Suna: Hajjaju
Tsara labari: Abdullahi Amdaz
Kamfani: Kabugawa Production
Shiryawa: Abba Kabugawa da A.B.H Bafarawa
Bada Umarni: Ali Gumzak
Jarumai: Hadiza Muhammad, Shamsu Dan Iya, Maryam Yahya, Nuhu Abdullahi, Shehu Hassan, Bashir Na Yaya, Asma’u Sani. Da sauransu.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Hajjaju (Hadiza Muhammad) a zaune cikin dakin ta tana kwalliya a fuskarta, yayin da ‘yar ta Amira (Maryam Yahya) ta shigo cikin dakin tana nuna takaicin abinda mahaifiyar ta take yi na yin kwalliya don zuwa wajen bazawarin ta. A wannan lokacin ne Samir (Shamsu dan iya) ya shigo cikin gidan sai yaci karo da bazawarin mahaifiyar sa a tsaye yana jiran ta (Shehu Hassan Kano) bayan sun gaisa ne Samir ya shiga cikin gida ya nunawa mahaifiyar sa rashin jin dadin sa akan auren da zata yi, anan ta nuna masa batayi tsufan da zata ha’kura da aure don mahaifin su ya rasu ba. Jin hakan ne yasa Samir ya fito ya riski bazawarin mahaifiyar sa ya soma yi masa rashin kunya gami da ‘kokarin korar sa. A sannan ne Hajjaju ta fito daga cikin gida taga abinda ke faruwa, cikin fushi ta kori Samir sannan suka soma hira da bazawarin ta. A wannan lokacin ne Safwan ya shigo cikin gidan (Nuhu Abdullahi) bayan ya shiga falo ne Amira ta fito wajen sa tana gaya masa ba’ka’ken maganganu akan ya takurawa rayuwar ta alhalin ita bata son sa domin matsayin su daya da yayanta tunda shi abokin yayanta ne. A wannan lokacin ne Amira ta tuna wani lokaci da suke zaune da ‘kawarta a wajen sha’katawa inda ‘kawarta ke bata shawara akan ta daina wulakanta Safwan akan ya nuna yana sonta, amma sai Amira ta nuna itama ai tana son sa lokacin bayyana masa hakan ne baiyi ba, suna cikin hirar ne yazo ya riske ta saboda alamu sun bayyana cewa yaji hirar da suke yi, amma anan Amira ta sake cin mutuncin sa ta nuna ya fita daga rayuwar ta. Bayan Amira ta gama wannan tunani ne yayan ta Safwan ya fito daga daki ya kawo mata waya a sanda Hajjaju ke kiran wayar ta da nufin ta kawowa bazawarin ta ruwan sha, a sannan ne Samir da Amira suka hada mugunta, nan fa Amira taje ha hada ruwan zafi a kofi ta kai masa, a sanda ta fita bata gaishe shi ba ta dangwarar da kofin ruwan a gaban sa, hakan ne ya batawa Hajjaju rai ta soma nuna wa bazawarin nata halin ‘ya’yan nata sai hakuri, amma sai ya basar ya nuna hakan ba komai bane. A wannan lokacin ne bazawarin nata yasha ruwan da Amira ta kawo masa amma sai yayi saurin furzar dashi saboda jin ruwan zafi ne da gishiri, a take a wajen yayi wurgi da kofin ruwan ya soma duba bakin sa, nan yayi fushi ya tashi ya tafi gami da tabbatar wa da Hajjaju cewar ya rabu da ita don haka indai tana son yin aure to ta fara zuwa ta gyara halin ‘ya’yan ta. Anan Hajjaju ta fusata ta nufi cikin gida wajen ‘ya’yan ta inda ta tabbatar musu da ta gaji da abinda suke yi mata don ta nemi aure kusan sau biyar suna ruguza mata shi. Ganin halin da ta shiga tana kuka sai hankalin ‘ya’yan ta ya tashi suka soma neman gafarar ta amma ba wai sun amince dai tayi auren ba.
