Tshohuwar matar tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a
wannan jamhuriyar Cif Olushegun Obasanjo mai suna Taiwo ta
bayyana ra'ayin ta na cewa ko kusa ba ta fatan shugaban
kasar Najeriya na yanzu ya sake tsayawa takara a 2019.
Uwar gida Taiwo din dai ta bayyana ra'ayin nata ne a yayin
wata firar da ta yi da majiyar mu a karshen sati inda ta ayyana
cewa ita yanzu tana ba shugaba Buhari shawara da ya tattara
kayan sa ya koma jihar sa ta Katsina.
Majiyar mu ta samu cewa haka zalika tsohuwar matar ta
Obasanjo har ila yau ta kuma kara da cewa ita tana ma rokon
Allah da kar ya ba shugaba Buhari damar zarcewar kamar dai
yadda ya hana tsohon mijin ta yin tazarce karo na uku a
shekarun baya.
A wani labarin kuma, Biyo bayan ayyana kudurin sake tsayawa
takarar tazarce da shugaba Muhammadu Buhari yayi a satin da
ya gabata yayin taron masu ruwa-da-tsaki na jam'iyyar APC
mai mulki, alamu na ta nuna yiwuwar ficewar wasu jiga-jigan
jam'iyyar zuwa wasu jam'iyyun domin samun tikitin takara a
2019.
Duk da dai har yanzu ba'a fallasa sunayen masu neman ficewa
daga jam'iyyar ba, amma dai jam'iyyun da ake tunanin za su yi
sabbin baki sun hada da Social Democratic Party (SDP),
Labour Party (LP), Accord Party (AP) da kuma hadakar nan ta
tsohon shugaba Obasanjo ta Coalition for Nigeria Movement
(CNM).
Source by ©Hausa Naija
0 comments:
Post a Comment