Monday, 30 April 2018

KARANTA YANZU KAJI: ABUBUWAN DA YAKAMATA KASANI DANGANE DA ZIYARAR SHUGABAN NIGERIA BUHARI KASAR AMERICA - HOTUNA DA LABARI

Tura Wannan Zuwa Ga

A yau litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da takwaran sa
na kasar Amurka, Donald Trump, suka gana tare da yin jawabi
ga manema labarai tare.

Ga wasu abubuwa biyar da shugaba Trump na Amurka ya fada
yayin ganawar ta su

1. Shugaba Trump ya bayyana cewar baya nadamar kalaman
sa a kan batun 'yan ci-rani daga Najeriya dake tururuwar zuwa
Amurka da kuma wadanda suke can amma basa kaunar
dawowa Najeriya.

2. Shugaba Trump ya musanta cewar sun yi tattauna da
jami'an gwamnatin sa inda ya yi kalaman kaskanci ga nahiyar
Afrika. Trump ya ce babu wannan maganar.
Trump yayin ganawa da Buhari

3. Trump ya bayyana cewar kwanannan Najeriya zata samu
jiragen yaki na musamman da ta saya daga kasar Amurka da
zarar an gama da duk wani batu dake da alaka da takunkumi
daina sayar wa da Najeriya makamai da gwamnatin Obama ta
kakabawa Najeriya, wanda kuma Trump ya janye shi.

4. " Ba zamu yarda da kisan Kiristoci ba a Najeriya," a cewar
Trump. Trump ya ce kasar Amurka zata shiga maganar kashe
mabiya addinin Kirista a Najeriya.

5. Shugaba Trump ya bayyana cewar yana ganin girma da
kimar shugaba Buhari kuma zasu yi aiki tare domin inganta
tsaro, kasuwanci, tattalin arziki da kuma kawo karshen kashe
Kiristoci a Najeriya.

Karin haske akan labarin BBC HAUSA

Shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa takwaransa na
Najeriya Muhammadu Buhari kan yadda yake yaki da
ta'addanci a lokacin da suka gana a fadar White House.

Mr Trump ya ce Shugaba Buhari "ya jajirce" a yakin da kasarsa
ke yi da ta'addanci kuma Amurka za ta ci gaba da aiki tare da
Najeriya domin kawar da wannan matsala.
Sai dai ya ce "ana kashe Kiristoci a Najeriyar, inda ya ce za mu
yi aiki kan hakan, domin shawo kan matsalar sosai da sosai,
domin ba za mu bar hakan ya ci gaba da faruwa ba."

Shugabbannin sun kuma tattauna kan batutuwan tattalin arziki
da kasuwanci da suka shafi kasashen biyu.
A nasa bangaren Shugaba Buhari ya yabawa rawar da Mr
Trump ke takawa wurin samar da zaman lafiya a yankin Koriya,
da kuma taimakawa Najeriya a yakin da ta ke yi da Boko
Haram

Sannan ya jinjina wa shugaban na Amurka kan yadda kasarsa
ke tallafawa ayyukan jin kai a yankin Arewa maso Gabas.
Muhammadu Buhari ya zamo shugaba na farko daga nahiyar
Afirka (Kudu da sahara) da ya gana da Mista Trump a
Washington.

Kasuwanci
Kan batun kasuwanci, Mr Trump ya nemi Najeriya da ta bude
kofofinta ga kamfanonin Amurka idan har tana son ayi
kasuwanci da gaske musamman a fannin noma.
Sai dai wannan lamari ne mai sarkakiya ganin yadda Najeriya
ke kokarin bunkasa noma a cikin gida da kuma rage dogara ga
man fetur.

Amurka da Najeriya na da alaka ta kut-da-kut wacce suka
shafe shekara da shekaru suna martaba wa.

Cin hanci da rashawa
Mr Trump ya kuma yabi yadda Buhari ke yaki da ta'addanci,
amma ya ce akwai cin hanci da yawa a kasar.
A don haka bai bayyana kai tsaye cewa ko Amurka za ta mayar
da kudaden da ake zargin an sace daga Najeriya an boye a
kasar ba.

Amma dai ya ce za su ci gaba da aiki tare da jami'an Najeriyar.
An zabi Shugaba Buhari ne bisa alkawarin yaki da cin hanci da
rashawa a kasar da ta yi kaurin suna a wannan fage.

Source by ©Hausa Naij and Bbc Hausa


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user