Saturday, 10 November 2018

KARANTA KA JI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA HUDU

Tura Wannan Zuwa Ga
Domin taimaka wa ɗalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.





Darasi Na Huɗu

ƘA’IDOJIN RABA KALMOMI

Raba kalmomi a muhallan da ke buƙatar rabawa, jigo ne babba da ya wajaba duk mai yin rubutu da Hausa ya kula da shi.

Babban amfaninsa shi ne gyara ma’anar kalmomi da fito da ma’anarsu yadda kowa zai fahimta. Haɗe kalmomi a inda bai dace ba, na iya haifar da sauya ma’anar kalma ko ma jumla baki ɗayanta.

Misali:

maraba – wurin rabuwa ko yi wa wani barka da zuwa

ma raba – wato za mu raba.

akuya – sunan dabba

aku ya – (tsuntsu) aku ya yi me?

sa mata kai biyu - sanya mata kawuna biyu

sa matakai biyu – sanya matakai guda biyu

sama ta kai biyu – adadin sama ya kai guda biyu

Idan muka duba waɗannan misalai da kyau, za mu ga yadda kalmomi da jumlolin suka sauya ma’ana sakamakon haɗe kalmomi ko raba su a inda bai dace ba.


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad.

KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA UKU

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user