Sunday, 29 April 2018

Karanta Kaji: Duniya tazo karshe Za'a hana kiran Sallah a kasar Norway

Tura Wannan Zuwa Ga

Wasu manyan jam'iyyu guda uku masu suna
(Fremskrittspartiet-Frp) wadanda suka kafa gwamnatin hadin
guiwa a kasar Norway sun bukaci a daina barin sautin muryan
kiran Sallah yana fita zuwa wajen masallaci kasar.

Shugaban kungiyoyin 'yan gudun hijira Jon Helgheim ya
bayyanawa manema labarai cewar jam'iyyar tasu zata zauna ta
tattauna a taron da zata yi na karshe a karshen wannan satin
akan bukatar sun ta a dauki matakin da za'a hana sautin kiran
Sallah da ake yi a cikin massalatai fita waje a fadin kasar.

Helgheim, ya kara da cewar bai san abinda kungiyar kare
hakkin dan Adam ta duniya zata ce akan batun nasu ba, tunda
kungiyar ta bayyana cewar hana kiran Sallah baki daya take
hakkin dan adam ne, amma mu muna bukatar wadanda suke
zama kusa da massalatai su dinga samun sukunin rayuwa ba
tare da kiran sallar yana damun su ba.

A kasar Norway dai ana kiran sallah ne a cikin masallaci tare
da yin amfani da lasifika domin wanda yake nesa ya san cewar
lokacin sallah yayi.

Source by ©Hausa Naija

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: