Friday, 2 March 2018

Hotuna Da Cikakken Tarihin Dr Rabi'u Musa Kwankwaso: Abubuwan Da Yakamata Ku sani Dangane Da Rayuwar Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Tura Wannan Zuwa Ga
An haifi Rabiu Kwankwaso a ranar Lahadi 21 ga watan Oktoba na shekarar alif dari tara da hamshin da shida (21 October 1956) a kauyen Kwankwaso dage karamar hukumar Madobi a jihar Kano ta Najeriya.




Mohammed Rabi’u Musa wanda aka fi sani da “Rabiu Kwankwaso” wani dan siyasa ne a Najeria.

Rabiu Kwankwaso ya kasance gwamnan Kano na farko a jamhuriyya ta hudu wanda aka zabe shi a karkashin jam’iyar PDP a shekarar alif dari tara da casa’in da tara zuwa shekara ta dubu biyu da uku (1999 – 2003). Kwankwaso ya fadi zabe bayan ya sake tsayawa a karo na biyu a shekara ta dubu biyu da uku (2003) inda Mallam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar APP ya kayar da shi. Sai dai bayan faduwar sa a watan Yuli na wannan shekara aka nada shi a matsayin ministan tsaro karkashin jagorancin shugaban kasa Olusegun Obasanjo .

Rabiu Kwankwaso ya sake zama gwamnan na jihar ta Kano a shekarar 2011 bayan sake tsayawa zabe da yayi a cikin ita jam’iyyar ta PDP.

Iyali da ‘Yan Uwa

An haifi Mohammed Rabiu Musa a ranar Lahadi a kauyen Kwankwaso na garin Madobi daga mahaifin sa mai suna Musa Kwankwaso. Duk da cewa yana da ‘yan uwa sosai, sai dai Rabiu ya kasance jigo a cikin dangin sa kasancewar yayi fice sosai. Yana da aure. Allah Ya albarkaci Rabiu Musa iyali da kuma guda shida.

Rayuwar Makaranta da Neman Ilimi


Rabiu Musa ya halarci makarantar firamare a garin Kwankwaso, inda dana nan ya samu ci gaba izuwa makarantar kwana ta Gwarzo duka dai a neman ilimin firamare. Sannan sai makarantar kere-kere dake garin Wudil da kuma kwalejin fasaha ta Kano bayan daga nan ya karasa makarantar foliteknik nake garin Kaduna inda ya samu yin difloma ta kasa da kuma babbar difloma ta kasa. ya samun yin karantar gaba a garin London dake kasar Ingila a kwalejin Middlesex a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyu zuwa da uku (1982-1983). Kwankwaso ya ci gaba da karantun sa a jami’ar fasaha dake Loughborough duka dai a kasar Ingila a shekarar alif dari tara da tamanin da uku zuwa da biyar (1983-1985) inda ya samu lambar babban digiri mai suna Masters a turance a fannin fasahar ruwa.

Kwankwaso ya kasance hazikin mutun a kusan dukkan lokutan karatun sa musanma ta bangaren tsayawa da yayi domin ganin cewa ya kammala karatu cikin nasara kuma ba tare da bata lokaci ba. Ya kasance dalibi wanda kullum yake a sawun gaba wajen karatu da yin dukkan wani aikin aji da akan bashi. An zabi Kwankwaso a matsayin shugaban dalibai a lokacin karatun sa, sannan ya kasance zababbe a kungiyar dalibai ta jihar Kano.

Aiki


Mohammad Rabiu Musa ya fara aikin gwamnati a shekarar alif dari tara da saba’in ba biyar (1975) a ma’aikatar ruwa ta jihar Kano mai suna (WRECA), inda yayi aiki na tsawon shekaru goma sha bakwai a fanni daban-daban inda har ya zama babban inginiya.

A shekarar alif dari tara da casa’in da biyu Kwankwaso ya kasance zababben dan majalisar wakilai ta kasa bayan shigar sa siyasa gami da tsayawa zabe a karkashin jam’iyyar SDP wacce Shehu Musa Yar’adua ya jagoranta. Majalisar wakilai ta wannan lokaci ta zabi Rabiu Kwankwaso a matsayin mataimakin kakakin majalisar inda yaci ba tare da hamayya ba. Kuma wannan matsayi da ya samu ya kasance abin haskakawar sa a siyasar Najeriya.

A lokacin gyaran kundun tsarin mulki na shekarar alifc dari tara da casa’in da biyar an zabi Kwanwaso a matsayin wakili daga jihar Kano kasancewar sa mamba a Peoples Democratic Movement karkashin jagorancin Shehu Yar’adua. Ya samu shiga jam’iyyar PDP a shekarar alif dari tara da casa’in da takwas a karkashin tafiyar Peoples Democratic Movement daga shiyar jihar Kano bisa jagorancin Musa Gwadabe, Sanata Hamisu Musa da Abdullahi Aliyu Sumaila.

