Kofa na budewa, sai Kasim ya fito waje da gudu, ya bangaje wasu daga cikin barayin nan. Kafin ya sake daga kafarsa wani daga cikin barayin nan ya raba shi gida biyu da takobinsa, gaya-wa-jini-na-wuce.
Barayin nan suka shiga cikin dutsen, suka ga mangalolin da Kasim ya cika da dukiyarsu. Kuma suka lura da cewa lalle ko bayan wannan dukiyar da Kasim ya dauka, akwai alamun an taba dibar dukiyar, ke nan ko Kasim din ne ya taba diba yanzu ya dawo ya kara, ko kuwa akwai wani bayan Kasim din wanda ya dibar musu dukiya.
Suka yi mamakin yadda Kasim ya san kalmomin da ake fada dutsen ya bude.
Domin su gargadi duk wani mai zuwa yana dibar musu dukiya, sai suka raba gangar jikin Kasim gida hudu, suka manna kowanne sashe daya a bango daya na dutsen, watau kudu da arewa, gabas da yamma. Suka fita suka kora jakunansa zuwa inda suke tara dabbobin da suke satowa.
Da dare ya yi matar Kasim ba ta ga ya komo gida ba, sai hankalinta ya fara tashi. Ta dauki mayafinta ta ruga da gudu zuwa gidan Ali Baba. Ta same shi yana zaune yana hutawa.
Bayan sun gaisa, sai ta ce masa, "Ya kai dan uwan mijina, na san cewa kana da labarin mijina ya shiga daji da jakai, tunda assalatu, akan zai samo wani abu a can, wanda bai fada mini ko mene ne ba. Ga shi har dare ya yi bai komo ba. Shi ne na zo gare ka na ji ko ka san wurin da ya tafi? Ina jin tsoro, ya Allah ko wani mummunan abu ya faru da shi"
Ali Baba ya ce da ita, "Haka ne, dan uwana ya fada mini zai shiga daji, ai na dauka ya dawo, amma bari yanzu na shirya na tafi neman labarinsa. Ki koma gida zan sanar da ke abin da ake ciki idan na dawo."
Ali Baba ya tashi cikin daren nan ya daura wa jakansa uku mangaloli, ya kora su ya nufi cikin dajin da dutsen 'yan fashin nan ya ke. Can zuwa tsakiyar dare ya isa inda dutsen sihirin ya ke. Da isarsa gindin dutsen ya haska fitilarsa, sai ya ga jini faca-faca ko'ina a gindin dutsen. Tun daga nan sai ya sha jinin jikinsa. Ya ce, "Fayau bude dutsen simsim." Nan take kofa ta bude, ya shiga ciki.
Da shigarsa sai kofa ta rufe, ya haska fitilarsa, sai ya ga gawar dan uwansa Kasim, an datsa ta gida hudu, an manna kowane datse a bangon dutsen. Nan take ya yi sauri ya harhada su wuri daya. Sannan ya kuma dibar dukiyar da jakansa biyu za su iya dauka, ya fita daga cikin dutsen. Ya dora wa jakinsa daya gawar dan uwansa, sauran biyun kuma ya dora musu dukiyar da ya diba, ya samu kiraren itatuwa ya rurrufe mangalolin da su, yadda mutane ba za su gane abin da aka dauko ba. Ya kora su da sauri ya nufi gida.
Can zuwa da hantsi Ali Baba ya isa gida, ya shiga da jakansa biyu masu dauke da dukiyar cikin gida, ya fada wa matarsa ta sauke kayan ta boye su inda suka boye na farko. Ya kora jakin daya zuwa gidan matar dan uwansa.
Da ya isa gidan sai ya kwankwasa kofa. Bayan kwankwasawa ta biyu, sai ya ga Murjanatu ta bude kofar. Murjanatu ta kasance baiwa ce ga Kasim, Allah ya hore ma ta tsananin wayo da dabara, duk da ta kasance yarinya karama, mai kananan shekaru, amma hankalinta da tunaninta ya zarta na manyan mutane. Shi ya sa ma duk wata shawara da ita Kasim ya ke yi.
Ali Baba ya kora jakinsa cikin gidan, Murjanatu ta mayar da kofa ta rufe, ya umurce ta da ta kira masa matar dan uwansa. Bayan sun koma, ya sauke gawar Kasim ya shaida musu abin da ya faru da Kasim duka. Bayan sun gama yan koke-kokensu, sun share hawaye, sai ya ce musu, "Abin da na ke so da ku shi ne, ina so mutanen garin nan su tabbatar da cewa dan uwana ya mutu ne a gida, a kan gadonsa, sanadiyyar rashin lafiya, ba na so kowa ya san abin da ya faru da shi."
