Friday, 8 June 2018

Shin me kasani dangane da Takaitaccen Tarihin Addinin Kirista? Shin me ne ne Alakar Addinin Kirista da Addinin Musulinci??

Tura Wannan Zuwa Ga

A duk Ranar 25 ga watan disamba na kowacce shekara, mabiya addinin Yesu Kiristi suke bikin tunawa da ranar Haihuwar Annabi Isa A.S Haka kuma, Mabiya addinan Islama dana kiristanci, dukkansu sun amince da wanzuwar Yesu Almasihu kuma suna darajanta shi.


Shin me kasani dangane da Takaitaccen Tarihin Addinin Kirista??

MarubuciSadik Tukur Gwarzo, RN.

Sai dai, yadda mabiyan kowanne daga addinan suka ɗauke shi keda bambamci.

A addinin musulunci, an nuna cewa Yesu Kiristi Mutum ne mai daraja, wanda Ubangiji abin bautawa ya aiko domin yayi wa'azi da kaɗaitashi.

Haka kuma mahaifiyarsa, an yabeta a matsayin mace mai gaskiya. A duba Alkur'ani (3:45) da (19:17)
Sai dai a kiristance, ba haka abin yake ba.

Domin kuwa da yawan mabiya addinin suna ɗaukar Yesu Almasihu a matsayin Ubangiji, yayin da wasu ke ɗaukarsa a matsayin ɗa-ga Ubangiji.

Don haka, wannan saɓani, zai warwaru ne kurum idan mukayi duba izuwa littattafai masu tsarki na waɗannan addinai guda biyu.

Da fari dai, acikin Suratu Maryam cikin littafin Alqur'ani mai girma, maganar Ubangiji ta faɗi labarin yadda aka haifi Yesu kiristi ba tare da Uba ba, har mutane ke tuhumar mahaifiyarsa da cewa "yake 'yar uwar Haruna, hakika kinzo mana da bakon abu, gashi kuwa mahaifinki ba fasik'i bane, mahaifiyarki kuma ba mai bin mazaje bace".

Sai kuwa Maryamu tayi musu nuni da Jaririn tana nufin su nemi ba'asi daga gareshi. Har suke cewa gareta "tayaya zamuyi magana da wanda ke cikin zanin goyo?"

Ai kuwa Sai Yesu Almasihu dake zanin goyo ya amsa da cewar "Ni bawan Ubangiji (Mai suna Allah) ne, ya bani littafi ya kuma sanyani Annabi".

"Ya sanya albarka a gareni a duk inda na kasance, yayi mini wasicci da Sallah da Zakkah matukar ina raye".

"Kuma aminci ya tabbata a gareni a ranar haihuwata, da ranar mutuwata, da ranar da za'a tashe ni rayayye".

Sai Ubangiji yace "wannan fa shine Isa Dan Maryamu.."(karanta har karshen Aya)
Maryamu: 26-34

A littafin Babil mai tsarki, nan ma ana iya cewa yazo a wurare daban-daban cewar Yesu Almasihu bashine Ubangiji ba.

Sahabban Yesu kiristi irinsu Matthew, Mark, da Luke waɗanda suka rubuto zantukansa har suka haɗa zantukan izuwa littafin Babil, sun tafi akan cewa Yesu kiristi bai taɓa kiran kansa da suna Ubangiji ba. A duba Matthew 10:18, da Matthew 19:17.
Abinda wasunsu suka yadda shine: shi ɗan Ubangiji ne, saboda haihuwarsa da akayi babu uba da kuma karamomin daya nuna a zamanin rayuwarsa.

Haka kuma, ɗaukarsa a matsayin ɗan Ubangiji na nufin kasancewarsa Mutumin kirki nagartacce, don haka ba shi kaɗai ba, duk wani nagartaccen bawa sukan kirashi ɗan Ubangiji. A duba Matthew 23:1-9 don a tabbatar.

Shikuwa Paul, wanda shima Maruwaicin Babil ne, ya aminta da cewar Yesu Kiristi ba Ubangiji bane.

