Sunday, 6 May 2018

Karanta Kaji: Shin ko Kasan Sunayen ’Yan kwallo 10 da suka fi samun kudi a Duniya???

Tura Wannan Zuwa Ga


Jim kadan bayan an fara kakar wasa ta bana a sassan duniya a
makon jiya ne sai Mujallar Forbes da ke bin diddigin yadda ’yan
kwallo ke samun kudin shiga a sassan duniya ta kawo rahoton
’yan kwallo 10 da suka fi samun kudi.

Kafar sadarwar Naij.com ce ta lalubo bayanin yayin da Aminiya
ta ci karo da shi a yanar sadarwar Intanent inda kuma ta fassara
wa masoya shafin labarin wasanninta kamar haka:

10. Luis Suarez (FC Barcelona). Mujallar Fobes ta kalato cewa
dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen shi ne na 10 daga jerin
wadanda suka fi daukar albashi da kuma samun kudi a harkar
kwallo a duk fadin duniya. Mujallar ta ce tsohon dan kwallon
Ajad da ke Holland da kuma Liberpool da ke Ingila yana dibar
albashin da suka kai Dala miliyan 16.5 kwatankwacin Naira
biliyan 3 da miliyan 630 a shekara. Baya ga haka dan kwallon
yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 4 da dubu 500 a
shekara a wajen yi wa wasu kamfanoni tallace-tallace a
lokacin da yake kulob din Liberpool na Ingila.
Sai dai duk da dambarwar da ta sarke dan kwallon a gasar cin
kofin duniya da aka yi a Brazil bayan an same shi da laifin yin
cizo, al’amarin da ya sa wadansu kamfanoni suka daina yin
hulda da shi, amma duk da haka dan kwallo ne na goma a
jerin wadanda suka fi samun kudi a harkar kwallo.

9. Sergio Aguero (Manchester City): Serrgio Aguero, haifaffen
Ajantina da yanzu haka yake buga wa kulob din Manchester
City da ke Ingila kwallo shi ne na 9 a jerin ’yan kwallon da suka
fi daukar kudi. An kiyasta dan kwallon yana daukar albashin da
suka kai Dala miliyan 17.9 kwatankwacin Naira Biliyan 3 da
miliyan 980 a shekara. Sannan yana yi wa kamfanoni tallan da
ta kai Dala miliyan 7 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan
540 a shekara.

8. Radamel Falcao (Chelsea FC): Duk da cewa dan kwallon bai
tabuka abin kirki a kulob din Manchester United da ke Ingila a
bara ba, kimarsa a wajen samun kudin shiga ba ta yi kasa ba.
dan kwallon da tuni ya koma kulob din Chelsea na Ingila a
kakar wasa ta bana an kiyasta yana samun Dala miliyan 25.9 a
shekara. Dala miliyan 21.9 daga cikin kudin a matsayin albashi
yayin da Dala miliyan hudu kuma a matsayin kudin tallace-
tallace ga kamfanoni da dama.

7. Wayne Ronney (Manchester United). Wayne Ronney dai dan
kwallon Manchester United da ke Ingila ne. A jerin ’yan kwallon
da suka fi samun kudi a duniya shi ne na 7. An ruwaito dan
kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 26.9 a
shekara. Daga adadin kudin Dala miliyan 19 da miliyan 9 a
matsayin albashinsa, yayin da yake samun Dala miliyan 7 a
matsayin kudin yin talla. Kafofin watsa labarai sun yi ta rade-
radin dan kwallon zai koma kulob din PSG a kakar wasa ta
bana, amma da alama dan kwallon ba zai canza sheka ba.

6. James Rodriguez (Real Madrid CF): James dan kwallon
kulob din Real Madrid da ke Sifen wanda ya koma kulob din
daga na Monaco na Faransa a bara, yanzu haka shi yake sanya
rigar kwallo mai lamba 10 a kulob din na Madrid. An ruwaito
sai da Madrid ta ajiye wa Monaco zunzurutun Dala miliyan 108
kafin ta saye shi daga Monaco. Mujallar Forbes ta ruwaito
yanzu haka dan kwallon yana daukar albashin da suka kai Dala
miliyan 29 a shekara. Dala miliyan 24.5 sun zama albashinsa
yayin da Dala miliyan 4 da miliyan 500 suka kasance kudaden
tallar da yake yi wa wadansu kamfanoni a sassan duniya.

