Monday, 2 July 2018

Karanta a Natse Kaji: Wasika Mai Zafi zuwa ga Dr rabi'u Kwankwaso-Daga Adnan Mukhtar

Tura Wannan Zuwa Ga
A wasikar farko da na rubuta maka a cikin watan Janairun shakarar nan a lokacin da kake shirye -shiryen zuwa jihar Kano wanda daga baya aka hana ka zuwa, kuma aka buga wasikar a gidajen jaridu da yawa a kasar nan na ba ka shawara a kan wasu abubuwa masu muhimmanci ba don saboda komai ba, saboda ina daya daga cikin magoya bayanka na gaske wanda kuma nake fadar gaskiya ga shugabana koda kuwa a ce gaskiyar ta saba da ra’ayinsa.



Ya mai girma Sanata, na yi rubutu da yawa a gwamnatinka yadda na nuna goyon baya sannan kuma ina goyon bayan aniyarka ta tsaya wa takarar shugaban kasa, har ila yau har yanzu kana da mutunci da kima a idona kuma na dauke ka a matsayin uba, shugaba sannan kuma wanda ya zamar da jihar kano wani babban birni.

Ba na tsoron fadin gaskiya kuma ina gayawa mutane gaskiya musamman masu mulki ba tare da la’akari da kujerar da suke rike da ita ba, wannan shi ne dalilin da ya sa na rubuta maka wasika ta a farko inda a ciki nake ba ka shawara da ka dakatar da shirinka na tsaya wa takarar shugabancin kasar nan a babban zabe mai zuwa zuwa shekara ta 2023 duk da cewa Allah ne yake ba da mulki ga wanda ya so sai dai damar ka ta lashe zabe a shekara ta 2019 ba ta da yawa duba da yanayin siyasar kasar a wannan lokaci.

Wasu daga cikin magoya bayanka da ke fadin tarayyar kasar nan sun yarda da irin shawarar da na ba ka a wasika ta ta farko duk da cewa wasikar ta tayar da hazo musamman a kafafen yada labarai na zamani kuma wasu da yawa sun fahimceni yayin da wasu kuma ba su fahimci inda na dosa ba a wasikar kuma suka kasa kawo dalilai kwarara da za su kare kansu da kin yarda da suka yi.

Wasu daga cikin wadanda ba su yarda da wasikar ba har cewa suka yi gwamnatin Kano ce ta dauki nauyin rubuta wannan wasikar tawa ta farko yayin da wasu kuma suke ganin ban isa in ba wa mutum kamar kwankwaso shawara ba.

Amma duk da haka ban damu ba a matsayina na marubuci, danjarida sannan kuma mai sharhi a kan al’amuran da suka shafi siyasa a kasar nan.

Ya mai girma Sanata, kai babban dan siyasa ne a kasar nan na fadi wannan a lokuta da dama kuma kana da dubban magoya baya a jihar kano kuma da a ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da lissafi a siyasa da ba zai taba yarda ka kufce masa ba domin za ka taimaka masa sosai a babban zabe mai zuwa na shekara ta 2019.

Jam’iyyar APC ba a hannunka take ba a yanzu, kuma ba ta hannun mutanenka a siyasa kuma burin kowanne dan siyasa shine ya kasance jam’iyya tana hannunsa domin ya yi duk abin da yake so a cikin jam’iyya amma a yanzu a jihar Kano jam’iyya tana hannun na hannun daman gwamnan Kano Ganduje.

Haka ma a mazabarka ta Kwankwaso da ke karamar hukumar Madobi inda babban abokin adawarka a siyasa, Musa Iliyasu Kwankwaso gwamnatin Kano ta ba wa kwamishina domin ya yake ka da magoya bayanka sannan kuma ya kwace jam’iyyar gaba daya daga hannunka.

Sannan kuma har ila yau duk wani wanda yake tare da kai kuma yake da wani mukami a jam’iyya gwamnan Kano ya kwace mukaminsa yabawa na jikinsa tun daga matakin kasa zuwa matakin yanki da jiha da karamar hukuma da kuma mazaba.

Lokacin da na yi shirin rubuta wannan wasika nasamu goyon baya daga wajen magoya bayanka na gaske dayawa musamman wadanda suke yawan rubuce rubuce akanka a shafukan sada zumunta sannan sun turomin sakonni kala-kala inda suke bayyana rashin jin dadinsu bisa halin rashin tabbas da suke ciki.

Za a yi zaben fid da gwani na jam’iyya a karshen watan Agusta zuwa watan Okotoba amma har yanzu ba ka fito ka bayyanawa dubban magoya bayanka halin da kake ciki ba da kuma irin shirinka na ganin ka samar musu da mafita a siyasa.

A babban taron jam’iyyar APC wanda ta gudanar a kwanan nan inda ta zabi sababbin shugabanni ba ka je ba kuma a matsyinka na jigo a jam’iyyar kuma tsohon gwamna tsohon minista sannan kuma Sanata mai ci a yanzu.

Na yi zaton da kai da ragowar ‘yan sabuwar PDP ba za ku halarci babban taron ba amma abin mamaki sai na ga har da shugabanku na sabuwar PDP, wato Abubakar Kawu Baraje ya samu zuwa taron jam’iyyar APC din sai shugaban majalisar Dattijai, data wakilai, da gwamnan Sokoto, Tambuwal da kuma da yawa daga cikinku.

Sannan ka kara tsorata magoya bayanka bayan da aka gano ka ka kaiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ziyara sannan kuma ka kaiwa gwamnan jihar Ekiti ziyara a jiharsa.

Ya mai girma Sanata, sakamakon haka yasa ka saka dubban magoya bayanka cikin zullumi kuma suna zaman rashin tabbas a matsayinsu na mabiyanka saboda kawo yanzu ba su san makomarsu ba a siyasar kasar nan.

Na yi wannan rubutu ne a madadin dubban magoya bayanka wadanda suka rokeni dana rubuta wannan wasika domin ka fito ga bayyana musu inda ka dosa saboda lokaci yana kurewa.

Allah ne yake bada mulki ga wanda yake so a lokacin da yake so kuma bana nufin cewa ba za ka zama shugaban kasa ba a nan gaba amma ina ganin damarka ta zama shugaban kasa a zabe mai zuwa ba ta da yawa.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya


FARIN CIKIN KU SHINE FARIN CIKIN MU

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user