A cewar sa, yesu kiristi ne wanda Ubangiji ya soma halitta, don haka yayi amfani dashi wajen halittar sauran halittu kamar yadda yazo a Colossians 1:15 da 1 corinthians 8:6.
Saboda haka, kasancewar Paul, John da sauran manyan maruwaitan littafin Babil mai tsarki, sun tafi akan cewar Yesu Almasihu shine halittar Ubangiji na farko kuma mafi daraja, har ma Paul ɗin ya ruwaito a Babil cewa yaji Yesu na faɗin "The Father is greater than I". Watau "Uban, ya fificeni" sai waɗanda suka biyo bayansu sukayi shishshigin ɗora masa lak'abin shi ɗan ubangiji ne, wasu kuma sukace shi Ubangiji ne kachokan.

Ga kaɗan daga ayoyin Babil da suke nuna Yesu Kiristi ba Ubangiji bane, bawan Ubangiji ne kamar yadda muka kawo Yesu ɗin ya faɗa da bakinsa daga Alkur'ani:-

"Men Of Israel, listen to this:Jesus of Nazareth was a Man accredited by God to you by miracles.." Acts 2:22

"God Has raised this Jesus"

Acts 2:32

"God Raised up his Servant"

Acts 3:26

"The Lord of Abraham, Isaac, and Jacob, the Lord of our fathers, has your holy servant Jesus"

Acts 3:13

A wani kaulin ma, shi da kansa Yesu Almasihu ya faɗi cewa bai san ranar da za'a tashi alkiyama ba, don haka shifa bawan Ubangiji ne (Matthew 24:36).

A Wani wajen kuma an ruwaito Yesu Kiristi yana neman taimakon 'Eloi', ko 'Eloh' wajen tabbatuwar ayyukansa, kamar yadda akace ya faɗa yayin da Yahudawa zasu halaka shi cewa "ELOI, ELOI, LAMA SABACHTANI (Markus 15:34. )

Ma'ana, "Ubangijina, Ubangijina, don me ka yasassheni?"

Don haka, idan har Yesu ya kasance ubangiji, me zaisa ya rinka neman taimakon wani kuma, sannan me zaisa me ya rinka faɗawa mutane da kansa cewar shi Ɓbawa ne ga ubangijinsa ELOHIM?

Koda yake, wannan k'in gaskiyar karamin aiki ne ga manyan malamaii mabiyansa idan muka kalli Babil, Song of Songs (5:16), inda kai tsaye akayi busharar zuwan wani Annabi mai suna ' מַחֲמַדִּים' cikin harshen yahudawa (wanda aka fassara haruffan da m-ħ-m-d-y-m, ake kuma furtasu da meħmadim ko
maħammaddīm don girmamwa bisa karin 'im'), amma kai tsaye sai sukace sam kalmar ba Annabi Muhammad take nufi ba, wai tana nufin wani wanda kowa keso ne ko kuma wani mafi cancanta..

MENENE SUNAN SA?

Akwai wasu Mutane 'yan ɗarikar Jehovah daga cikin ɗarikun kiristoci masu zagayawa gida-gida ga 'yan uwansu kiristoci suna tambaya menene sunan sa? (Suna nufin menene sunan Ubangiji)
Sai kaji kirista yace "Ubangiji"
Sai suce "Ubangiji ai ba suna bane, abin bauta ne".

Sai su kara tambaya, "to menene sunan sa?"
Sai kaji kirista yace "Sunan sa Uba (Baba God)"
Sai suce masa "shin Ubanka Ubangiji ne?"
Nan take kirista zaice "A'a".

Sai su sake tambayarsa, "to menene sunan sa?"
Idan yayi shiru babu amsa, sai suce "Jehovah shine sunan sa".

Waɗannan kalmomi guda huɗu da ake kira Tetragammation, sun hana kowa yabisu dalla-dalla don zakulo asalin ma'anarsu.
Amma idan ka tambayesu, menene 'Je-ho-va-h', sai suce maka 'Y-H-W-H', watau kalmomi huɗu da suka zo a littafin Babil mai tsarki na yaren Ibraniyanci.

Kasancewar tsohon rubutun Ibraniyanci da Larabci babu wasulla, waɗancan kalmomi na YHWH (ko JHWH saboda matsalar J da ake sauyata da Y a larabci, kamar misalin Jacob da Yakub, Jesus da Yesus, Joseph da Yusuf, W kuwa har yau a wasu yarukan da lafazin V suke ambatonta) kaɗai sunzo da maimaicin akalla sau 6,823 acikin Babil.