A wannan lokacin ne Hajjaju ta soma tunanin neman wata mafitar, hakan ne yasa ta umarci ‘ya’yanta Amira da Safwan akan su fito da wadanda zasu aura don su tashi su bar gidan ko hakan zai sa ta samu damar yin aure. Jin hakan ne yasa Amira ta bawa Safwan damar fitowa don suyi aure kuma ta nuna masa dama can tana son sa. Safwan da abokin sa Samir sun ji dadin amincewar da Amira tayi, hakan ne kuma ya bawa Hajjaju damar sauya dabara watarana ta rutsa Safwan saurayin ‘yarta ta nuna masa tana so ya bata hadin kai suyi rayuwa mai dadi kuma tayi masa al’kawarin zata ba shi kudi da ababen more rayuwa gami da ba shi auren Amira, jin hakan yasa Safwan yayi mamaki kuma ya fice yabar gidan gami da dauke ‘kafarsa gaba daya ya daina zuwa. Hakan ne yasa Amira da Samir suka soma mamakin abinda yasa ya daina zuwa gidan, Amira taje har gidan iyayen Safwan tana neman sa, amma sai ‘kanwar Safwan ta nuna mata baya nan, tayi ‘kokarin kira mata shi a waya amma bai daga wayar ba. A bangaren Hajjaju kuwa rashin ganin Safwan duk sai ya dameta ya zamana cewa ko ta kwanta bacci bata komai sai tunani, a sannan ne taje dakin Amira cikin dare ta dauki wayar Amira ta turawa Safwan sa’ko akan tana son ganin sa, washe gari Hajjaju ta aiki Samir da Amira a sanda Safwan yazo ta rufe ‘kofa har ta hilace shi ya amince da ita. Tun daga sannan Safwan da Hajjaju suka cigaba da neman juna ba tare da kowa ya sani ba har na tsahon wani lokaci, daga bisani wata rana Amira ta shiga dakin Hajjaju da safe ta tarar da Safwan yana bacci a gadon mahaifiyar ta, nan taje ta kira yayan ta Samir suka zo suka yiwa Safwan mugun duka har ya suma. Bayan an kai Safwan asibiti ne mahaifin sa (Bashir Na Yaya) yayi wadarai da halin sa yayin da mahaifiyar Safwan (Asma’u Sani) itama tayi tur da halin Safwan. Haka Safwan ya saura a kwance cikin jinya. Yayin da su kuma su Amira a gida suka nuna takaicin su akan abinda mahaifiyar su ta aikata, a sannan ne ta fada musu tana dauke da cikin Safwan kuma auren shi zata yi. Su Amira sun nuna sai an zubar da cikin amma Hajjaju taki amincewa. Bayan tsahon wani lokaci a sanda Hajjaju ta haihu sai ta kaiwa Safwan dan sa da ta haifa sannan suka yi sallama da ‘ya’yan ta bayan ta tabbatar musu da bazata iya cigaba da rayuwa ba.
Abubuwan Burgewa:
1- Labarin ya fadakar kuma ya nishadantar, domin an yi ‘kokar wajen rike me kallo.
2- Jaruman sun yi ‘ko’kari wajen isar da sa’kon labarin.
3- Daraktan yayi ‘ko’kari wajen ganin an tafiyar da camera ta hanyar da ta dace.
4- Sauti ya fita radau, haka ma camera don an samar da hoto me kyau.
Kurakurai:
1- Titin sama da aka fara nuna wa a fim din (fly ober) ba titin garin Kano bane, alhalin a cikin garin Kano aka dau fim din.
2- Wane irin hukunci aka yankewa Hajjaju wanda har yasa take sallama da ‘ya’yanta? Tunda ba’a nuna cewa ta kai kanta kotun musulunci don a yanke mata hukuncin da ya dace da laifin da ta aikata ba, to ya dace a fadi irin hukuncin da aka yanke mata ko da baki ne.
3- Bai kamata mai kallo yaga Amira a cikin wa’kar da aka yi a ‘karshen dim din ba, domin an ga lokacin da Samir yace tana can a kwance bata da lafiya ba zata iya zuwa wajen ba, amma sai aka ganta ana wa’ka tare da ita. Shin warkewa tayi?
4- Lokacin da Amira taje gidan su Safwan tana neman sa, lokacin da ‘kanwar sa ta dauko waya ta soma kiran sa, yanayin da aka nuna tana kiran sa bai yi kama da cewar ana kiran lambar wani ba. Fuskar wayar ta fi kama da wayar da take a kulle ko a kashe.
Karkarewa:
Fim din ya fadakar, kuma zaren labarin har ya dire bai karye ba. Sai dai kuma ya kamata a ce karshen fim din ya fi haka inganci. Wallahu a’alamu!
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com
Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: Leadership A Yau

Fim ɗin Hajjajju