Mun tambaye shi a kan yadda ya samu kansa a cikin fim din In Search of the King da kuma irin rawar da ya taka, inda yake cewa:
“To a wannan fim din dai na fito a matsayin sarki na wani gari da ake kira Tumashe kuma na ji dadin karanta labarin ya burge ni musamman da ya zamo fim din na Hausa ne amma da yaren Turanci aka yi shi, domin irin finafinan da ya kamata mu rinka yi kenan don mu nuna wa duniya ta san ko wane ne Bahaushe ta bangaren addininsa, al’adarsa da ma sauran mu’amularsa ta rayuwa da irin yadda yake tafiyar da mulkinsa, domin kuwa ana kalon yaren turanci a matsayi na daya a duniya, kuma rol din da na hau a matsayin sarkin Tumashe kamar yadda shi jarumin fim din yake tafiya kuma a cikin tafiyar tasa yake ratsowa ta garina. Kuma a cikin fim din sai na zamo wani azzalumin sarki na kasance sarkin da ba ya so a kawo masa ilimina kowanne irin yanayi don ba na so jama’ata su yi ilimi su waye a matsayi na mai mulkin kama karya, don haka idan har ilimi ya zo to karshen sarautar ya zo ya ci gaba da cewa, “A yanayin sarki da na fito a In Search of the King, sarki ne da yake yi wa ‘yan masarautarsa kwacen mata da wasu abubuwa na kama karya, wadanda ya kamata a ce an san da irin wadannan da kuma a yi bayani a kan wanne irin tanadi ilimi ya yi wa wannan zalunci na sarakuna da suke da irin wannan dabi’a.”
Ya kara da cewa, “Kuma a gaskiya juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta, domin idan ka duba shi Kabiru Musa Jammaje dama shii ya fito da tsari na daban ne a masana’antar finafinai ta Kannywood inda ya fito da tsarin yin finafinan turanci, kamar finafinan da ya yi a baya, to amma a yanzu da ya karkata bangaren al’adu na sarauta da tafiyar da mulki irin na kasar Hausa ka ga wannan wani karin ci gaba ne.To amma sai na ji dadi ya fara yi da bangaren ilimi, don finafinansa da suka fita za ka ga suna magana ne a kan ilimi da matasa. To yanzu kuma sai aka dauko al’adarmu ta Bahaushen gabadaya, don ita rayuwar Bahaushe idan ka kalle ta z aka ga rayuwa ce da ilimi ya yi tasiri a cikinta don haka ina ganin wannan labarin zai zama zakaran gwajin dafi. Ko ba komai aljihusnsa ya amsa, su kuma jaruman da suka fita a cikin fim din jikinsu ya fada musu kuma na san duk wanda ya ga yadda ake yin fim din nan to ya tabbatar dim muke yi ba wasa ba. Don fim ne da da ya amsa sunansa a matsayin fim. Kuma wannan fim din ya fito da jama’a da dama da suke a boye da ilimi na zamani ba tare da an sani ba. Kuma abin zai bunkasa ne a lokacin da fim din ya fito a nan za a ga yadda tasirin ilimi yake a cikin ‘yan fim kuma kalubalen da muke samu na kallon da ake yi mana da wadanda ba su da ilimi a yanzu wadanda ba su da ilimi a yanzu abin zai canza ta hanyar irin wadannan finafinan da Kabiru Musa Jammaje yake yi.”
A game da rol din da ya hau kuwa cewa ya yi, “Ai tun da aka ba ni labarin na karanta na ce to fa aikin ba karami ba ne, kuma daman shi dan fim ana so ya zamo ta ko’ina za a iya lankwasa ka. Watarana ka fito makaho ko kuturu ko dan daba, wani lokaci ka fito almajiri, amma dai abin da na fahimta da fim din da kuma irin matsayin da na hau, abu ne da za a bar wa masu kallo su yi alkalanci, amma dai na san cewa da yardar Allah za a fita kunyar masu kallo.”
Daga karshe ya yi wa masoyansa fatan alheri tare da kiran su da su taimaka wajen yakar masu satar fasaha ta hanyar sayen fim mai inganci, kuma ita ma hukuma ta ba da goyon baya da tallafi ga masu sana’ar fim din Hausa, musamman a yanzu da muke da burin tallata al’adunmu duniya ta yin finafinan masu inganci da harshen Turanci.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke
Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya
Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.
DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng
Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki
Mungode
Source: Leadersbip A Yau