Thursday, 26 July 2018

Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (2)

Tura Wannan Zuwa Ga
Lokacin da Kasim ya dawo daga kasuwa tun bai huta ba, matarsa ta tare shi ta ce, "Maigida, na san da cewa ka dauki kanka a matsayin wanda ya fi kowa arziki a duk fadin garin nan, to amma abin da ba ka sani ba shi ne, yanzu akwai wanda ya dame ka ya shanye game da arziki cikin wannan gari namu. Domin yana da tarin zinariyar da ta fi karfin a kidaya ta da hannu sai dai a auna ta da mudu."


Kasim ya ce, "Wane ne wannan attajiri haka, amma dai bai dade da zuwa garin nan ba ko?"

Matar ta ce, "Ba kowa ba ne face dan uwanka Ali Baba." Ta kwashe dukkan labarin yadda matar Ali Baba ta zo aron mudu a wurinta, da kuma dabarar da ta yi har ta gano abin da aka auna da mudun.

Kasim ya kasance ba ya kula da taimakon dan uwansa Ali Baba duk da tarin dukiyarsa, ba ya ko yarda ya matso kusa gare shi, wai kada ya shafa masa talauci. Da ya ji wannan labari daga matarsa, sai ya cika da mamaki tare kuma da hassadar jin cewa wai har akwai wanda ya fi shi arziki a garinsu. Ya ce a cikin ransa, "Yanzu dare ya yi, amma gobe tunda safe zan je gidan dan uwana na ji inda ya sami wannan dukiya da rana tsaka. Lalle idan ya fara sata ne, zan tsegunta wa Sarki a daure shi." Ya kwanta amma ya kasa yin barci, yana ta kahon dandi har gari ya waye.

Da gari ya waye, tunda sassafe Kasim ya sallama wa Ali Baba. Bayan ya fito, ko gaisawa ba su yi ba, sai Kasim ya ce, "Ali Baba ka yi wa mutane badda sau, suna ganin ka a matsayin talaka wanda bai mallaki komai ba sai jakai guda uku da kake zuwa daji kana yiwo itacen siyarwa.

Amma abin mamaki, jiya bayan na dawo daga shagona, matata ta ba ni wannan kwayar zinariyar ta ce mini a cikin mudun da ta ara muku ta makale. Wannan ya tabbatar mata da cewa ba hatsi kuka auna da mudun ba. Wannan ne dalilin da ya sa yanzu na yo maka sammako domin na ji inda ka sami wannan dukiya, idan kuwa ka ki fada mini zan je na shaida wa Sarki cewa kana daya daga cikin barayin nan da suka addabi mutanen wannan gari da kewayensa da sata, yanzu haka ma zinariya na nan kime a gidanka da kuka sato. Kuma na tabbata idan aka bincike gidanka kaf, za a gan ta."

Da Ali Baba ya ji wannan zance na dan uwansa, sai ya tabbatar da cewa matarsa ta fallasa musu sirrinsu ba tare da ta sani ba, don haka babu wani boye-boye illa ya fada wa dan uwansa gaskiyar abin da ya faru.

Ali Baba ya kwashe labrin abinda ya faru duka ya fada wa Kasim. Ya yi masa kwatancen dajin nan da kuma dai dai wurin da dutsen da barayin nan suke tara dukiyarsu ya ke. Ya kuma fada masa abin da ake cewa dutsen ya bude da kuma abin da ake cewa ya rufe.

Kasim na gama jin wannan labari, bai zame ko'ina ba sai kasuwa. Ya siyo jakai guda goma, kowane da mangalarsa, ya kawo gida ya daure.

Tun da asuba ya daura wa jakuna mangaloli, ya nufi dajin nan da Ali Baba ya yi masa kwatance. Can zuwa rana tsaka ya isa, ya bi kwatancen da aka yi masa har ya gano wurin da dutsen ya ke. Ya daure dabbobinsa a kusa da dutsen.

Ya tsaya gindin dutse ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Rufe bakinsa ke da wuya, sai ya ga kofa ta bude daga jikin dutsen. Mamaki ya rufe shi, nan da nan ya kwanto mangaloli daga jakunansa ya kutsa kai cikin dutsen, yana shiga dutsen ya rufe.
Kasim ya ga ashe dutsen wani katon daki ne mai cin dakuna sama da uku. Ya ga tarin dukiyar da ko a tunani bai taba zaton akwai irinta ba a fadin duniya. Komai bangarensa dabam, zinariya da azurfa da tagulla da tsabar kudi, ga su nan bila haddin. Ba tare da bata lokaci ba, ya fara cika mangalolinsa da ita yana tunanin abubuwan da zai yi idan ya kwashe ta duka ya kai gida.

Da ya gama cika mangalolinsa, ya ga kamar ma bai debi komai ba, domin babu alamun dukiyar nan ta ragu. Ya kiyasta cewa koda zai kwashe dukiyan nan duka, to sai ya yi wata uku ko fiye yana zuwa kullum yana dibar ta. Ya zo inda kofar dutsen ta ke ya ce, "Fayau, bude dutsen Cimcim." dutse ya ki budewa. Ya kara cewa, "Fayau, bude dutsen Jimjim." Dutse bai ko motsa ba.

Kasim yayi ta kiran kalmomi kamar su, Timtim, Kimkim, Zimzim, amma Allah da ikonsa har ya gaji ya kasa tuna kalmar "Simsim." Kamar ma da dai, bai taba jin kalmar ba. Daga nan sai murna ta koma ciki, domin ya tabbata idan barayin nan suka dawo suka same shi a ciki, lalle kashinsa ya bushe.

Sai duk dukiyar da ke cikin dutsen ta fita daga ransa, ya fara safa da marwa yana kokarin tuna kalmar da ake fada dutsen ya bude. Yayi duk iyakar kokarinsa amma ya kasa tuna kalmar. Da ya gaji sai ya sami wuri ya zauna yana tunanin makomarsa idan barayin nan suka same shi a cikin ma'ajiyarsu.

Bai san tsawon lokacin da ya kwashe a cikin dutsen ba. Can sai ya ji karar kofatan dawaki suna nufo wurin da dutsen ya ke. Tun yana jiyo su daga nesa, har suka zo daf da gindin dutsen. Daga nan sai ya ji duk sun sauka daga kan dawakansu. Ya duba cikin dutsen nan ko zai ga wani makami da zai kare kansa da shi, bai samu ba.

Ya duba ko akwai wani wuri da zai iya boyewa, ya ga babu. Ya yanke shawarar ya tsaya daf da bakin kofa, idan dutsen ya bude sai ya yi wuf ya yi waje da gudu ya kama dokinsu daya ya sukwane shi, idan Allah ya taimake shi zai iya tserewa. Don haka sai ya tsaya daf da wurin da kofar za ta bude cikin shiri.

Su kuwa barayin nan da suka zo gindin dutse sai suka ga jakai guda goma a daure, suka duba ko'ina ba su ga mai su ba. Sai jikinsu ya ba su, domin ba su taba sa ran wani dan Adam zai iya zuwa cikin wannan daji ba, kuma har gindin dutsensu.

DUBA WANNAN: Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (3)

Babbansu ya matsa gaban dutsen ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim." Nan take dutse ya bude.


Za mu ci gaba....Ranar  Litinin Insha Allah


Ku ci gaba da Kasancewa da Mu domin samun ci gaban wannan ƙayataccen Labarin...


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user