don ci gaba da tsohon yakin iyaye da kakaninsu watau yaki da jahilci. dakuna a makarantun sakandare da firamare, tare da sa littafin tarihin rayuwarsa a manhajar makarantun firamare. Ko ma a gina masa jami’a ko a sa sunansa a wani bangare na makarantun gaba da sakandare. Imam ya wuce yadda aka aje shi a gefe. Ya kamata marubuta su rika yi wa Abubakar Imam mauludi kowace shekara.

Duk da yadda ake sukarsa a matsayin mai fassara, su farfesoshin me suka yi? Shin sun karfafa wa dalibai su yi bincike ko da fassarar ce? Ai ita kanta fassara ai iyawa ce, kuma wani ilimi ne mai zaman kansa. 

Shakka babu a yau duk abin da mutum ya rubuta da Hausa sai a ce shi ne na farkon yinsa. Wani abin mamaki shi ne har yau ba a daidaita rubutacciyar Hausa ba, yayin da sai a rubuta abu daya da harufa daban kuma a amince da duk daidai ne. kai, wasu abubuwan ma na wannan zamanin an ki a amshe su sai dai an fassara su, watau abin da ya kamata a fassara shi ba a yi ba.
Abin da ya kamata a hadiye, a hausantar da shi, an bar shi sai an fassara kuma wai har irin wadannan farfesoshin za su muzanta malaminmu Abubakar Imam!

Daure, ya rubuto daga kofar kauna Katsina (07035986444)



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Aminiya
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user