Abin da ya sa Ali Baba ya fadi haka kuwa shi ne, ya tabbata idan barayin nan suka koma maboyarsu ba su ga gawar Kasim ba, za su shiga binciken wanda ya zo ya dauke ta. To idan mutanen gari suka san gaskiyar labarin yadda Kasim ya mutu, da yadda aka rufe gawarsa guntu-guntu, labarin ba zai boyu ga barayin nan ba, kuma za su yi saurin gane Ali Baba su kashe shi. Amma idan mutanen gari suka san cewa Kasim ya mutu ne a kan gadonsa sanadiyyar rashin lafiya, kuma an yi jana'izarsa gaban mutane, shi ke nan babu wanda zai koma ta kan batun. Don haka babu yadda za a yi barayin su gane wanda ya dauke gawar.
Bayan Ali Baba ya tafi, sai matar Kasim ta ce da Murjanatu, "Na bar wannan a hannunki, ke kika san dabarar da za ki yi, ki kawar da hankalin mutane har su dauka cewa Kasim ya mutu ne sanadiyyar rashin lafiya a kan gadonsa."
Murjanatu ta ce, "Wannan abu ne mai sauki a wurina." Sai ta ruga da gudu zuwa shagon wani mai sayar da magunguna, hankalinta a tashe, ko takalmi babu a kafarta, ta ce da shi, "Don Allah yi sauri ka bani maganin zazzabi, ubangijina Kasim na can zazzabi mai zafi ya rufe shi, har ba ya iya gane masu zuwa wurinsa."
Mai magani ya dauko wani magni ya ba ta. Ta karba ta ba shi dirhami daya, ba ta ko tsaya karbar canji ba, ta nufi gida da sauri, ta na rike da magani a hannunta, tana tafe hawaye na fita daga idonta. Duk wanda ta hadu da shi a kan hanya, idan ya ga halin da take ciki, ga kuma magani a hannunta, sai ya tausaya mata, ya kuma gane abin da take ciki na jiyyar mara lafiya.
Ali Baba da matarsa suka dinga Safa da Marwa tsakanin gidansu da gidan Kasim, domin dai su baddalar da mutane a kan cewa wani abu na faruwa a gidan Kasim. Don haka lokacin da mutane suka ji kuka daga gidan Kasim tare kuma da labarin mutuwarsa cikin dare ba su yi mamakin hakan ba.
Tun da sassafe kafin Ali Baba ya gama shaida wa mutane labarin mutuwar dan uwansa Kasim, domin yi masa jana'iza, ita kuwa Murjanatu sai ta nufi shagon wani baduku, dattijo mai suna Baba Mustafa, domin dama dabi'arsa ce da an fito daga sallar subahi yake bude shagonsa.
Ta same shi a zaune cikin shagon, bayan ta yi masa sallama sun gaisa, sai ta ce da shi, "Baba Mustafa ina da wani aiki da nake so ka yi mini yanzu, amma da sharadi daya." Ta dauko dinari daya ta danka masa a hannu.
Ya yi sauri ya karbe yana murmushi, dama idonsa idon kudi kamar wuta da auduga ne, ya ce da ita, "Diyata, fadi abin da kike so na yi miki, ko menene idan dai zan iya yin sa, to zan yi miki shi duk da dai ban san ki ba, ban ma taba ganin ki ba."
Murjanatu ta ce da shi, "Jiya cikin dare barayi suka shiga gidanmu suka kashe mijina kuma suka sassara shi guntu-guntu. Ina so, a matsayinka na baduku, ka harhada gawarsa wuri daya ka dinke, yadda za a ji dadin yi masa jana'iza. Amma da sharadin zan rufe fuskarka da mayafi ta yadda ba za ka iya gane hanyar da muka bi zuwa gidan ba, kuma ba za ka iya gane gidan ba. Haka kuma idan ka gama zan sake rufe fuskarka na maido ka shagonka.
Zan biya ka kudi mai yawa, ka yarda da wannan sharadi?"
Baba Mustafa ya ce ya amince. Murjanatu ta rufe masa fuska, ta ja hannunsa har suka isa gidan, ta bude kofa suka shiga ciki, ta ja shi har cikin dakin da gawar Kasim ta ke, sannan ta bude masa ido. Ta ce ya yi sauri ya hada shi masu jana'iza na nan zuwa.
Nan take kuwa ba tare da bata lokaci ba Baba Mustafa ya dinke gawar Kasim wuri daya, kamar ba a taba sassara ta ba. Murjanatu ta ba shi kudi masu yawa, sannan ta rufe masa idanu ta mayar da shi shagonsa.
Aka yi jana'izar Kasim aka gama ba tare da kowa ya san gaskiyar abin da ya faru gare shi ba.
Su kuma barayin nan bayan kwana biyu suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan.
HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN (40)

DUBA WANNAN: Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (4)
Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"...
Za mu ci gaba....Ranar Laraba Insha Allah
Ku ci gaba da Kasancewa da Mu domin samun ci gaban wannan ƙayataccen Labarin...
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com
Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode
Source: www.muryarhausa24.com.ng