Shugaba Buhari ne shugaban kasar Afrika na farko da
gwamnatin Trump ta gayyata zuwa fadar gwamnatin ta domin
tattaunawa.
1. Yaki da ta'addanci: Najeriya ta shiga shekara ta tara tana
yaki kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ga
kuma sabon rikicin makiyaya da ya kunno kai.
Shugabannin biyu zasu tattauna hanyoyin da zasu hada karfi da
karfe domin kawo karshen aiyukan ta'addanci a Najeriya.
Trump ya taba sukar tsohon shugaban kasar Amurka Barack
Obama saboda kin sayar wa da Najeriya makamai.
2. Inganta dangantaka tsakanin kasar Amurka da Najeriya da
kasashen Afrika: Gayyatar shugaba Buhari wata manuniya ce
cewar kasar Amurka ta yarda da cewar Najeriya ce ga
kasashen Afrika.
Kalaman kaskanci da shugaba Trump ya yi a kan kasashen
Afrika a watannin baya ya jayo barkewar cece-kuce da
kunakuni daga shugabannin duniya da 'yan Afrika.
3. Tazarce: Shugaba Buhari da Trump zasu sake yin takara
domin zarcewa a kan mulki. Shugaba Buhari zai yi amfani da
damar ziyarar domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin sa ta
samu a bangaren noma domin samun goyon bayan kasar
Amurka a zaben shekarar 2019.
4. Tattalin arziki: Kasar Amurka ta nuna damuwar ta a
kwanakin baya dangane da yadda kasar China ke yunkurin
mamaye kasuwancin kasashen nahiyar.
A kwanakin baya kasar Amurka ta turo tsohon sakataren
gwamnatin ta, Rex Tillerson, domin nunawa kasashen Afrika
illar kulla harkokin tattalin arziki a nahiyar Afrika. Saidai bai
karasa ziyarar ba shugaba Trump ya kore shi daga aiki.
Source by ©Hausa Naija
0 comments:
Post a Comment