Saboda haka, mabiya ɗarikar jehovah sun gamsu cewar Kalmar JHVH (YHWH) sunan Ubangiji ne daya kira kansa da kansa a littafi mai tsarki sama da sau dubu shidda, to amma kalmar ELOHIM (YHWH ELOHIM) ce ke tare da waɗancan haruffa a mafi yawan lokuta.

Idan muka kalli kalmar 'ELOHIM', zamuga kalmomi ne biyu a haɗe, watau ELOH da kuma IM.

Da Fari, ita IM, ɗango ne na girmamawa ga ELOH a yaren Annabi Ibrahim A.S. misali, idan za'ace Ibrahim yana da girma, sai a kara masa IM, ya zamo 'Ibrahimim', kamar yadda idan aka lura har yanzu yaren yahudanci da wasu yaruka na bin wannan tsari.

Saboda haka 'ELOH' shine sunan, wanda shima zamu gane ainihinsa idan muka kalli yadda Larabci ke kiran duk abinda Ibraniyanci ya kira da 'EL' da lafazin 'AL'.
Don haka, kalmar 'Eloh' ta yaren Ibraniyanci na nufin 'Aloh' kenan a larabci.
Kalmar da idan mukaci gaba da mai-mai-ta-ta a zukatanmu zamuga ta sauya daga Eloh, Eloh, Zuwa Aloh Aloh.. Zuwa Allah Allah..

Wannan ke nuni da cewa kalmomin 'YHWH ELOHIM' da suka zo a Babil na Ibraniyanci ba komai suke nufi ba sai 'YA HUWA ALLAH' a larabci, kusan Aya kenan ta farko a Suratul Ahad, da Ubangiji yace "Qul Huwallah..." (watau kace shine Allah)
To waɗannan kalmomin fa, sune sukazo a Babil sama da sau dubu shidda.. Abinda Allah ke faɗawa Manzonsa Annabi Isah A.S shine "ka sanar musu da cewa Ubangijinka Shine Allah.." Kuma abinda Yesu Kiristi yayi ta sanarwar kenan, amma har zuwa yanzu Ubangiji baisa 'yan uwanmu kiristoci sun gane cewar Allah ne sunan ubangiji abin bauta da gaskiya ba.

Marigayi Sheik Ahmad Deedat Rahimahullah yana Cewa dangane da wannan batu "Idan da Malaman kiristoci zasu sanar da Mabiyansu wannan abu, tabbas da lokaci yayi wanda musulmai da kiristoci zasu haɗu wajen bautawa Ubangiji makaɗaici".

Daɗi akan haka, shine kalmar nan ta ELLELUYA, wadda babu kiristan dabai santa ba.

Har ma sukan ambace ta aduk sanda suka so godewa Ubangiji, kamar yadda Musulmai ke faɗin Allahu Akbar don tsarkake Ubangiji.

Ya kuwa ishemu misali idan muka kalli kalmar Ibraniyanci ta ELLELU-YA muka musanya ta da zubin larabci izuwa ALLELU-YA.. (muka sauya EL da AL)

Sai mu kalli waɗannan kalmomi:-

ALLELU YA
YA ALLELU
ALLAHU YA
YA ALLAHU

Ku tambayi kanku, don girman Allah akwai banbanci ko babu?

Sheikh Deedat, Zakir Naikh da sauran malumman musulunci duk sun tabbtar da cewa Ya Allahu shine asalin Kalmar Elleluya.

Don haka, aduk sanda kaji malaman kiristoci na faɗin "Praise the Lord!" sukuma suna amsawa da "ElleluYa!!!" kasani cewa "Ya Allahu" kurum suke ambata a sauye.
Allah da aka ambata a Linjila, shine aka sake ambata a Alqur'ani mai tsarki, amma k'alilan daga mutane ke fuskantar haka.

Hakika, Tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai tsarki da Buwaya. Allah kayi daɗin tsiranka ga Shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran Annabawan Allah masu tsarki. Amin.

Karanta Yanzu Kaji: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Marigayi Ali Banat - Waye Wannan Ali Banat din da ake Magana Akai???

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user