Fitacciyar jarumar fina finan Hausa ta Kannywood, Rahama Sadau, wadda aka dakatar daga shiga harkar Fim, ta bayyana a ranar Asabar cewar, ta fara shiga matsaloli ne tun bayan da ta fara yin shirin fim din ‘yan kudancin Najeriya da aka fi sani da Nollywood da kuma na turawa wato Hollywood.
Rahama ta bayyana irin yadda take shan bakar wahala daga aftawan Kannywood, tace abu ne marar dadi matuka idan mutun yace zai tsallaka zuwa shirin finafinai na kudanci ko na turawa musamman yadda al’adu da dabi’u suka sha bamban.
Ta bayyana cewar, kowadanne masu shirya finfinai musamman wadan da ake ganin sun saba da dabi’unmu, suna da nasu yanayin gudanarwar harkar fim da ta sha bamban da ta Kannywood. Rahama Sadau ta yi kira ga ‘yan uwanta masu harkar fim da masu shirin shiga harkar da su sanya damara wajen mai da hankali akan abinda suka sanya a gaba ba tare da wani tsoro ko shakka ba.
“Ina mai baiwa jarumai shawara, da su nutsu su mayar da hankali sosai akan duk abinda suka sanya a gaba, tare da yadda da abinda suke yi, da kuma yadda da zabin da suka yiwa kan, in sun yi haka zasu ci nasara” “Kasan me kake yi a harkar fim, ka yi aiki tukuru dominsa, tare da jajircewa da kuma tsayawa tsai dmin samun nasara da kuma daukaka, in mutum ya maida hankali sosai akan abinda yakeyi to zai ci nasara”
Da aka tambayeta kan rawar da ta taka akan wani shir mai suna “Zeero Hour” Wanda yanzu haka ake aikin daukar shirin a birnin tarayya Abuja, Rahama ‘yar shekaru 24 tace ta fito a shirin fim din a matsayin Zainab ne.
“A cikin shirin na fito a matsayin Zainab ne wadda take tsakanin daukar fansar kawunta da aka kashe da kuma batun abokin samartakarta wanda shima yake cikin rudani game da ita a cikin shirin”
Da aka tambayeta kan batun lambar yabo da ta samu daga jaridar Leadership a matsayin jaruma mafi barkwancita shekara, tace ta cika da mamakin jin cewar ita ce ta lashe wannan lambar yabo.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin
Source by ©Press Hausa