Gwamna

Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance zababben Gwamnan Jiha mafi girma a shiyar Arewacin Najeriya wato Kano daga alif dari tara da casa’in da tara zuwa shekara ta dubu biyu da uku (1999 – 2003) a karkashin jam’iyyar PDP.

Kwankwaso ya dauki rantsuwar mulki tare da mataimakin sa Abdullahi Umar Ganduje wanda ya kayar a lokacin zaben fitar da gwani da yayi kafin zabe.

Kwankwaso ya samu tsayawa zaben fitar da gwani tare da Ganduje, Engr. Mukhtari Zimit da Kabiru Rabiu. Bangaren ‘yan Santsi sun kasance a bayan takarar Ganduje inda Kwankwaso ya samu kayar dashi wanwar a zaben na fitar da gwani.
Kwankwaso a wannan lokaci bai samu cin zabe da ya sake tsayawa ba domin dawowa a karo na biyu inda Mallam
Ibrahim Shekarau wanda na jam’iyyar APC ya kayar dashi. Zaben Shekarau a matsayin Gwamna a Kano ya kasance abin tattaunawa kasancewar sa wanda Kwankwaso ya kora daga babban mukamin Permanent Secretary kuma ya mayar da shi malamin makarantar kwalejin kimiya ta Kano saboda wata ‘yar takaddama da ta shiga tsakanin su.

Kwankwaso ya samu damar komawa kujerar ta Gwamna a Jihar Kano karo na biyu shekaru takwas bayan ya fadi zabe a yayin da Shekarau ya kammala zagayen sa na biyu inda ya kayar da dan takarar ANPP Mallam Salihu Sagir Takai a zaben da aka gudanar a ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar dubu biyu da sha daya (26 April 2011) da kuri’u dubu sittin da uku inda aka rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu na dubu biyu da sha daya (29 May 2011) tare da Abdullahi Umar Ganduje a matsayin mataimakin sa.

Siyasa

Rabiu Musa Kwankwaso ya kasance jigo a tafisar siyasar Nigeria. Ya shiga siyasa ‘yan shekaru kadan da barin aikin gwamnati. Kwankwaso ya kasance mai kwakwarmaya sosai kuma tsayayye wajen dagiya da juriya irin ta siyasa inda ya rike mukamai daban-daban a fannin siyasar Najeriya.

Rabiu Musa ya fara siyasar sa a jam’iyyar SDP inda ya zama zababbe a karshin ita jam’iyyar da SDP a shekarar alif dari tara da casa’in da biyu (1992). Sai kuma ya samu komawa jam’iyyar PDP bayan kafa sabbin jam’iyyu da akayi a kudurin mika mulki izuwa hannun farar hula da Shugaban Kasa Abdulsalami Abubakar yayi bayan ya dare mulki sakamakon mutuwar Shugaba Sani Abacha .

A ranar 26 ga watan Nuwamba na shekara ta dubu biyu da sha biyar Kwankwaso ya samu sauya shekar siyasa inda ya koma jam’iyyar adawa ta APC wanda ya sami yin takarar tsayawa zaben share fage na shugaban kasa da jam’iyyar tayi a garin Legas a watan Disamba na shekara ta dubu biyu da sha hudu (December 2014).

Zaben watan Disamba na shekara ta dubu biyu da sha hudu (December 2014) Rabiu Musa Kwankwaso ya sha kaye bayan Muhammadu Buhari shima dan takarar share fagen shiga zaben shugaba Kasa din ya lashe. Kwankwaso ya kasance na biyu inda ya zarta tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar .

Mukamai

Kwankwaso ya rike mukamai da yawa a Jihar Kano dama Najeriya baki daya wadanda suka haka da aikin gwamnati dana siyasa baki daya.

A shekara ta 2003 bayan ya fadi zabe a karo na biyu a takatar Gwamnan Jihar Kano Shugaban Kasa Olusugun Obasanjo ya nada shi a matsayin babban Ministan Tsaron Najeriya wanda ya rike na tsawon shekaru hudu. Sannan an sake nada shi a matsayin Jakadan Najeriya a Dafur dake Kasar Sudan a karkashin gwamnatin Umar Musa Yar’adua .

1. Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya – Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993
2. Gwamnan Jihar Kano – 29 Mayu 1999 zuwa 29 Mayu 2003
3. Ministan Tsaro na Kasa – Yuli 2003 zuwa 2007
4. Babban Jakadan Najeriya a Dafur – 2007 – 2011
5. Gwamnan Jihar Kano – 29 Mayu 2011 zuwa 29 Mayu 2015
6. Satanan Kano ta Tsakiya – 11 Yuni 2015 har izuwa yanzu.

An zabi Mohammed Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Sanata daga Kano ta tsakiya a zaben dubu biyu da sha biyar (2015) wanda ya tsaya bayan faduwar sa zaben share fagen tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.


Takaitaccen Tarihin Nasir Ahmad El-rufa'i: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Siyasar Arewacin Nigeria Nasir Ahmad El-Rufa'i - Hotuna da Cikakken Tarihi

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.


Source: Muryar Arewa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user