Najeriya da Argentina za su fafata a wasansu na karshe na rukunin D na gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018.
Wasan shi ne zai tantance makomar kasashen biyu a gasar, kuma hankalin masu kaunar kwallon kafa a duniya ya karkata a kansu.
Sai Argentina ta doke Najeriya, san nan Croatia ta ci Iceland ko kuma sun tashi canjaras, san nan Argentina za ta samu zuwa zagaye na gaba.
Najeriya kuma na bukatar ta doke Argentina ko kuma ta tashi canjaras da ita, sannan ta yi fatan kada Iceland ta yi nasara a kan Croatia domin zuwa zagaye na gaba.
Ga abubuwan da nake ganin ya kamata 'yan Super Eagles su yi domin samun nasara:
1. Kai hare-hare
Najeriya na bukatar fara wasan da kai hare-hare saboda 'yan magana kan ce mafi kyawun tsaro shi ne kai hari.
Idan suka zauna a gida ba sa kai hari, 'yan Argentina za su samu damar kame tsakiyar fili kuma wannan zai ba su damar rike kwallo fiye da Najeriya, duk da cewa ana hasashen dama za su rike fiye da su din.
Idan hakan ta faru, to Argentina za ta samu damar kai hare-hare da wahalar da Najeriya sosai.
Amma idan Super Eagles ta sa kaimi, ta fito aka fafata, amma tare da yin taka-tsan-tsan, to za ta iya cin kwallo ta hannun 'yan wasanta irinsu Ahmed Musa da Victor Moses da sauransu.
2. Rashin sake
Croatia ta yi amfani da dabaru ciki har da killace madugun Argentina, Lionel Messi, a wasan da ta doke su da ci 3-0.
Najeriya na bukatar irin wannan dabarar saboda tawagar Argentina an gina ta ne a kan Messi.
Sai dai kocin Argentina, Jorge Sampaoli, zai iya sauya salon wasa, a don haka dole ne Super Eagles su kula da dukkan 'yan wasan Argentina musamman na gaba da kuma tsakiya (masu shirya kwallo).
Yin hakan zai taimaka musu wurin dakile kaifin Messi ko da kuwa ba su iya rufe shi kwata-kwata ba, wanda dama abu ne mai matukar wahala.
3. Da'a
Ya kamata 'yan wasan Najeriya su mayar da hankali wurin bin dokokin wasa musamman wadanda suka jibinci keta.
Argentina na da 'yan wasa da suka iya yanka kamar su Lionel Messi da sauransu.
Yi wa irin wadannan 'yan wasan keta ka iya janyo wa Najeriya fenareti ko kuma jan kati, abin da zai iya jawo tawagar koma baya.
A don haka 'yan wasan baya irinsu Leon Balogun da Ndidi na bukatar su yi taka-tsan-tsan kan yadda za su tunkuri wasan, ganin cewa sun jawo wa kansu fanareti a duka wasa biyun da suka yi a baya.
4. Mayar da hankali har zuwa karshen wasa
A gasar cin kofin duniya ta bana wasu kasashen da suka yi kokari tun daga farkon wasa sun sha kaye domin sakacin da suka yi a karshe.
Daya daga cikin irin wadannan kasashen ita ce Sweden wadda ta rike Jamus ana kunnen doki har zuwa minti na 95, inda Jamus ta samu ta zura mata kwallo daya a raga abin da ya sa ta sha kaye a wasan.
Irin wannan ci a kurarren lokaci ka iya saka Najeriya a wani mawuyacin hali, kamar yadda Italiya ta fitar da kasar a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a shekarar 1994.
A don haka wajibi su nutsu, kada su karar da kuzarinsu a farko-farkon wasa, kuma kada su bari Argentina ta gajiyar da su.
5. Cin kwallo
Babu yadda za a yi nasara a wasa ba tare da zura kwallo a raga ba. Ya kamata 'yan wasan gaban Najeriya Ahmed Musa da Kelechi Iheanacho da Kuma Victor Moses su nemi ci ido rufe.
Babu shakka idan suka matsa kaimi, za su iya samun damar zura kwallo domin 'yan bayan Argentina suna da rauni kamar yadda wasanninsu na baya suka nuna.
Idan Super Eagles ta yi nasara, wannan zai sa ta samu zuwa zagaye na biyu a gasar.
Hakazalika, zai sa Najeriya ta rama kadan daga cikin shan kayen da ta sha a hannun Argentina a baya.
Sau hudu Najeriya na shan kaye a hannun Argentina a gasar kofin duniya- ko a wannan karon Super Eagles za su taka mata burki?
Ku Kasance Da Mu a Koda Yaushe domin Jin abinda ke wakana a wasan Nigeria da Argentina .
Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode
Source: BBC HAUSA
Tuesday, 26 June 2018
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
MAKALOLI MASU ALAKA
Karanta Dalilin da yasa aka yankewa Cristiano Ronaldo Hukuncin Ɗaurin Shekara 2 Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7, bayan d
Kalli sabbin Hotuna 3 na MC Tagwaye sanye da rigar 'yan kwallon Najeriya Fitaccen Tauraron me wasan barkwanci ta hanyar
NAFI KOWA FARIN CIKIN KORAR SUPER EAGLE A WASAN AFCON 2019 - DATTI ASSALAFYNaji dadi da aka koro kungiyar kwallon kafa ta ka
Karanta Kaji Dalili: Ronaldo zai fara shirya fina-finaiShahararren dan wasan kwallon kafa,Cristiano Rona
Karanta Yanzu Kaji: Shin ko kasan dalilin da yasa 'yan Najeriya suka yi caa kan Cüneyt ??? Sau hudu Najeriya na shan kaye a hannun Argentin
Wasanni: Da mun yi rashin nasara akan Chelsea zan kashe kaina - WengerMai horar da kungiyar Arsenal, Arsene Wenger, ya
Karanta Cikakken Tarihin Mesut Ozil: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Wasan Kwallon Kafa Mesut Ozil - Hotuna da Cikakken Tarihi Ko Dan Ni Musulmi Ne Ake Kalubalanta Ta A Kungiy
Karanta Dalilai 13 Da Suka Sa Na Musulunta- Inji Emmanuel Adebayo Dan Kwallon Kafa Ya Ce Yana Da Dalilai Kan Yadda Musulmai Suka
KARANTA WASU DAGA CIKIN RA'AYOYIN 'YAN NIGERIA AKAN SAKAMAKON WASAN NIGERIA DA ARGENTINA - HOTUNA DA CIKAKKEN LABARIN WASANSakamakon wasan Nigeria da Argentina Niger
Labarin Wasanni: Man United ta samu fam miliyan 141Manchester United ta sanar da samun kudin shiga d
Kaga wannan hoton kuwa: Kalli Hotan Da Ronaldo yawa Muhammad Salah kallon 'Zaka sani' Wannan wani hoto ne da aka dauka kamin fara w
Labarin Wasanni: Najeriya za ta kara da Argentina a gasar cin kofin duniyaAn kammala fitar da jadawalin kasashen da za su f
- Blog Comments
- Facebook Comments