5. Neymar Jr. (FC Barcelona): Neymar dai haifaffen Brazil ne.
Yanzu haka shekarun dan kwallon 23, kuma ana hasashen dan
kwallon zai iya zama Gwarzon dan kwallon duniya nan da
wadansu shekaru masu zuwa. Mujallar ta ce an kiyasta yana
dibar albashin da ya kai Dala miliyan 31 kwatankwacin Naira
biliyan 6 da miliyan 820 a shekara. Sai dai daga cikin wannan
adadi an kiyasta yana samu Dala miliyan 17 ne daga wajen yi
wa kamfanoni tallace-tallace. Da alama dan kwallon zai fi
kowane dan kwallo haskakawa a nan gaba idan ya cigaba da
nuna kwazo kamar yadda masana harkar kwallo suka nuna.

4. Gareth Bale (Real Madrid CF): Gareth Bale shi ne dan
kwallon da ya fi kowane tsada a tarihin cinikin ’yan kwallo a
duniya. Sai da kulob din Real Madrid ya ajiye Fam miliyan 85
kwatankwacin Naira Biliyan 31 da miliyan 875 kafin ta saye shi
daga kulob din Tottenham da ke Ingila shekaru biyu da suka
wuce. An kiyasta dan kwallon yana daukar albashin da ya kai
Dala miliyan 35 kwatankwacin Naira biliyan 7 da miliyan 700 a
yanzu. Sai dai daga kudin an ruwaito yana samun Dala miliyan
9 da dubu 500 ne daga bangaren tallace-tallace. Kenan tsuran
albashinsa ya kasance Dala miliyan 25 da dubu 500.

3. Zlatan Ibrahimobic (PSG): Haifaffen Sweden, Zlatan
Ibrahimobic dai shi ne na 3 a jerin ’yan kwallon da suka fi
samun kudi a bangaren kwallo. Yanzu haka yana kwallo ne a
kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kuma an
kiyasta yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 33.1 a
shekara. Daga ciki kuma yana samun akalla Dala miliyan 6 ne
a bangaren tallace-tallace.

2. Lionel Messi: (FC Barcelona): Lionel Messi, dan kwallon da
ake ganin babu kamarsa a duniya shi ne na biyu a halin yanzu
a jerin ’yan kwallo 10 da suka fi daukar albashi. Mujallar ta ce
dan kwallon yana samun kudin da suka kai Dala miliyan 73 a
shekara kwatankwacin Naira Biliyan 160 da miliyan 60 a
shekara. Sai dai Dala miliyan 51.8 daga cikin kudin yana samun
su ne daga bangaren tallace-tallace ga kamfanoni daban-
daban a duniya.

1. Cristiano Ronaldo: (Real Madrid CF): dan kwallon Madrid
kuma haifaffen Sifen, Ronaldo shi ne Mujallar Forbes ta
ruwaito a matsayin dan kwallon da ya fi kowane dan kwallo
samun kudi a fadin duniya. An ce dan kwallon yana dibar kudin
da suka kai Dala miliyan 79.6 a shekara kwatankwacin Naira
biliyan 175 da miliyan 120. Sai dai dan kwallon yana samun
kudin da suka kai Dala miliyan 52.6 ne daga bangaren yin
tallace-tallace daga cikin adadin kudin da yake samu. Masu
wasan damben boksin Floyd Mayweather da Manny Packuaiao
ne kadai aka ruwaito suka fi Ronaldo daukar albashi a duk
fadin duniya. Yanzu haka dan kwallno ne yake rike da kambun
Gwarzon dan kwallon duniya da ya lashe sau biyu a jere,
amma Lionel Messi ne ya kafa tarihin dan kwallon da ya taba
lashe kyautar sau hudu a jere. Sannan a ranar Laraba
ne Hukumar FIFA ta fitar da jerin ’yan kwallo uku da za su
fafata a gasar Gwarzon dan kwallon duniya ta bana ciki har da
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Aminiya
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user