Mutane da yawa, musamman masu amfani da manyan wayoyi na zamani,kamar wayoyin Android sukan koka akan yanda datarsu ke saurin karewa da zarar sun yi
subscription. Wannan dalili ne ke sanya wasu ma kan bar yawan bude datar ko kuma ma su rabu da
wayar baki daya.
Wannan abu ba hakanan kawai yake faruwa ba, akwai dalilai da kan sanya hakan.
A cikin wannan darasin namu, zamu yi tsokaci akan wadannan dalilan da kuma yanda zaku shawo kan wannan matsala ta yawan shan data. Sanin kowa ne a wannan lokaci da muke ciki, kusan dukkanin wayoyin da muke amfani da su, musamman ma manya wayoyi, mafi yanwancin aiyukansu sun dogara ne akan internet. Wannan dalili ne ya sanya cewa, idan har mutum baya da data a cikin layinsa, to sai ka ga ya kasa yin wasu da yawa daga cikin muhimman ayyukan da wadannan wayoyin kan yi. Saboda amfanin da wadannan wayoyin ke yi da
data ne ya sanya aka basu damar cewa, da zarar mutum ya kunna data, to su ci gaba da yin wasu
muhimman aiyuka ba tare da sun sanar da mai wayar ba (wato background data).
Wasu wayoyin kuma application din su ne ke yin update lokaci zuwa lokaci domin inganta ko kuma sabinta
yanayin yanda wayar ke aiki. Wani lokacin kuma, applications din da mutum ke yin installing a cikin
wayar ne ke amfani da wannan damar domin yin wasu ayyukan da ke bukatar data ba tare da sun nemi izinin mai wayar ba.
Shin ko kana cikin wadanda ke fama da irin wannan matsala ta shan data?
To kwantar da hankalinka, ga hanyoyin da zaka bi domin ragewa
ko kuma tsaida wannan shan data da wayarka take yi. Background Data App background data shine babban abin da ke sanyawa waya ta rika shan data babu gaira babu
dalili! Duk da cewa wayoyi da yawa na zuwa da wannan tsarin, wayoyin android sun fi kaurin suna
akan wannan matsala. To sai dai, duk da haka, wayoyin android din suna bada dama ga mutum
domin ya zabi applications din da yake bukatar ya rika amfani da data a ko da wane lokaci, tare da
kuma tsayar da wasu application din daga yin amfani
da data ba tare da saninshi ba.
Domin gane ko wane application ne yake shan
data ba tare da saninka ba, to sai ka shiga cikin
Settings na wayarka, ka duba daga kasa kadan, zaka ga inda aka sanya Data Usage . Idan ka shiga wurin zaka ga list na duk application da ke amfani da datarka, idan kaga akwai wani wanda baka
yarda da shiba to zaka iya hanashi yin amfani da data har sai ya samu izininka.
Domin tsaida
application daga shan data kai tsaye, sai a bi wadanna matakan:
1. Shiga cikin settings
2.Duba daga kasa kadan, akwai inda aka sanya
Data Usage
3.Idan ka shiga Data usage , zaka ga list na applications din da ke shan data da kuma yawan
datar da suka sha
4 . Domin tsaida application daga shan data, sai ka taba application din, nan take wani page zaya bude.
5 . Sai ka duba daga kasa, akwai inda aka sanya Restrict app background data , sai ka taba ko kuma ka kunna.
Haka zaka yi ma duk wani application da kake
bukatar takaita yanayin shan datar da yake awayarka. Daukar wadannan matakan kadai, zaya
taimaKa maKa wajen rage yanayin yanda wayarka ke sha maka data sosai. Wannan sune hanyoyi da zaka bi domin rage yawan data da wayarka ke amfani da ita ba tare
da saninka ba.
Allah ya kiyaye
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin
Source by ©Hausa Class