Friday, 9 November 2018

Karanta Kaji: Wata Sabuwa Amurka Ta Kera Jirgin Annabi Nuhu

Tura Wannan Zuwa Ga
Ma'aikatar kirkire-kirkire ta jihar Kentucky ta Amurka, ta kashe tsabar kudi har Dala miliyan 100 wajen gina wani jirgin ruwa kwatankwacin kwamin Annabi Nuhu, bisa dogaro da yadda aka siffanta shi a littafin Injila. Kelly Grovier ya yi nazari kan hakan.



An sabunta labarin bayan da aka fara wallafa shi ranar 20 ga watan Yulin 2016.

Shin da me kake neman tsira a wannan duniyar? Addini? Ko Iyalinka? Ko kuma harkar wasanni?

Wasu hotuna da suka rinka kai-komo a kafafen yada labarai da na shafukan sada zumunta, a 'yan kwanakin nan dangane da wani jirgin ruwa da aka gina, sun haddasa wata mahawara a tsakanin mutane a arewacin jihar Kentucky, abin da kuma ya yi nuni da irin yadda al'umma ke neman kariya daga wasu bakin al'adu da ba sa so.

Hotunan katafaren jirgin da aka gina domin kwaikwayon kwamin Annabi Nuhu wanda kuma ya lankwame Dala miliyan 100, kwatankwacin Fam miliyan 77, sun zama abubuwan da za su sanya mutane su yi duba ga irin dimbin basirar da Allah ya huwacewa wani Ba-Amurke masanin hikayoyi, a karni na 19, mai suna Edward Hicks.

Shi dai wannan mutum yana da tunani daban da na mutane kan yadda tarihin kwamin na Annabi Nuhu ya zama wani abin da zai zaburar da mutane wajen kirkire-kirkire a wannan zamanin.

Jirgin wanda aka yi dai-dai da yadda aka siffanta shi a littafin Injila wanda ya ba da labarin irin yadda Allah ya shaidawa Annabi Nuhu cewa zai saukar da Ruwan Dufana ko kuma ruwa kamar da bakin kwaryar da zai halakar da mutanen wancan zamanin saboda irin laifukan da suke aikatawa.

Yana da girman kafa 450 wato dai-dai da nisan kilomita 137, sannan tsawonsa ya kai kafa 75 wato kilomita 23 sannan kuma yana da fadin kafa 45 kwatankwacin kilomita 14.

Mutanen ma'aikatar ta kirkire-kirkire wadanda suka goyi bayan a gina shi wannan jirgi, sun yi ammanna ne da ma'ana ta zahiri dangane da abubuwan da littafin Injila ya zo da su, abin da yasa suka yi kiyasin cewa a yanzu haka shekarar duniya 6000.

A tunaninsu, kwaikwayon jirgin na Annabi Nuhu zai zaburar da dan adam tashi tsaye wajen neman kariya daga illolin bidi'a ko kuma wasu abubuwa kagaggu kamar yin imani da tsarin da ke kore shigar da Ubangiji cikin al'amuran yau da kullum da aka fi sani a turance da 'secularism'.

To sai dai kuma wadanda suke sukar gina jirgin irin na Annabi Nuhu wanda aka gina cikinsa dauke da halittu iri daban-daban kamar kakannin kadangaru da ake kira 'Dinosaurs' a turance (wasu halittun da yanzu babu su a doron duniya), sun kalubalanci yadda wasu 'yan majalisar dokokin jihar ta Kentucky suka zuba kudade wajen gida jirgin.

A lokacin da suke zanga-zangar nuna kyamar jirgin, masu adawar sun dage cewa idan mutane suka goyi bayan ginin jirgin wanda tsari ne na kiristanci kamar hakan na nufin ma'aikatar ta kirkire-kirkire na fito da wasu abubuwa da ka iya zamowa kishiya ga kimiyya, wani abu da ya yi hannun riga da tsarin kasar Amurka na addini daban kuma harkokin gwamnati ma daban.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun takaddama kan jirgin na Annabi Nuhu da kuma halittun da suka kasance a cikinsa. Shi dai marubucin hikayoyin na karni na 19 dan Amurka, Edward Hicks, ya kan yi abubuwa masu alaka da irin abin da addini ya zo da su tun asali.

Hicks dai ya kasance mutum wanda bai yi imani da Allah ba, a lokacin yana matashi kafin daga bisani ya koma bin akidar addinin kiristanci ta 'quakerism' wadda ta yi ammana da duk wani abu da littafin Injila ya zo da shi, da kuma kore duk wani abu da ya yi karo da littafin.

Ya kuma ta kokarin nuna jajircewarsa da sadaukarwarsa ga akidar tasa, a inda ya yi ta wallafa zane-zane da ya kira 'Daula ta zaman Lafiya' wadda mutane da dukkan halittu na duniya za su rayu a ciki ba tare da damuwa ba.

Daya daga cikin zane-zanen nasa da suka fi shahara shi ne sake dabba'a rubutu da dutse wanda Nathaniel Currier ya yi a 1846, a inda aka nuna yadda dabbobi suka shiga kwamin Annabi Nuhu.

Hoton da Hicks ya zana kansa da kansa wanda ba kasafai ake samun hakan ba, a inda ya bayyana a siffar zaki yana hararar mutane.

An dai ajiye hoton na Hicks ne kusa da katafaren jirgin da ya gina irin na Annabi Nuhu, lokacin Ruwan Dufana, abin da ke nuni da irin almarar da ke nuna cewa wata rana za a dare jirgin domin tsira daga wannan duniyar da za ta iya nutsewa a cikin irin wancan ruwan na Dufana.

Idan kana son karanta wannan labarin a turanci, to za ka iya latsa wannan The Gian Noah's Ark — in Kentucky

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user