Kalli Hotunan Sun Kayatar da Masoyan Buhari
Ina Da Ja Dangane Da Kalaman Shugaban Kasa Buhari Akan
Matasan Najeriya A Kasar Ingila
Sunana Bashir. Na kammala karatun digiri na, sannan na
kammala yi wa kasa hidima a shekarar bara, kuma ni ba
malalaci ba ne kamar yadda ka fada a taron kasuwanci na
commonwealth a London kuma na san akwai dubban matasa
kamar ni wadanda suma ba malalata bane.
Mai girma jagoran kasa ka umarce mu da mu shiga cikin shirin
N-Power, Youwin, da sauran su amma duk da haka ba a bamu
damar shiga cikin shirin ba. Muna aiki tukuru don samun abin
da zamu ci. Amma ka ce muna jiran manyan aiki, kamar yadda
na fada a sama, mun ciccike neman shirin N-power (# 30,000
kowane wata) amma ba a sanya sunayen mu ba, yaya kake
tsammanin za mu sa rai da babban aiki bayan ko wa’yan nan
ma bamu samu ba.
Dole ne gwamnati ta ba mu ilimi mai kyau sannan kuma ta
inganta asibitocinmu.
Sannan Baba inaso in fadama cewa
matasan kasar nan ba malalata bane yanzu, wai to ma in ma
malalatan ne waye ya jefa su cikin lalacin?
Baba na cike shirin Youwin a bara, nayi aiki tukuru don ganin
nasami nasarar wannan shirin, Na kashe kudi fiye da 10,000
don kallon laccoci a yanar gizo, sannan na amsa tambayoyi,
na sami kashi 80 bisa dari amma saboda shirin na iyalai da
abokan arziki ne sai muka ji anayi.
Baba na kasance manomi a bara, Na shuka alkama, Na samu
gona fiye da 1 hectare, na bata lokacina a gonar don ganin na
girbin abinda zai sa gobe na dawo. Ban sami tallafi daga
gwamnatin tarayya ko gwamnati jaha ba, nayi mata hidima
daga kudin ajjihuna da kuma kadarorina dana siyar, amma
rashin sa’a na ƙare da buhun alkama 12.
Baba Na bude shagon gudanar da harkar yanar-gizon, na saka
duk wani abu da ake bukata amma yawan zuwan masu karɓar
haraji na karuwa daga kan gwamnatin tarayya har zuwa
gwamnatin jihar, harajin allon shaida, takardar kudin wuta,
ma’aikatar sadarwa, kudaden shiga na jihar da sauransu.
Baba Menene kake tsammanin mutumin da yake
gwagwarmayar irin wannan rayuwa ya zama malalaci? Kuma
akwai dubban matasan da ke gwagwarmaya fiye da irin
wannan da nake yi. Idan ka ce ka saukaka mana, na san akwai
dubban matasan da zasu sauke lalacin da kake fada.
Baba ban kasance a nan ba don kalubalantar ka, amma sai
don kalubalantar wasu kalmomi da naji ka fada a wajen taron
kasuwanci na Commonwealth a London. A karshe ina fatan
wannan rubutun zai isheka ta hanyar danka Yusuf, wanda yake
lallatsa wayarsa yake ciki na’urar sanyaya daki kuma ya kunna
talabijin don kallon fina-finan turawa, ina fatan sakon zai same
shi cikin koshin lafiya.
Ina kuma mai yi maka addu'a da Allah ya dawo mana da kai
gida lafiya daga London
Bashir B. Yakasai
Global Youth Ambassador
Source by ©Muryarhausa24.com