Wani malamin makaranta da ke koyar da darasin Lissafi a Makarantar Sakandaren garin Ekwulobia a daramar Hukumar Aguata, Jihar Anambra, Chiadikobi Ezeibekwe, ya auri danwarsa ’wacce suke uwa daya uba daya.
Angon, mai shekara 23 ya auri danwarsa mai shekara 16, inda ya ce Allah ne Ya ba shi umarnin ya auri ’yar uwar tasa. Ya karanta wa manema labarai wani sashi a cikin Baibul a surar Kubawar Shari’a (Deuteronomy), inda ya ce Allah ne Ya umarce shi cewa ya dulla aure da ’yar uwarsa. “daya daga cikin alfanun wannan auren shi ne, yana dauwamar da zumunta har abada,” inji ango Chiadikobi.
Ya ce bai biya ko kwabo a matsayin sadaki ba a yayin dulla auren. “Ni ba na jin cewa na aikata wani laifi kuma ba na jin kunyar al’amarin a jikina ko kadan, kuma babu wani abu da nake ji yana yi mini barazana kan wannan mataki, Allah ne kadai zai iya hana mu zama a matsayin miji da mata da ita,” inji shi.
Shi dai wannan aure, yayan angon ne mai suna Chijioke Ezeibekwe ne ya daura shi a cocinsa da ke garin Agba. Sai dai daga bisani matasa sun harzuda, inda suka done cocin, mai suna ‘Dwelling Fullness of God Church.’
A nasa bangaren, maigarinsu Gabriel Ezeukwu ya ce, “Matasa a dauyen Agba ne suka harzuda, inda suka nuna cewa wannan aure bai dace da al’ada ba, don haka suka cinna wa cocin da aka daura auren wuta. Sai dai na hana su daukar wani mataki kan angon da ’yan uwansa. Idan da a da ne aka yi wannan, da gaba daya za a done dukan zuri’ar gidansu, saboda wannan babban laifi ne da ya deta dokokin al’ada.”
Haka kuma, babban wan angon, wanda kuma shi ne shugaba a gidansu, mai suna Emeka Ezeibekwe ya yi alkawarin cewa ba zai taba lamunta auren ya dore ba.
“Sai dai a bayan raina, amma ba zan taba aminta dannen nawa su zauna a matsayin miji da mata ba. Wannan ba za ta taba sabuwa ba,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra, Nkeiruka Nwide, ta shaida wa manema labarai cewa, ita ma ta ji labarin faruwar al’amarin, sai dai ba a kawo musu rahoto a hukumance ba.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum
An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.
Source by ©Hausa Mini
0 comments:
Post a Comment