Friday, 19 October 2018

Karanta Kaji Dalilin sa: Ina Mamakin Masu Haɗa Buhari Da Atiku A Fannin Nagartar Shugabanci - Inji Balarabe Musa

Tura Wannan Zuwa Ga
Malam Balarabe Musa ya kara da cewar Nijeriya za ta tafka kuskuren samar da gwamnatin wacce take ta 'yan tsiraru kuma wacce za ta dakushe adawa da gwamnati baki daya saboda irin hadin guiwar da Atikun yake da ita da wani tsohon shugaban kasa na mulkin soja wanda shi ma kansa yake da wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa akansa.


Marubuci: Real Sani Twoeffect Yawuri

Tsohom Gwamnan na jihar Kaduna, ya kara da cewa "Saboda haka ne ma nake jin takaicin yadda wasu tsirarun 'yan Nijeriya suke ikirarin cewar Atiku ya fi shugaba Buhari. Sam ba su da mahada babu yadda ko kusa za a kamanta Buhari da Atiku.

"Tsoffin shugabannin kasa da wasu tsoffin Janar na soja da sukayi ritaya suna tsoron shugaba Buhari ya sake dawowa kan karagar mulki a karo na biyu saboda suna cike da tsoron idan Buhari ya dawo a karo na biyu to zai bude shafin binciken soke zabin June 12 na Abiola kuma zai tunkari yaki da cin hanci da rashawa gadan-gadan.
"Shi yasa suke ta kokarin haduwa wuri daya domin dai kada shugaba Buhari ya yi nasara ba wai domin su kansu suna da yakinin Atiku yafi Buhari ba. A'a, saboda kawai dai sun san Atikun ba zai binciki barnar da suka aikata a baya ba.

Ya kamata Atikun ya tambayi kansa ta yaya Obasanjo cikin sauki zai yafe masa ba tare da wani dalili ba har ma ya taya shi (Atiku) yakin neman zabe a yankinsa domin samun nasara a zabe mai zuwa na shekarar 2019".

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user