A zamanin khalifa Umar dan Khattaab, wasu mutane uku suka zo masa suna rike da wani saurayi suka ce:
Ya Amiral muminina! Wannan mutum ya kashe mana mahaifinmu.
Umar: kai donme ka kashe musu uba?
Saurayi: Ni makiyayi ne, rakumata ce ta ci itaciyar gonar mahaifinsu, sai mahaifinsu ya bugi rakumin da dutsi, rakuma ta mutu, ni kuma na dauki dutsin na buge shi
ya mutu.
Umar: saboda haka zan tsaida haddi akanka.
Saurayi: ka saurara mini kwana uku, mahaifina ya mutu ya barni da kanwata da
kuma dukiya, idan ka kasheni dukiyar da yar uwata zasu tozarta.
Umar: wa zai lamunceka?
Saurayi ya duba cikin mutane sai ya nuna Sahabi "Abu Dhar".
Umar: ka lamunce masa Ya Aba Dharr?
Abu Dharri: na'am
Umar: ba ka san mutum ba ka lamunce, to idan ya gudu haddi zai koma kanka.
Abu Dharr: na yarda.
Saurayi ya tafi, aka kwana biyu, an shiga na so uku, saurayi bai zo ba,
Hankalin kowa ya tashi akan Abu Dharri kar haddi ya koma kansa.
Kafin sallar magariba sai ga saurayi ya zo a gajiye, ya tsaya a gaban khalifa Umar.
Saurayi: na mika dukiyar ga kawuna yanzu ina hanunka, ka tsaida haddi
akaina.
Cikin mamaki Umar ya ce: me ya dawo da kai bayan ka sami dama da za ka
iya gudu abinka?
Saurayi: na ji tsoro, Kar a ce cika alkawari ya Kare
cikin mutane.
Umar ya juya ga Abu Dharr: me ya sa ka lamunce
masa?
Abu Dharr: na ji tsoro, kar a ce alheri ya Kare cikin
mutane.
Wannan jawabi ya yi tasiri ga masu Neman jinin ubansu, suka ce sun yafewa
saurayi.
Umar: don me?
Suka ce: muna tsoro, kar a ce afuwa ta Kare a cikin mutane.
Ni ma na isar muku da wannan labari ne don ina tsoron kar a ce kira/tunatarwa zuwaga aikata alkhairi (wato da'awa) ya Kare cikin mutane. Don Allah kai ma ka tura kar ace yaɗa alheri ya ƙare cikin mutane.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: www.MuryarHausa24.com.ng
Thursday, 18 October 2018
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
MAKALOLI MASU ALAKA
- Blog Comments
- Facebook Comments